Hausa Karatun Allo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Karatun Allo


Gabatarwa

Makarantar allo, ita ce tsohuwar hanyar koyo da koyar da karatun Al-Ƙur’ani a ƙasar Hausa. A garuruwa kamar Kano da Katsina.

A Kano ana sa ran shigowar wannan karatu tun kusan shekaru ɗari shida da sittin a baya, zamanin sarki Yaji Ɗan Tsamiya (1349 – 1385) lokacin da Fulani Wangarwa suka zo garin na Kano.

A Katsina kuma, ana ganin tun shekaru ɗari shida da sittin da uku baya da suka gabata a zamanin Sarki Muhammadu Korau (1384 – 1398) lokacin da Sheikh Abdurrahman Zaite da jama'arsa suka je Katsina.

Wannan makaranta a cikinta ake koyon karatu, rubutu da kuma haddace shi Al-Ƙur’anin baki ɗaya. Malaman makarantar allo su suke rubuta Al-Ƙur’ani kodai da ka, ko kuma ta hanyar mai-da-kama.


Almajirai Suna Karatu a kan Girgir a Makarantar Allo

Tsarin Makarantar Allo

Makarantar allo makaranta ce mai tsari sosai. Asali iyaye kan kai yara wannan makaranta kuma yaran da ake kaiwa sai sun kai shekaru shida ko bakwai wanda a wannan lokacin idan namiji ne an yi masa kaciya kenan. Idan aka kai yaro to shike nan yaro ya zama ɗanmakaranta da ake kira almajiri.

Waɗannan ɗalibai kala biyu ne, akwai waɗanda ke kwana a makaranta, akwai kuma waɗanda suke zuwa daga gidajensu su yi karatu su koma (kamar dai yanzu yadda ake da tsarin makarantar kwana da kuma jeka-ka-dawo a makarantar boko).

Lokutan Karatu

A makarantar allo ana karatu kusan sau biyar a kowace rana.
 1. Ana fara zama a ƙarshen dare dab da sallar Asuba (misalin karfe huɗu na asuba kenan a yanzu) har zuwa wayewar gari. Ana cikin wannan karatu ake tashi a je a yi sallar Asuba sannan a dawo a ci gaba da karatu har zuwa wayewar gari. Idan gari ya waye, sai kuma a ɗumama guntun tuwon da ya kwana a ci. Wannan tuwo shi ake ƙira gajala.
 2. Lokaci na biyu shi ne idan hantsi ya yi, sai kuma a tafi wajen gari a shiga Kisƙali (ɗaki ne da ake yinsa a wajen gari da ciyawa da kara), ko kuma a zauna a gindin bishiya. Wannan lokaci yakan zarce har zuwa tsakiyar rana. Daga nan kuma sai a tafi hutu idan rana ta zo tsakiya. A cikin wannan hutu ake neman abinci a ci, idan kuma akwai abincin a ajiye sai a ɗauka a ci.

 3. Cisƙadi/Kisƙali/Cisƙali

 4. Lokaci na uku kuma shi ne bayan sallar Azahar. Idan aka yi sallar Azahar sai kuma a sake zama. Wannan lokaci yakan kai har zuwa kusan da faɗuwar rana. Shima wannan lokaci ana cikin karatu ake tashi a yi sallar La’asar.
 5. Sai kuma bayan sallar Magariba. Ana idar da sallar Magariba ake zama na ɗan gajeren lokaci kafin sallar Isha (Idan aka kwatanta da zamani, tsawon wannan karatu baya wuce rabin awa). Wannan shi ake kira karatun Magariba.
 6. Sai kuma bayan sallar Isha. A kan zauna wannan karatu bayan sallar Isha har zuwa ɗaya bisa ukun dare na farko. Wannan karatu shi suke kira ja-dare. Sai dai, akan samu wasu su ma zarce da karatun basa barci. Sannan kuma duk wanda barci ya rinjaya koda ba a kai lokacin tashi ba yakan tashi ya je ya yi.
Waɗannan matakai guda biyar su ne abin da aka sani game da lokutan karatu a makarantar allo ta asali. Haka nan ƙolo da tittiɓiri basu cika yin ja-dare ba.

Tsarin Shugabanci

Sanannen abu shi akan samu unguwa guda da ake kira Tsangaya wacce nan ce cibiyar karatun Al-Ƙur’ani a gari. Baƙin malamai, gardawa, da ‘yan gari nan suke zuwa dan koyo da kuma koyar da karatun Al-Ƙur’ani. Saboda haka akwai kyakkyawan tsarin shugabanci a ciki. Yana da matakai kamar haka:
 1. Uban Tsangaya: Uban tsangaya shi ne asalin wanda ya kafa wannan tsangaya. Saboda haka shi yake zamowa mai faɗa-a-ji na ƙarshe. Wato shi ne sama da kowa a wannan tsangayar. A wasu lokutan ma akan kira tsangayar da sunansa. Misali, a ce ‘Tsangayar Malam Sale’.
 2. Maidarasu: Mutum na biyu a tsarin shugabancin tsangaya shi ne Maidarasu; malamin da ke bayar da karatu ga gardawa waɗanda a cikinsu wasu ma alarammomi ne. Sai dai, ana raba wannan matsayi ne da na Uban Tsangaya idan ya zama shi Uban tsangayar ba shi da isasshen karatun da zai bayar da darasi. Amma idan Uban tsangaya ya zama yana da karatun da zai bayar da darasu, to shi ne kuma yake zamowa Maidarasu a wannan tsangaya tasa.
 3. Shugaban Gardawa: Muƙami na ƙarshe shi ne jagorancin dukkan almajiran tsangayar wanda suka haɗa da ƙolo, tittiɓiri, gardi, da kuma sauran alarammomi. Dukkan su suna ƙarƙashin shugaban gardawa. Akan zaɓi gardi maras tsoro kuma ƙaƙƙarfa a ɗora masa wannan nauyi. Shugaban gardawa shi yake da alhakin kula da zirga-zigar sauran almajirai ‘yan’uwansa. Ba kasafai ake zuwa gaban Uban tsangaya da matsala ba sai ta tsananta.


Allon Karatu

Horo

Akwai matakan horaswa da ake ɗauka a makarantar allo a kan duk wanda ya saɓawa tsari ko yake ƙoƙarin fanɗarewa. Matakan sun kama tun daga matakin yin nasiha, gargaɗi, duka, tsarewa a ɗaki, saka mutum a turu, ƙauracewa, dakatarwa, har zuwa matakin kora daga makaranta baki ɗaya.

Sana’o’i

Yawancin sana’o’in gardawa su ne ɗinki (ɗinki hula da kuma aikin riga kamar kufta ko babbar riga), saƙa, rini, noma da kuma jima (sai dai jima da rini a can lokutan baya masu tsawo aka fi yin su).

Ana Gudanar Da Karatu A Makarantar Allo

Tsarin Koyon Karatu

Akwai matakai goma sha ɗaya zuwa sha biyu da ake ɗauka na koyon karatun Al-Ƙur’ani a makarantar allo. Idan aka kammala irin waɗannan matakai, to, daga ƙarshe akan zama gwani ko kuma gangaran kamar yadda zamu kawo su daki-daki.
 1. Gwaji: Shi ne matakin farko da ake ɗora sabon almajiri mai shekaru shida ko bakwai a kai. Ana farawa da koya masa karatu da baki. Manufar wannan mataki shi ne a gane cewa yaron zai iya yin karatun ko kuwa ba zai iya ba. A wannan mataki ana koya masa karanta Fatiha ne zuwa Alamtarakaifa da ka.
 2. Babbaƙu: Mataki na biyu shi ne matakin babbaƙu. Idan yaro ya iya kammala wancan mataki na farko, to sai kuma a kawo shi mataki na biyu, wato an gane zai iya koyon karatun kenan. A wannan mataki ana rubutawa almajiri harrufan Al-Ƙur’ani ne tun daga A’uzu billahi har zuwa Alamtarakaifa. Akan kira shi da Alu-Ambaki waw zal (ا عو ذ) . Almajirin da yake wannan mataki shi ake kira ƙolo.
 3. Farfaru: Shi ne mataki na uku. A wannan mataki ake koya wa almajiri yadda ake haɗa sautin Al-Ƙur’ani. A nan almajiri yana maimaita mataki na biyu ne amma kuma ana yiwa baƙaƙen wasali (اَ عُوْ ذُ ). Dukka wannan ƙolo ne yake yin su.
 4. Hajjatu: Shi ne mataki na huɗu. A wannan mataki ake koyawa almajiri haɗa jimla, furta kalmomin Al-Ƙur’ani da kuma yin rubutu. Shi ma dai waɗancan surori da ya yi a mataki na biyu da na uku su yake sake maimaitawa. Amma yanzu, sautin yake faɗa. Sannan kuma ana koya masa gaɓa-gaɓa ne da farko, idan ya kai Alamtarakaifa, sai a koma ana koya masa aya-aya, sannan kuma a ba shi dama ya fara rubutu. Haka zai yi ta yi har sai ya kai Sabbi; izu guda kenan. To idan ya zo wannan mataki ana sa ran zai samu abubuwa uku; iya haɗa baƙi, rubuta shi da kuma hadda. Idan ya iya wannan, to ya zama tittiɓiri kenan.
  Haka zai yi ta tafiya, yana rubutawa ana gyara masa, yana haddacewa har sai ya kai izu goma, amma wajen rubutun idan aka zo gajeruwar sura za a rubuta ta baki ɗaya, idan kuma doguwa ce sai a rabata biyu ko uku gwargwadon fahimtar ɗalibi. Ana tabbatar da haddarsa ne idan ya miƙa allon ga malam sannan ya kawo karatun da ka.
 5. Sare: Shi ne mataki na shida, a wannan mataki ne almajiri yake rubuta simini-simini a jikin allonsa ta hanyar saro izun da ke gaba, sannan ya iyo baya. Misali, Suratul Ahƙaf, ba zai rubuta suratul Jathiya ba sai ya wuce suratul Zukhrufi kan izu (قَلَ أَوَلَوْ جِعْتُكُمْ...) ya faro daga can ya gangaro ya haɗe da surar Ahƙaf ɗin, sannan ya sake saro izu na gaba, da haka-da-haka sai ya kai Baƙara. Idan ya gama wannan sai a ce ya yi saukar sare, sannan kuma ya zama Gardi.
 6. Ture: Shi ne mataki na shida. A wannan mataki gardi zai sake juyowa da karatu ne daga Baƙara zuwa Nasi. Wato zai turo karatun kena zuwa ƙasa. A wannan mataki ana yin tilawa ne tare da hadda. Wannan mataki shi ke ƙara goge tilawar gardi. Gardi zai riƙa rubuta rubu ko nisfu (ɗaya bisa huɗu na izu, ko nisfu, wato rabin izu) gwargwadon basira.
  A wannan mataki gardi yake yin gallari (gallari shi ne haɗa alluna biyu); zai samu alluna guda biyu, ɗaya na hadda ɗaya kuma na gwaji. Wato gardi zai yi ainihin rubutun da zai riƙa zuwa ana biya masa, sannan ya haddace. Idan ya haddace kafin ya je gurin malam sai ya ɗauko wancan ɗaya allon ya rubuta da kansa ba tare da ya kalli takardu ko wani allon ba, sannan ya ɗauko allonsa na asali ya duba ya ga gurin da ya yi kuskure tun kafin ya je gaban malam.
  Wanda ya yi wannan sauka ta Ture, shi ake kira alaramma (amma shima alaramman a matakin farko).
 7. Satu: Mataki na bakwai kuma shi ne matakin Satu; wanda shi ne matakin da alaramma zai riƙa rubuta izu guda ko rabin izu (nisfu) da ka a jikin allonsa ba tare da ya duba takardu ba (wato zai ajiye allon gallari kenan). Sannan ya je gurin malam ya yi darasu. Idan ya je sai malam ya riƙa karantawa shi kuma yana bi, idan aka zo gurin da gyara yake sai malam ya nuna masa, shi kuma ya gyara sannan ya kiyaye. Ana maimaita wannan mataki har sau biyu ko uku, ko ma sama da haka gwargwadon fahimta (wato ana yin sauka daga Baƙara zuwa Nasi sau biyu ko sama da haka).
 8. Karya Takarda: Mataki ne da alaramma ke fara rubuta Al-Ƙur’ani dukkansa da ka, banda Fatiha ita kaɗai. A wannan mataki zai rubuta dukkan Al-Ƙur’anin a jikin takarda, sannan ya kai wa malaminsa ya rubuta masa Fatiha sannan kuma ya gyaggyara masa. Idan gyare-gyaren basu yawaita ba, sai a yi masa izinin ci gaba da rubutu. Idan kuma suka yawaita, to sai a umarce shi da ya wanke allo, sannan ya sake komawa makaranta.
 9. Shan Fari: Wannan mataki ne na tishi. A nan alaramma zai riƙa rubuta izu guda da ka, sannan ya ɗauka ya tafi wajen darasu. Idan aka biya ba gyara, to sai ya ci gaba da haka har sai ya sauka. Bayan ya gama shan fari kuma, sai shima a yi masa izinin yin darasi. Wato ya zama cikakken malami kenan da zai riƙa bayar da darasu.
 10. Gwani: Shi kuma mataki ne da ake taka shi ta hanyar iya rere karantun Al-Ƙur’ani wanda ake samu saboda yawan maimaita karatun. Ana hawa wannan mataki ba sai lallai da hadda ba. Mutumin da ya ƙware wajen rera karatun Al-Ƙur’ani; wato ya iya furta harrufan a yayin rera karatu, shi ake kira gwani. Akan samu gwani amma kuma bashi da tilawa.
 11. Gangaran: Mataki ne da sai mai hadda yake hawansa. Wanda ya samu hadda mai ƙarfin da bai cika yin kuskure ba; wato idan ana tukuri ba a cika kama shi ba koma ba a kama shi, to shi ake kira gwani. Ba lallai ne gangaran ya zama gwani ba, kamar yadda yake ba kowane gwani ne gangaran ba.


Ɗalibai a Makaranta Suna Karatu

Manazarta:


Fago S.I. da Usman Y.B. (2010). Issues in the Impact of Islam on Hausa Land in the 21st Century. The Nigerian Academic Forum Ɓolume 19 No. 2 November, 2010.

Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Printing and Publishing.

Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

Tattaunawa a ranar 11 da 12 ga watan Nuwamba na shekarar 2016, tare da Malam Sale Mai-almajirai, Rimin Kebe, Ƙaramar Hukumar Ungogo, Jahar Kano, Najeriya.

Darrusan Hausa

 • Darrusan Hausa

 • Musulunci


  Ƙasar Hausa  Zuwan Turawa


  Tarbiyya


  Bukukuwa


  Wasanni


  Kayan Kiɗan Hausa  Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


  Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin  Sauran Shafukanmu:

  Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub