Rumbun Ilimi - Waƙar Jamhuriyya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Waƙar Jamhuriyya: Sa'adu Zungur


In zaka faɗi faɗigaskiya,
              Kome ta ka ja maka ka biya!

Haka ne, editanmu na gaskiya,
              Wadda ta fi dubun zinariya.

Sai mu gode Allah shi ɗaya,
              Don shi ne Sarkin gaskiya.

Ya mallaki dukkan talikai,
              Na kwari da tudu da samaniya.

Da mutum, aljan da mala’ika,
              Dabbar sarari da ta maliya.

Mulki, iko, daula duka,
              Na ga sarki Allah shi ɗaya.

Shi ya ke ba wanda ya so duka,
              Ya sarautu a lardin duniya.

Shi ya ke karɓe ta ga talikai,
              Don ya ɗanɗani wahalar duniya.

Shi ka girmama wanda ya so duka,
              Shi ka sanya waɗansu su sha wuya.

Shi ka cusa dare a cikin wuni,
              Kuma ya zaro hasken safiya.

Shi ka rayawar mamaci duka,
              Shi ke kashe mai rai, shi ɗaya.

Ikonsa a kan kome ya ke,
              A ruwa da tudu da samaniya.

Alwakilu, mu dogara duk garai,
              Zahirinmu da ɓoye a zuciya.

Mu amince, zai mana taimako,
Na haƙiƙa inda majaziya.

Sallama a gare ku, sarakuna,
              Mun yi niyyar bayyana gaskiya.

Addu’armu ga Allah Rahimi,
              Ya kiyaye Arewa gaba ɗaya

Muminai da Masihai jumlatan,
              Kuma da arna, dodannin giya.

Tutocin Shehu Mujadaddi,
              Goma sha biyu ne Nijeriya.

Sir Assidiƙu Abubakar,
              Ga Arewa tana kan shan wuya.

Shehu Alkanemi a Yarwa ko,
              Za ka yarda a rushe mulukiya?<

Hausawa su da Barebari,
              Ai amana ce da kilefiya

Shehu Laminu shi da Mujadaddi,
              Sun bar mana girman duniya.

Yalla za mu kiyaye har mu bar,
              ‘Ya’yanmu su gaji halaliya?

Ya jikokin Shaihunnai biyu,
              Sai ku ɗau tutarku ta gaskiya.

Haƙƙi na ƙabiloli duka,
              Na wuyanku, ku sauke lafiya!

Daularku a kayin muminai,
              Da wasunsu, ta wanye lafiya!

Da aminci babu gwagwarmaya,
              Babu zalunci da hatsaniya!

Sai mu je ga malam Yahaya,
              Can a birnin Gwandu, mu kewaya.

Shaihu Abdullahi haƙiƙatan,
              Ya bar mana gadon gaskiya.

Ilmi, hikima, addini duka,
               Da dabarar sarrafa duniya.

Muka lalata, muka wargaza,
              Gas hi yau sai anai mana dariya.

Babu tsuntsu  ba tarko duka,
              Wallahi mun yi hasarar duniya!

Jahilci ya ci lakarmu duk,
              Ya sa mana sarƙa har wuya.

Ya sa mana ankwa hannuwa,
              Ya ɗaure ƙafarmu da tsarkiya.

Bakunanmu ya sa takunkumi,
               Ba zalaƙa sai sharholiya.

Ya Allah kai mana agaji,
              Don mu kauce kunyar duniya!

Ilmi mai amfani duka,
              Inda addininmu ya rataya.

Im fa addini ya raunana,
              Babu alheri nan duniya.

Duka cuta kai ke magani,
              Har a san ingantar lafiya.

Allah ya tsare mu da jarraba,
              Lahirarmu da rayin duniya.

Addu’armu da mu da sarakuna,
              Na Arewa ta zam karɓaɓɓiya.

Ya Sarki Alhaji Bayero,
              Ga ‘yam birni da Kanawuya.

Tun Bagauda yana sarar Kano,
              Suka fara fataucin dukiya.

Hijira da ta iske Alwali,
               Sai ta ƙarfafa tushen gaskiya.

Sabon tsari zam bayyana,
              Ban da tajdidi na mutan Gaya.

Ai Sulaiman shi ne jagaba,
              Kuma Dabo ya bi shi da gaskiya.

Ga sarauta, ga ilmi ciki,
               Ga adala, shari’ar gaskiya.

Sai arnanci ya yi sallama,
              Daɗa har abada ba dawaya.

Sarki Abdullah ka taimaka,
              Ga Ciroma Sanusi da tarbiya.

Ka kiyaye al’ummarka duk,
              Don ƙasarmu ta wanzu mulukiya.

Birni da Fage da Tudun wada,
              Ƙauyuka, bukkokin tsangaya.

Kar ka bar arna su shige musu,
              Don su watsa dafin jumhuriya.

Katsinawa, sai ku yi tuntunin,
              Umarun Dallaji, mazan jiya.

In ji dai kun hangi mutan Gusau,
              Masu mai da ƙasa jumhuriya?

Ai ga ku da gado mai yawa,
              Na zumunci, babu hatsaniya.

Ga sarki Alhaji Usuman,
              Ya Nagogo idanun duniya!

Am bar maka nauyi mai yawa,
              Allah sa fa ka sauke lafiya.

Mu dai ilimi muka tambaya,
              Ko a London ko a Arebiya.

Yaƙubu Yaƙubu na Maigari,
              Ya fi ƙarfin ai masa dariya.

Arna da Musulmi Bauchi duk,
              Sun yi caffa, don su ga gaskiya.

Da shirin mulki mai ƙa’ida,
              Na adala, ban da haramiya.

Ilmi na sana’a mai yawa,
              Da shirin addinin gaskiya.

Da shari’ar bin bahasi da kyau,
              Babu hanci, ba kuma toshiya.

Ya Ja’afaru, zo ka wuce gaba,
              Malami ne, sarkin duniya.

Mallawa, su da Barebari,
              Sun ga adalcinka da gaskiya.

Katsinawa har da Zagezagi,
              Sulluɓawan lardin Zariya.

Duka sun san kai ne shugaba,
              Ka riƙe zarafinsu da gaskiya.

Za mu bi ka, ka ja mu zuwa gaba,
              Kar ka yarda Arewa ta sha wuya!

A ƙasar Adamawa da Ahmadu,
               Lamiɗo fitillun gaskiya.

Mun kai masa caffa har gida,
               Allah sudda asiri a duniya!

Jikan Madibbo Subaɗo sai,
              Ka tsare daularka da gaskiya.

Jaumirawo ya taimaki Fulɓe duk,
              Don su san girma a Nijeriya.

Madalla, Muhammadu mai Muri,
              Sarkin da ya hangi ɗari ɗaya.

Ko Lugard ya san himma tasa,
              Da irin ƙwazonsa a duniya.

Kyakkyawar fata kewano,
              In ji Kenci a yamma da Zariya.

Haƙƙi na Nufawa na wuyan,
               Ndyako Etsu, abin biya.

Ga Umaru Sanda a Guddiri,
               Malami ne ya san gaskiya.

A Misau ga Sarki Ahmadu,
               Malami ne a mazan jiya.

Jama’are akwai su da shugaba,
              Ya gane shu’unen duniya.

Gwambe su ma ai da Abubakar,
              Adali ne ya shige tambaya.

Ya Daurawa, ku bi mai dubu,
              Abdu mai zance da macijiya!

Ko Bawo yana shakka tasa,
              Ya gaje tutar gaskiya.

Marigayi Abdu na Ƙadiri,
              Can Haɗeja mu ke musu ta’aziya.

Wa ya gaji maza su Nagwamutse?
              Sarkin Sudanin gaskiya.

Kwantagora tana murna da shi,
              Ibrahim ya shige tambaya.

A Ilorin, Igala da Igbirra,
              Gaisuwarmu gare su, alafiya!

Kabiyesi Abdulƙadiri,
              Ka riƙe tutarka ta gaskiya.

Atta Attanmu guda biyu,
               Ɗaya Alhaji ne ba tambaya.

A Okene, Buraima ya ce da mu,
              Ya san daraja ta mulukiya.

Mun kira, ya Sarkin malamai,
              Ilmi da sarautar duniya!

A Abuja ya ke kan yaɗuwa,
              Zai sadu da Birnin Lafiya.

A ƙasar Kuza ga Sarkin Birom,
              Rwang Pam ya ɗauki ɗawainiya!

Can a Binuwai ga Sarkin Jukun,
              Aku ne na Waziri abin biya.

Ka ji sunaye na sarakuna,
               Lardi lardi ba tambaya.

Manufarmu mu bayyana danguna,
              Na Ƙabilu, ban da tsirariya.

Don akwai wasu ma a sarakuna,
              Mun bar su da ayar tambaya.

Haƙƙin jama’a na kansu duk,
              Su riƙe igiyarsa da gaskiya.

In sunka sake jama’ar Kudu,
              Suka hau mulkin Nijeriya.

Daɗa ba sauran mai tambaya,
              Kowa ya san zai sha wuya!

An sha bamban bisa kan nufi,
              Na shirin mulkin Nijeriya.

Niyyar Kudu in suka ɗaukaka,
              Duk ƙasa ta zamo Jumhuriya.

Mu kam niyyarmu a karkasa,
              Don Arewa ta zavi mulukiya.

Ku fahimci shiri na mulukiya,
              Da yawan haɗarin jumhuriya

Sarki da gidajen shawara,
              Da shari’a kun ji mulukiya.

Mulki na wakilai guruguzu,
              Ba Sarki babu Sarauniya.

Sai ‘yan sanda, sai soja, sai,
              Oda, ita ce jumhuriya.

Fatarmu Arewa ta farga duk,
              Don ta gane lamarin duniya.

Farfagandar makirci duka,
              Sai a bar ta, a bincika gaskiya.

Huɗubobin kinibibi duka,
              Dangin zance na filaniya.

A jaridu ko a matattara,
              A wurin lacca da hatsaniya.

Allah ya kiyaye Nijeriya,
              Ga masifar lardin Indiya.

Tsoron Allah ɗai am magani,
              Shi ɗai ka kiyaye mulukiya.

Mu dai haƙƙinmu gaya muku,
              Ko ku karva ko ku yi dariya.

Dariyarku ta zam kuka gaba,
              Da ladamar mai ƙin gaskiya.

Wa’azi ne mulkin Indiya,
              Da ta zam daular jumhuriya.

Yau ina manya na sarakunan,
              Pakistan, ko kuma Indiya?

Da Nizam, Maharaja da Raja duk,
              Sai kuka, ba mai dariya.

Da sarakai sun fi ɗari biyar,
              Duka sun waste, ba ko ɗaya.

Sai ka ce fa da ɗai ba a yi su ba,
               Kun ji sharrorin jumhuriya.

A mujallar “Daily Mail” akwai,
              Tarihin Mulkin Indiya.

Da abinda ya faru a bara duk,
               Bisa rushe gini na mulukiya.

Ko a Burma akwai sauran iri,
              Na sarakai? Sai ku yi tambaya.

Indonesiya su sun rage?
              Kaito, tsarin jumhuriya!

Duk misalan nan na Amirka ba,
               Mai kyau, na shirin jumhuriya.

Kar ku ruɗu da zancen ja’irai,
              Masu son halakar Nijeriya.

Gaskiya ba ta neman ado,
              Ko na daɗin musyar zabiya.

Ƙarya ce mai launi bakwai,
              Ga fari, da baƙi, ga rawaya.

Ga shuɗi, ga kuma algashi,
              Toka-toka, da ja, sun garwaya.

Ba ta ‘ya’ya sai ko tai fure,
              Sai rassa sun fi dubu ɗaya.

‘Yan Arewa ku daina gaganiya,
              Ku riƙe Daularku da gaskiya.

Allah ya kaɗe muku ja’iba,
              Ya tsare ku ga sharrin duniya!

To, sarakai, sai ku yu tattali,
               Na adala, ban da haramiya.

Sai ku hango gemun ɗan’uwa,
              Da ya kama wuta da gaganiya.

Don ku nemi ruwa ku yi yayyafi,
              Kada ku ma naku ya sha wuya.

In kun dage, kun shamtake,
              Bisa al’adu na mazan jiya.

Za ku rera faɗar da-na-sani,
              Da na bi jawabin “Gaskiya”.

Allah ya tsare ku faɗar haka,
              Ya kiyaye Arewa gaba ɗaya!

Tutocin Shaihu Mujadaddi,
              Daɗa basu zama jumhuriya!

In sha Allahu! Mu tsarkake,
              Bisa fatan za mu bi gaskiya.

Domin fa Arewa da hargitsi,
               Da yawan varna ba kariya.

Matuƙar Arewa da karuwai,
              Wallah za mu yi kunyar duniya.

Matuƙar ‘yan iska na gari,
              Ɗan daudu da shi da magajiya.

Da samari masu ruwan kuɗi,
              Ga maroƙa can a gidan giya.

Babu shakka ‘yan Kudu za su hau,
              Dokin mulkin Nijeriya.

Su yi ta kau sukuwa bisa kanmu ko,
              Mun roƙi zumuntar duniya.

Mutuƙar yaranmu suna bara,
              “Allah ba ku mu sami abin miya!”

A gidan birni da na ƙauyuka,
              Da cikin makarantun tsangaya.

Sun yafu da fatar bunsuru,
              Babu shakka sai mun sha wuya.

Matuƙar da musakai barkatai,
               Da makaho ko da makauniya,

Ba mahalli nasu a Hausa duk,
              Babu mai tsayonsu da dukiya.

Birni ƙauye da garuruwa,
              Duk suna yawo a Nijeriya.

Kai Bahaushe bas hi da zuciya,
              Za ya sha kunya nan duniya!

A Arewa zumunta ta mutu,
              Sai nishaɗi, sai sharholiya.

Sai alfahari da yawan ƙwafe,
              Girman kai, sai ƙwambon tsiya.

Camfe-camfe da tsibbace-tsibbacen,
               Malaman ƙarya, ‘yan duniya.

Cin amana kuma da yawan riya,
              Ga hula mai annakiya.

Babu mai aiki bisa hankali,
              Da basira, don ya ga gaskiya.

Rantse-rantse da Allah yai yawa,
              Ga ƙarya, ga zambar tsiya.

Gorin asali da na dukiya,
              Sai ka ce ɗan “Annabin Fariya”.

Sai kinibibi sai kwarmato,
              Ga gulma da son ƙullaliya.

Wagga al’umma me za ta wo,
              A ciki zarafofin duniya?

To, sarakai, sai fa ku himmatu,
              Don ku gyara ƙasarku da gaskiya.

Kuma Allah shi ne zai cika,
              Ya kiyaye Arewa gaba ɗɗaya.

Mun gode Allah shi ɗaya,
              Don shi ne Sarkin Gaskiya.Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub