Gwamna Abubakar Zakariyya Maimalari

Me ka ke nema?


Colonel Abubakar Zakariyya Maimalari 1998 – 1999


Gabatarwa

Kanal Abubakar Zakariyya Maimalari, soja ɗan soja. Shi ne gwamnan Jahar Jigawa na biyar, sannan kuma na huɗu a jerin gwamnonin soja.

Haihuwa

An haife shi a watan Disamba na shekarar 1961 a garin Quetta na ƙasar Pakistan, a lokacin da mahaifinsa ke halartar wani horon soja.

Karatu

Ya yi karatunsa na firamare a makarantar ‘Kaduna Capital School’, daga nan kuma sai kwalejin Barewa (Barewa College) da ke Zariya daga shekarar 1974 zuwa 1978. Yana kammalawa a lokacin yana da shekaru goma sha takwas a duniya, sai ya shiga ‘Nigerian Defence Academy’.

Shigarsa Aikin Soja

Tun kammala karatunsa na makaranta 'Nigerian Defence Academy' ya fita da muƙamin ‘Second Lieutenant’ a watan Disamba na shekarar 1981, lokacin yana da shekara 20 kenan cif-cif a duniya. Daga nan ya ci gaba da samun ƙarin girma har zamowarsa gwamnan Jahar Jigawa.

Zamowarsa Gwamnan Jahar Jigawa

Kanal Abubakar Zakariyya Maimalari, ya zamo gwamnan Jahar Jigawa a watan Agusta na shekarar 1998.

Barinsa Mulki

Ya bar wannan kujera ta gwamnan Jahar Jigawa bayan ya gudanar da zaɓe ya kuma damƙa mulkin Jahar ta Jigawa a hannun Alhaji Ibrahim Saminu Turaki a shekarar 1999.

Barinsa Aikin Soja

Abubakar Zakariyya Maimalari ya bar aikin soja yana da muƙamin Kanal (Colonel).


Gwamnoni


Masarautu

  • Dutse
  • Gumel
  • Hadejia
  • Kazaure
  • Ringim

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub