Jahar Jigawa

Me ka ke nema?


Barka da Zuwa Jahar Jigawa



Jahar Jigawa mai helikwatar mulki a Dutse, wadda ake yi wa take da sabuwar duniya (New World). Jaha ce da aka ƙirƙireta a shekarar 1991 a zamanin mulkin Shugaban Najeriya Janaral Ibrahim Badamasi Babangida. Ita kuwa Dutse, wacce ita ce helikwatar mulkin Jahar, gari ne mai tsohon tarihi wanda ake fara lissafa shekarun kafuwar sa daga ƙarni na goma sha uku (13). Gwamnanta na Farko shi ne Manjo Janar Olayinka Sule. Gwamnan da kuma yanzu haka ya ke karagar mulki shi ne Alhaji Mohammed Badaru Abubakar.

A wannan shafin, cikin yardar Allah, za mu labarta muku wasu abubuwa game da wannan jaha mai albarka. Tare da cewa, wannan shafin yana a matsayin mabuɗi ne; wato shafin farko na jahar.

Jahar Jigawa, jaha ce mai masarautun gargajiya guda biya da suka haɗa da Masarautar Dutse, Haɗejia, Gume, Kazaure da kuma Ringim. Sai kuma yankunan 'Yanmajalisun Dattawa uku kamar kowace jaha a Najeriya; Jigawa ta tsakiya, kudu da kuma arewa.

Jahar Jigawa tana da ƙananan hukumomin mulki 27, waɗanda aka karkasa zuwa waɗancan shiyyo guda uku. Sannu a hankali, bayanai za su zo. Akwai majonai a jikin wannan shafi da za su kai mai karatu zuwa ga cikakke


Gwamnoni


Masarautu

  • Dutse
  • Gumel
  • Hadejia
  • Kazaure
  • Ringim

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub