Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gwamnan Kano Abdu Baƙo 1968 – 1975



Gwamna Abdu Baƙo.

Gabatarwa

Alhaji Audu Baƙo shi ne gwamnan Jahar kano na farko. An haife shi a garin Kaduna a cikin barikin ‘yan sanda na Kaduna a ranar 24 ga watan Nuwamba na shekarar 1924 (24 November, 1924). Sunan mahaifinsa Malam Baƙo.

Karatu

Ya yi karatunsa a makarantar Gwamnati ta Kaduna (Kaduna Government School) da kuma Makarantar Tsakiya ta Zariya (Zaria Middle School).

Shigarsa Aiki Ɗansanda

Bayan kammala wannan karatu nasa sai ya shiga aikin Ɗansanda (wato ya gaji mahaifinsa kenan), a shekarar 1942.

Bayan zamowarsa Ɗansanda, a shekarar 1954, ya samu halartar Makarantar Horas da ‘Yansada (Metropolitan Police Training School) da ke United Kingdom. Haka nan kuma dai a shekarar 1955 ya samu nasarar komawa Landan (London) dan samu wani horon a kan (forensic science course).A cikin shekarar 1958, ya sake zuwa United Kingdom dan halartar kwas a makarantar (Ryton Oudunesmore), inda ya samu horo na Babban Jami’in Ɗansanda (Senior Police Officer Course). Haka nan kuma a shekarar 1959, ya samu horo a kan Babban Jami’in Kwalejin ‘Yansanda (Police College Senior Officer). A cikin 1962 kuma, ya sake samun horo a fannin Kula da yankin birni na ‘Yansanda (Metropolitan N.4 District-Directing Office). Duka waɗannan biyun ƙarshen a Najeriya ya yi su.

Gogayyar Aiki

Kafin zamowarsa Kwamishinan ‘Yansanda, muƙamin da shi ya kai shi zama gwamna a Kano, sai da ya zama mataimakin kwamishinan ‘yansanda mai kula da dukkan lardin Arewa. Ya kuma taɓa zama wakilin Najeriya kan harkar zaman lafiya a ƙasashen Afirka ta Yamma ƙarƙashin Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka (OAU). Sannan ya taɓa zama malamin da ke koyar da abin da ya shafi doka a kwalejin ‘Yansanda ta Kaduna.

Zamowarsa Gwamnan Kano

Shi ne ya kafa tubulin ginin jahar Kano. Duk da cewa tun kafin Kano ta zama Jaha, Masarauta ce mai kyakkyawan tsari.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Savannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Eɗecutive Governor, Government House, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

Obii-Mbta R.A. (1994). Alhaji Ado Bayero and the Rorayl Court of Kano. Carpricorn 25 Limited. Kano-Nigeria.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub