Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gwamnan Kano Kabiru Ibhrami Gaya 1992 - 1993



Kabiru Ibhrami Gaya

Gabatarwa

Alhaji Kabiru Ibrahim Gaya, shahararren mai zanen taswirar gine-gine ne, tsohon gwamnan jahar Kano, kuma Ɗanmajalisar Dattawan Najeriya mai wakiltar Kano ta Arewa. Shi ne gwamnan jahar Kano na 11. An haifi Alhaji Kabiru Ibrahim a garin Gaya a cikin shekarar 1952.

Karatu

Ya halarci makarantar firmare ta gaya (Gaya Primary School) daga shekarar 1961 zuwa 1964, daga nan aka tura shi makarantar firamare ta Tsanyawa (Tsanyawa Primary School) da ke ƙaramar hukumar Bici a lokacin, wanda kuma yanzu ta zama ƙaramar hukuma mai cin gashin kanta. Ya yi karatu a wannan firmare daga 1964 zuwa 1968. Bayan kammala wannan karatu a Tsanyawa sai kuma aka sake tura shi zuwa Kwalejin Gwamnati (Government College Birnin Kudu) da ke Birnin Kudu wacce yanzu ta ke cikin jahar Jigawa. Daga Birnin Kudu sai Babbar Kwaleji (College of Advance Studies) ta Kano, wacce yanzu ta koma makarantar share fagen shiga jami’a (College of Arts, Science and Remedial Studies) a shekarar 1974. Ya wuce zuwa jama’iar Ahmadu Bello ta Zariya, inda ya yi karatun digirin farko da na biyu duka a fannin zanen taswirar gidaje (Arcitecture) daga shekarar 1975 zuwa 1979.

Gogayyar Aiki

Bayan Kammala karatunsa, Alhaji Kabiru Ibrahim Gaya ya zama malami (lecturer) a kwalejin fasaha ta Kano (Kano State Polytechnic). Daga nan kuma sai ya tsallaka zuwa hukumar albarkatun ruwa da aikace-aikacen injiniyarin (Kano State Water Resources and Engineering Construction Agency) a matsayin babban mai zane-zanen taswirar gidaje (senior architect). Daga nan sai ma’aikatar gona inda ya ɗan yi aiki a matsayin jami’i mai kula da kayan amfani sannan kuma tare da saka ido a harkar dajin Falgore.

Bayan ya bar aikin gwamnatin, an naɗa shi a matsayin mamba na bod (Board member) a hukumar tsarawa tare da kula da muhalli (Kano State Environmental Planning and Protection Agency) ta jahar Kano.

Zamowarsa Gwamnan Kano

An zaɓe shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jahar Kano ƙarƙashin tutar jama’iyyar NRC a zaɓen da aka gudanar a shekarar 1992.

Gudunmawar da ya Bada

Duk da cewa gwamnatinsa bata kasance mai tsawo ba, amma dai ya bar abubuwan ambato kuma abubuwan koyi. Ya yi amfani da salon mulki na ɗorawa daga inda aka tsaya. Salon mulkin da aka rasa a Nijeriya. Inda a ce gwamnatocin Nijeriya suna bin irin wannan salo, ai da ba kwaɗo ba in ji gaya.

Shi ya kammala aikin ginin asibitin Ƙiru da Shanono. Ya kuma kawo motocin sufuri ɗari ga hukumar sufuri ta jahar Kano. An saka guda 32 kai tsaye ga kamfanin sufuri na jahar Kano (Kano Line), sannan kuma aka raba 68 ga ɗaiɗaikun mutane su biya a hankali. Haka nan kuma ya kammala ginin makarantun kimiyya na ‘yanmata da ke Ƙiru da Garko, sannan kuma ya tabbatar da fara amfani da su.

Shi ya ƙararasa aikin ginin asibitin dabbobi guda biyu waɗanda ɗaya ke a garin Tudun Wada na ƙaramar hukumar Tudun Wada, ɗayan kuma a garin Dawakin Kudu cikin ƙaramar hukumar ta Dawakin Kudu. Sannan kuma ya kammala aikin ƙananan titunan da yawansu ya kai 129 wanda tsawonsu ya kai jimillar kilomita 2158, da kuma ayyukan rijiyoyi da birtsatsen da yawansu ya kai 720 duk a ƙarƙashin hukumar DFFRI.

Sannan kuma shi ya kammala aikin samar da ƙaramar tashar talabijin ta Kano wacce ake yi a ƙarƙashin KBC, inda aka samu tagwan tashoshin CTV 67, da kuma CTV 2.

Barinsa Gwamna

Ya bar kujerar gwanman jahar Kano bayan soke jamhuriya ta uku da shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ya yi a shekarar 1993.

Manazarta:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Executive Governor, Government House, Kano.

Danyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taxation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

Yakasai T. (2004). Tank Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, Volume I. Goverment Printers, Kano-Nig


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub