Alhaji Abdukadir Balarabe Musa

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Abdulƙadir Balarabe Musa


Gabatarwa

Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa shi ne gwamnan farar hula na farko a jahar Kaduna, wanda ya yi wa'adin mulki daga 1979 – 1981. Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa mutum ne manomi, mawallafi, ƙwararren akawu (Chartered Accountant) sannan kuma ƙwararren ɗan siyasa mai aƙidar gurguzu (socialist).

Haihuwa

An haife shi a shekarar 1936 a garin Ƙaya, ta cikin ƙaramar hukumar Giwan jahar Kaduna.

Karatu

Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa ya yi karatunsa na firamare a makarantar elimantare (Elementary School) ta Giwa, daga 1943 zuwa 1947, daga nan kuma ya tafi makarantar tsakiya (Middle School) ta Zaria a shekarar 1947. Ya kuma yi kwas na shekara guda a makarantar harkokin mulki (Institute for Administration) ta Zaria, daga 1952 zuwa 1953. Daga nan kuma sai ya wuce Ingila don yi karatuttuka masu dama tun daga shekarar 1961 har zuwa 1969.

Gagayyar Aiki

Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa mutum ne mai ƙwazon aiki, ya yi ayyuka da dama da suka haɗa da aikin akawu, 1952, karantarwa 1955 zuwa 1960, akawun gidan radiyon Arewa (Broadcasting Company of Northern Nigeria) wanda yanzu ya koma radiyon Najeriya (Radio Nigeria) na Kaduna daga 1969 zuwa 1970, sakatare na gidan radiyon tarayya na Kaduna, babban akawu (Chief Accountant) na radiyon tarayya na Kaduna har zuwa 1976.

Gwamna

Bayan ya bar aikin gwamnati kuma sai ya shiga harkokin siyasa, abin da ya bashi dama aka zaɓe shi a matsayin gwamnan Jahar Kaduna a ƙarƙashin tutar jama'iyyar PRP (Peoples Redemption Party), jama'iyyar da aka kafa tare da shi bisa jagorancin Malam Aminu Kano. An yi wannan zaɓe a shekarar 1979. Bai cika wa'adin mulkinsa ba aka tsige shi sakamakon wata 'yar tangarɗa da ya samu da 'yan majalisarsa. Ya bar kujerar gwamna a shekarar 1981.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).



Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub