Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, 2015 zuwa yauMai Girma Gwamnai Dr. Abdullahi Umar Ganduje Ganduje, OFR, Khadimul Islam.

Gabatarwa

Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje OFR, mutumin garin Ganduje ne ta cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa. Ɗan siyasa, gogaggen ma’aikaci, masanin mulki a ilimance kuma a aikace, ya yi kwamishina har sau biyu, sannan kuma ya yi mataimakin gwamna shi ma sau biyu, yanzu kuma yana zaune daram a kan kujerar gwamnan Kano.

Matum ne shi mai haƙuri, kawaici, da kuma biyayya ga duk wanda ya grime shi ta kowace fuska wanda ka iya kasancewa girma na shekaru ko na harkar aiki.

Haihuwa

Shi ɗa ne ga dagacin garin Ganduje ta cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa. An haife shi a ranar 25 ga watan Disamba na shekarar 1949. Cikakken sunansa shi ne Abdullahi Umar Ganduje, sannan kuma ana yi masa laƙabi da ‘Bandirawo’ saboda kasancewarsa ɗan ƙabilar Fulani.

Karatu

Abdullahi Umar Ganduje ya buɗi ido da karatun Alƙur’ani da kuma na Islamiyya. Ya yi karatunsa na firamare a makarantar firmare ta Dawakin Tofa tun daga shekarar 1956 har zuwa 1963. Daga nan kuma sai ya samu nasarar shiga makarantar Kwalejin Gwamnati ta Birnin Kudu (Birnin Kudu Government College) daga shekarar 1964 zuwa 1968. Sannan kuma sai babbar makarantar horas da malamai(Advance Teachers College, Kano) da ke Kano tun daga 1969 har zuwa 1972 inda ya samu takardar shedar ‘NCE’ (Nigerian Certificate of Education). Daga nan kuma sai ya sake zarcewa zuwa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, inda ya samu karatunsa na digiri a fannin Ilimin Kimiyya (Bachelor’s Degree in Science Education) daga shekarar 1972 zuwa 1975. Bai tsaya nan ba sai ya sake wucewa zuwa Jami’ar Bayero da ke Kano (Bayero University Kano) inda nan kuma ya yi digirinsa na biyu a fannin ‘Applied Educational Psychology’ inda ya kammala a shekarar 1979. Ya kuma sake komawa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya inda ya sake yin wani digiri na biyun kuma a fannin ‘Public Administration’ daga shekarar 1984 zuwa 1985. Daga ƙarshe kuma ya je Jami’ar Ibadan, inda ya yi ‘PhD in Public Administration’ daga shekarar 1989 zuwa 1993.

Gogayyar Aiki

Karatuttukan da Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje OFR ya yi a fannonin Ilimi da mulki kamar yadda aka gani, basu tsaya iya takarda kawai ba, sai da ya aikata su a aikace. Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, ya fara aiki da  hukumar ilimi ta jahar Kano a matsayin ‘Education Officer II’ a shekarar 1976. Sannan kuma ya koma makarantarsa ta ‘Advance Teachers’ College, Kano’a matsayin lakcara (Lecturer I) mai karantar da ‘Educational Psychology’. A shekrar 1978 Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya sake samun komawa tsohuwar Jami’arsa ta Bayero da ke Kano nan ma a matsayin Lakcara (Lecturer I). Ya bada gudunmawa a wannan fanni na ilimi tsawon shekara biyar.

Ya yi aiki da ‘Federal Capital Development Authority’da ke Abuja a matsayin ‘Admin Officer’. A shekarar 1993 aka ɗaukaka darajarsa zuwa  ‘Director Planning, Research and Statistics’. An kuma sake ɗaukaka darajarsa zuwa ‘Development Secretary’ na Kwali ‘Development Area’ sai kuma Kantoma (Sole Administrator) na Abaji ‘Area Council’ sannan kuma aka yi masa ciyaman (Chairman) na Gwagwalada ‘Area Council’. Ya zama ‘Eɗecutive Secretary’ na ‘FCT resettlement and compensation’, dukkan waɗannan muƙamai da ma waɗanda ba a ambata, Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya taka su a tsawon zamansa na aiki da wannan hukuma ta ‘FCDA’ a cikin shekaru goma sha bakwai.

Bayan barowarsa waccar Hukuma ta ‘FCDA’, an yi masa kwamishina na Ma’aikar Ayyuka, Gidaje, da Sufuri ta Kano (Ministry of Works, Housing and Transport Kano State), muƙamin da ya riƙe tun daga Janairun 1994 har zuwa Nuwambar 1998.

Siyasarsa

Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya fara siyasa tun a jamhuriya ta biyu, inda ya shiga jama’iyyar National Party fo Nigeria (NPN). A wannan jama’iyyar ya riƙe muƙamin mataimakin sakatare na jahar Kano daga 1979 zuwa 1980.

Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya sake shiga jama’iyyar PDP a shekarar 1999, Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya canja sheƙa tare da gwamnansa Engineer (Dr.) Rabi'u Musa Kwankwaso, inda suka fice daga jama'iyyarsu ta PDP suka koma sabuwar jama'iyyar haɗaka ta APC, wanda a ƙarƙashin tutar wannan sabuwar Jama'iyyar ya samu nasarar cin zaɓensa na gwamna.

Takara

Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya tsaya takarar Kujerar Gwamnan jahar Kano a shekarar 1999, inda daga baya aka yi musu sulhu ya janye ya barwa tsohon Gwamna kuma Sanatan Kano ta Tsakiya, (Dr.) Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda shi kuma daga baya ya ɗauke shi a matsayin mataimakinsa.

A shekarar 2015, Dr. Alhaji Umar Ganduje, ya sake tsayawa takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin tutar jama’iyyar APC.

Mataimakin Gwamna

Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, ya samu nasarar zamowa mataimakin gwamnan jahar Kano bayan lashe zaɓen da aka gudanar da suka yi, shi da tsohon gwamnan Kano Engineer (Dr.) Rabi’u Musa Kwankwaso. Ya zauna a kan wannan kujera tun daga shekarar 1999 har zuwa 2003.

Ya sake zama mataimakin gwamna a karo na biyu, bayan da suka ci zaɓe a karo na biyu shi da Engineer (Dr.) Rabi’u Musa Kwankwaso. Sun fara wannan sabon zangon mulki a shekarar 2011, suka kuma ƙare shi a 2015.

Wasu Muƙaman

Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, ya riƙe wasu muƙaman siyasa ƙari akan waɗanca da aka ambta, daga ciki akwai riƙe:

  1. Ofishin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi (Commissioner for Local Government) daga shekarar 2003 zuwa 2007. Haka nan ma ya sake riƙe wannan ofishi na Kwamishinan Ƙananan Hukumomi daga 2011 zuwa 2015.
  2. Ya zama mai bada shawara na musamman ga Ministan Tsaro na Nijeriya, Engineer (Dr.) Rabi’u Musa Kwankwaso (Special Adviser (Political) to the Hon. Minister of Defence, Federal Republic of Nigeria), muƙamin da tun da Nijeriya take a kansa aka fara yinsa.
  3. Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, ya zama mamba na ‘Nigerian Civil Aviation Authority (NCAA)’
  4. An zaɓe shi a matsayin ciyaman na ‘Federal Polytechnic, Ado Ekiti’ a shekarar 2008.
  5. Sannan kuma an yi masa muƙamin ‘Executive Secretary Lake Chad Basin Commission’ da ke Ndjamena, ta ƙasar Chadi.
  6. Ciyaman na ‘TABITAL FUAKU Nigeria’ mai kula da Afirka ta Tsakiya da Afirka ta Gabas (East and Central Africa sub-region) wacce ƙungiya ce mai fafutikar kare haƙƙin Fulani makiyaya.
  7. A shekarar 2006, ya zama mamba na ‘Nigerian Political Reforms Conference’.

Gwamnan Kano

Dr. Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, ya samu zama zaɓaɓɓen gwamnan jahar Kano bayan da ya lashe zaɓen da aka gudanar a shekarar 2015 a ƙarƙashin tutar jama’iyyar APC. Wannan kujera ta gwamna, ita ce kujerar da yake kanta har zuwa yau ɗin nan (2016).

Manzarta:


Nigerian Biography (2015). Biography Of Abdullahi Umar Ganduje. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.nigerianbiography.com/2015/04/biography-of-abdullahi-umar-ganduje.html

Politicoscope. (2016). Nigeria: Abdullahi Umar Ganduje Biography And Profile. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: http://www.politicoscope.com/2015/08/03/nigeria-abdullahi-umar-ganduje-biography-and-profile/

Progressive Governors Forum Eɗplained (2015). 9. Dr. Abdullahi Umar Ganduje of Kano State. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.nigerianbiography.com/2015/04/biography-of-abdullahi-umar-ganduje.html

Wikipedia (2016). Abdullahi Umar Ganduje. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Abdullahi_Umar_Ganduje


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub