Tsarin Sauti: Yanayin Furuci Baƙaƙe

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tsarin Sauti: Yanayin Furuci Baƙaƙe


Gabatarwa

Abin lura game da yanayin furucin baƙi shi ne halin da iska ta shiga a lokacin da gaɓoɓin furuci suka yi yunƙurin furta baƙi. Daga cikin irin waɗannan halaye, akwai halin da gaɓoɓin ke datse iskar; su tsayar da ita cik, na wani ɗan lokaci maras tsawo, akwai kuma wanda suke kusantar juna dab-da-dab, da sauransu. Saboda haka a wannan gaɓar ta yanayin furuci za mu nazarci waɗannan halaye na fitar iska a lokacin furta baƙi.

Kamar yadda aka saba, a wannan matakin ma, masana sun saɓa da juna wajen raɗa sunayen halayen da ma yi wa baƙaƙen muhalli. Ga dai yadda ta kaya:

Tsayau

Tsayau su ne baƙaƙen da idan aka zo furta su gaɓoɓin furuci suke tsayar da iskar huhu mai fita waje, waje ɗaya cik na wasu ‘yan daƙiƙoƙi, sannan su sake ta. Akwai gurare huɗu da gaɓoɓin ke haɗewa su tsayar da iskar cik: Haɗewar leɓen ƙasa dana sama; haɗewar tsinin harshe da hanƙa; haɗewar doron harshe da hanɗa da kuma rufewar maƙwallato.

Ga jerin baƙaƙe tsayau: /b/, /t/, /d/, /k/, /kj/, /kw/, /gw/, /g/, /gj/, /Ɂ/ da /Ɂj/. Dukkan waɗannan baƙae tsayau ne.

‘Yan Hanci

Su ne baƙaƙen da idan aka zo furta su gaɓoɓin furuci ke datse iska, su ɗan jinkirta, lokacin da za su buɗe tuni iskar ta riga ta karkata akalarta zuwa hanci, sai ta fita ta hancin. A wannan rukuni akwai gaɓoɓin da ke datse iskar kamar haka: Leɓɓa, tsinin harshe da kuma hanƙa; gaban harshe da ganɗa sai kuma doron harshe da hanƙa. Baƙaƙen da suke cikin wannan aji su ne: /m/, /n/, /ɲ/ da kuma /ŋ/.

Zuzau

Su ne baƙaƙen da tsinin harshe da hanƙa suke kusantar juna sosai, su rage faɗin kwararon fitar iskar huhu, har ta kai ga iskar ta yi amfani da ƙarfi ta fita tana zuzar su. Baƙaƙen da ake kira da wannan suna su ne /s/, /z/, /Φ/, /Φj/, /h/ da /ʃ/.

Kusantau

Su ne baƙaƙen da tsinin harshe yake kusantar hanƙa a lokacin furta su, amma kusancin ba mai tsanani ba. A nan, iska bata amfani da ƙarfi wajen fitar ta, sannan kuma bata zuzar komai. A wannan jerin akwai harrufa biyu; /j/ da /w/.

Haɗiyau

Su ne baƙaƙen da idan aka zo furta su gaɓoɓin furuci suke amfani da iskar maƙwallato mai faɗawa ciki. Saboda haka idan gaɓoɓin suka matse suka buɗe, sai iskar ta faɗa ciki. Wannan ta saka ake kiran su haɗiyau, saboda haɗiye iskar da mai furuci yake yi. A cikin wannan aji akwai /ɓ/ da /ɗ/.

Tunkuɗau

Su ne baƙaƙen da idan aka zo furta su doron harshe da hanɗa suke haɗuwa su datse iskar maƙwallato mai fita waje na ɗan ƙanƙanin lokaci, suna warewa, sai iskar ta fito kamar an tunkuɗo ta. Baƙaƙe irin su /ƙ/, /ƙw/, /ƙj/ da /s’/ su ne a wannan aji.

‘Yan Atishawa

Baƙaƙe ne da idan aka zo furta su gaɓoɓin furuci suke haɗewa su toshe mafitar iska na ɗan lokacin da jikinrinsa bai kai na tsayau ba, da zarar sun ware, sai iskar ta fice a hankali tana amon zuza. Baƙaƙen /ʤ/, da /ʃ/, su ne a wannan ajin.

‘Ɗan Jirge

Shi ne baƙin da tsinin harshe yake haɗuwa da hanƙa sannan kuma su ware ba tare da jinkiri mai tsawo ba a yayin furta shi, saboda haka sai iska ta fita batare da wata tangarɗa ba. Harafin /l/, shi kaɗai ne a wannan ajin.

Ra-Gare/Ra-Kaɗe

Baƙi ne da idan aka zo furta shi, tsinin harshe yake garawa yana bugun hanƙa da saurin gaske, abin da ke haifar da katsewar iskar kaɗan-kaɗan wajen fita. /r/ ce kaɗai a wannan ajin.

Ra-Kaɗe/Ra-Buge

Baƙi ne wanda idan aka furta shi tsinin harshe yakan bugi hanƙa sau ɗaya rak, sai iskar ta fice.

/r/ wacce take a cikin kalmar randa ake kira da waɗannan sunaye. Wato Ra-kaɗe ko kuma Ra-Buge. Sannan kuma har yau ana alamta ta da /Ƴ/ ko /ȓ/, kamar yadda ya zo a mabambantan ruwayoyi.

Manazarta:


Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M (Babu Shekara). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Nigeria.

Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Sani M.A.Z., Muhammad A. Da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Langugae Don Masu Rubuta Jarabawar WASC da SSCE. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M da ‘Yar’aduwa T.M. (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub