Gwamna Olayinka Sule

Me ka ke nema?


Major General Olayinka Sule August 1991 – December 1991


Gabatarwa

An haifi Olayinka Sule a ranar 4 ga watan Mayu na shekarar 1943 a Sabon Garin Jahar Kano.

Karatu

A makarantar ‘Holy Trinity Primary School’ da ke Kano ya yi karatunsa na firamare, daga nan kuma ya zarce zuwa makarantar sikandire ta Ansaruddeen da ke Legas, bayan nan kuma ya je Kwalejin Aikin Gona (College of Agriculture) ta Akure, daga nan kuma sai ya tsunduma a Jami’ar Ibadan dan ci gaba da wannan karatu nasa na fannin gona.

Shigarsa Aikin Soja

A shekarar 1968 Olayinka Sule ya shiga aikin Soja. Bayan samun horo na soja da ya yi, ya riƙe muƙamai da dama.

Zamowarsa Gwamnan Jigawa

Shi ne gwamnan Jahar Jigawa na farko. Ya zama gwamna a ranar 27 ga watan Agusta na shekarar 1991, ya kuma samu isa wannan gari na Dutse, helikwatar mulkin Jahar ta Jigawa a ranar 30 ga watan Agusta 1991.

Gudunmawar da ya Bada

Ya bada gudunmawa sosai wajen kafa tubalin gina wannan jaha. Babban abinda ya fara aiwatarwa shi ne samar da matsugunnai da ofisoshin da ma’aikatan da jahar ta gada daga tsohuwar Jahar Kano za su tsugunna dan aiwatar da ayyukansu.

Bayan wannan kuma sai ya tusa buƙatar samar da ruwan sha gaba, dan tabbatar da walwala da jin daɗin Jama’ar wannan birni na Dutse, da kuma sababbin ma’aikatanta. Wannan ta tabbata ta hanyar samar da ma’aikatar ruwa ta Shuwarin.

Shi ne kuma gwamnan da ya sake tabbatar da masarautun Dutse da Ringim ya kuma naɗa musu sarakuna masu daraja ta ɗaya ƙari a kan Haɗeja, Gumel, da Kazaure da aka gada daga tsohuwar Jahar Kano.

Barinsa Mulki

Ya bar kujerar gwamnan Jahar Jigawa bayan ya gudanar da zaɓe ya kuma damƙa kujerar ga zaɓaɓɓen gwamna Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu a shekarar 1993.


Gwamnoni


Masarautu

  • Dutse
  • Gumel
  • Hadejia
  • Kazaure
  • Ringim

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub