Sana'ar Kira

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar Ƙira


Gabatarwa

Sana’ar Ƙira tana daga cikin daɗaɗɗun sana’o’in ƙasar Hausa. Maƙera su ke samar da mafiya yawan kayan aikin da sauran masu sana’o’in Hausa ke amfani da su. Gurin da ake yin wannan sana’a shi ake kira maƙera. Haka nan ma mai yin ƙira akan kira shi da maƙeri (mutum ɗaya kena) ko kuma maƙera (jama’u kenan).

Sana’ar Ƙira sana’a ce da ake sarrafa tama da ƙarafa, zinariya ko azurfa, da sauran dangogin ƙarfe a mayar da su abin amfani wanda ka iya zama makami ko ma’aikaci (abin yin sana’a).

Rabe-Raben Ƙira

Sana’ar ƙira ta kasu kashi biyu bisa la’akari da abubuwan da ake ƙerawa. Akwai ƙirar fari, akwai kuma ƙirar baƙi.

Ƙirar Fari

Ƙirar fari ita ce ƙirar kayan alatu (kayan kwalliya na mata kamar ɗan-kunne, sarƙa, da sauransu, da kuma kayan adon ɗaki kamar irinsu kumbo, da kuma kayan adon dawaki, da sauransu) da kuma sauran ƙanan kayan aiki. Maƙeran fari su ke ƙera kayayyaki kamar irin su abin hannu na mata, askar wanzamai, da sauran abubuwan alatu.

Ƙirar Fari

Ƙirar Baƙi

Ita ce gama-garin ƙira. Ta hanyar wannan ƙira ake ƙera kayayyakin amfanin yau-da-kullum kamar irin su fartanya, garma, takobi, da sauransu.

Ƙirar Baƙi

Kayan Aiki

  1. Maƙera: Ƙarfe ne dunƙulalle, a kanta ake bugun ƙarfen da ake son ƙerawa ya zama wani abu bayan an fito da shi daga wuta.

  2. Maƙera

  3. Zugazugi: Fatar akuya ce ko tinkiya ake yi mata jima ta musamman sannan a saka mata ƙota da ƙarfe a bakin ƙotar. Da su ake iza wutar ƙira.

  4. Zugazugi

  5. Guduma:  Ƙarfe ne ake yi masa ƙota. Da ita ake dukan ƙarfen da ake son ƙerawa bayan an ɗora shi a kan maƙera.

  6. Guduma

  7. Masaba: Abin bugun ƙarfe ce da ake yin ta da zallar ƙarfe.

  8. Masaba

  9. Awartaki ko Araftaki: Ƙarfe ne ake yin sa dan ɗauko ƙarfe daga wuta.

  10. Awartaki/Araftaki

  11. Gawayi: Shi ne makamashin wuta.
  12. Tama: Sinadari ne da ake yin ƙarfe da shi.
  13. Ƙarfe: Shi ake ƙerawa.
  14. Kasko: Ana zuba ruwa a ciki da wasu lokutan ake tsoma ƙarfen da ake son rage wa zafi.
  15. Kurfi: Da shi ake sara ƙarfe.

  16. Kurfi

  17. Gizago: Ana sassaƙe ƙota da shi idan buƙatar hakan ta taso.

  18. Gizago

  19. Matsoni: Da shi ake yin huda (ƙofa) a jikin ƙarfe.

  20. Matsoni

  21. Madashi: Da shi ake huda ƙota bayan an saka shi a wuta ya yi ja.

  22. Madashi

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.

Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Services (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.

Madauci I., Isa Y., da Daura B. (1968) Hausa Custom. Northern Nigerian Publishing Compnay, Zaria-Nigeria.

Yakasai K.I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cikinsa (Babu Sunan Maɗaba’a).

Zarruƙ R. M., Kafin Hausa A. A. da Al-Hassan B. S. Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press, Ibadan.

Tattaunawa da Hussaini Shu’aibu a Ranar 9/11/2016, a Garin Farken Yamma, cikin Ƙaramar Hukumar Minjibir, Jahar Kano a Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub