Gwamna Ibrahim Aliyu

Me ka ke nema?


Biegediya Janar Ibrahim Aliyu 1993 – 1996


Gabatarwa

Sunansa Ibrahim Aliyu, yana da muƙamin Birgediya Janaral (Brigadier General), amma ya yi ritaya.

Haihuw

An haife shi a ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 1947 a garin Yimirshika cikin ƙaramar hukumar Hawul ta Jahar Barno.

Karatu

Ya halarci makarantar firamare ta Yimirshika mai suna ‘CBM Primary School Yimirshika’, sannan ya wuce zuwa‘provisional secondary school’ da ke Maiduguri. Bayan kammala sikandire ne kuma kai tsaye ya wuce zuwa jami’ar sojoji ‘Nigerian Defence Academy’ da ke Kaduna shekarar 1968.

Shigarsa Aikin Soja

Dama duk wanda ya samu shiga makarantar 'Nigerian Defence Academy' to ya zama soja, saboda haka da kammala wannan karatu nasa a shekarar 1971, sai ya fita da muƙamin ‘Second Lieutenant’, daga baya kuma aka ɗaukaka darajarsa zuwa kyaftin (captain) a shekarar 1977. Bayan nan ma kuma ya samu damar zuwa kwasa-kwasai da horo iri-iri a wannan fanni nasa na soja. Daga ciki ya je Aberdeen ta Jahar Maryland ta ƙasar Amurka a shekarar 1979. An kuma ɗaga muƙaminsa zuwa manjo (major) a shekarar 1980, daga baya kuma aka yi masa muƙamin laftanal kanal (lieutenant colonel) a shekarar 1987, ya kuma zama kanal (colonel) a shekarar 1992.

Zamowarsa Gwamnan Jigawa

Ya zamo gwamnan jahar Jigawa na uku, sannan kuma na biyu a gwamnan soja, a shekarar 1993 bayan rugujewar gwamnatin riƙon ƙwarya ta shugaba Ernets Shonekan. Ya yi gwamnatinsa ƙarƙashin shugaba Muhammad Sani Abacha.

Barinsa Mulki

Ya bar kujerar gwamnan Jahar Jigawa a watan Agusta na shekarar 1996.

Barinsa Aikin Soja

Ya bar aikin soja yana matsayin birgediya janar (Brigadier General).


Gwamnoni


Masarautu

  • Dutse
  • Gumel
  • Hadejia
  • Kazaure
  • Ringim

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub