Saƙa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Saƙa a Ƙasar Ibira


Kayan Aikin Saƙa

Sana’ar saƙa na ɗaya daga cikin daɗaɗɗu kuma muhimman sana’o’in ƙasar Ibira. Sana’a ce da suka gado ta tun zamansu cikin Jukunawa a Wukari. Ahmad (2011), ya ruwaito cewa, akwai sana’ar saƙa a ƙasar Ibira tun kafin ƙarni na goma sha uku. Lukman (2015), ya ce, wannan sana’a ta saƙa mata ne suka mamaye ta. A cikin rubutunsa ya ruwaito shugabar ƙungiyar Matan Ibira Masaƙa (masu sana’ar saƙa) tana cewa babu wani gida wanda ba a saƙa a gidan a duk faɗin ƙasar Ibira, kasancewarta sana’ar da uwa ke koyar da ‘yarta; babu wata mace da bata iya saƙa ba a ƙasar Ibira.

Okene da Suberu (2013), sun ruwaito cewa wannan saƙa ta Ibira ta taɓa zama mafi kyau da nagarta a duk faɗin yammacin Sudan kafin zuwan Turawa. Hakan kuwa ta faru ne saboda canje-canje, da sabunta launuka da tsari da sana’ar ta samu a ƙasar. Sun kuma ruwaito Henry Barth yana cewa wannan saƙa ta Ibira ta kere sa’a ta fuskacin launi, salo da kuma ƙyale-ƙyale. Barth ya kuma sake tabbatar da haka lokacin da ya ziyarci kasuwar Duniya ta Kurmi da ke Kano a wannan shekara. Haka nan kuma sun sake ruwaito Ahmadu Buruji Adoke wanda shi jami’i ne na Rundunar Sojan Najeriya reshe na biyu yana cewa, a lokacin da sutura ta yankewa sojojin Najeriya a filin daga zamanin yaƙin basasa, to wannan kayan saƙa na Ibira su suka samar musu da mafita.  Wannan sutura da ita aka yi amfani wajen yin belet ɗin sojoji da kuma kayan rufa. Haka nan kuma dab da bayan ƙare yaƙin ma tarayyar Najeriya ta sayi waɗannan kayayyaki dan amfanin sojoji.

Suna kiran abin da suke saƙawa da ‘Agidi’ da yarensu. Amma shi wannan Agidi ba komai bane illa saƙe da muka sani a ƙasar Hausa.

Manazarta:


Abdullahi, O.E. (1992). Cultural and identity crisis among Ebira Adolescents. Ilorin Journal of Education Foundations. Journal of Faculty of Education. University of Ilorin. 12.50-55.

Abdulƙadir M.S. (2011). Islam in the Non-Muslim Areas of Northern Nigeria, c.1600-1960, Department of History, Bayero University, Kano, Nigeria. Ilorin Journal of Religious Studies, (IJOURELS) Vol.1 No.1, 2011, Pp.1-20.

Audu S.M. (2010). Politics and Conflicts in Ebiraland, Nigeria: The Need for a Centralised Leadership Since 1917.  Journal of Sustainable Development in Africa. Volume 12, No.1, 2010), ISSN: 1520-5509, Clarion University of Pennsylvania, Clarion, Pennsylvania.

Attadescendant (2013). The Ebira Traditional Marriage Rite. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://attadescendantforum.wordpress.com/2013/03/ 17/the-ebira-traditional-marriage-rite/

David M.A. (2013). Ebira Youth Forum Association (E.Y.F.A). An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://ebirayouthforumassociation.blogspot.com.ng
/2013/05/history-of-ebira-people.html

Ekeh A. (2015). List of Traditional Marriage Requirements in Kogi. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://constative.com/people/lifestyle/list-of-traditional-marriage-requirements-in-kogi

Haruna M. (2012). Historical Background of Kente (Aso-Oke) in Okene Local Government Area of Kogi State. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://culturenaija.blogspot.com.ng/2012/07/historical-background-of-kenteaso-oke.html

Jimba M.M.M. (2012). Muslim of Kogi: A Survey. Nigeria Research Network (NRN), Oxford Department of International Deɓelopment, Queen Elizabeth House, University of Oxford

Kwekudee (2014). Ebira People: The Most Outspoken, Talented and Hardworking People of Kogi State In Nigeria. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://kwekudee-tripdownmemorylane.blogspot.com.ng/2014/03/ebira-people-most-outspoken-talented.html

Lukman I. (2015) Ebira. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://docilepen.blogspot.com.ng/p/blog-page.html

Mohammed, A.R. (1984), History of the Spread of Islam in the Niger-Benue Confluence Area: Igalaland, Ebiraland and Lokoja c. 1900-1960. Ph.D thesis submitted to Bayero University, Kano.

Okene A.A. da Suberu O.A. (2013). The British Conquest of Ebiraland, North Central Nigeria 1886-1917: A Military Interpretation of Sources. Professor (History & International Studies) Nigerian Defence Academy Kaduna, Africa’s Top Military University PMB 2109, Kaduna – Nigeria. American International Journal of Contemporary Research Vol. 3 No. 6; June 2013.

Segun J. A. (2013). Politics and Conflicts: a Study of Ebiraland, Nigeria (1977-2007). Department of Political Science and International Relations, School of Social Sciences, College of Development Studies, Covenant University, Ota, Nigeria.

Segun J. A. da Samuel O. (2010). Politics, Violence and Culture: The Ebira Tao Nigeria Experience. Bassey Andah Journal Vol3.

Tenuche M.S. (2002). Intra-Ethnic Conflict and Violence in Ebira Land, from the Selected Works of Marietu S Tenuche (PhD). Kogi State University, Anyigba.

Ukonga P.F.O. (2013). The imperatives of Ebira Unity of 40 million people to the development of Ebira Nation, Nigeria and sub Saharan Africa- A realistic perspectiɓe. Lecture delivered to the Ebira summit in Okene on the 30th March 2013.

Wikipedia (2016). Ebira People. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Ebira_people



Masarautar Okene

Sarakuna Ƙasar Ibira

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub