Sana'ar Sussuka

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar Sussuka


Gabatarwa

Sana’ar sussuka ko casau, sana’a ce da ake cire kayan amfanin gona mai ƙwaya kodai daga jikin zangarniya ko kuma daga cikin kwanso/ɓawo. Misali, akan cire wake daga jikin ɓawonsa, gyaɗa kuma daga cikin kwansonta. Amma dawa, gero, masara, maiwa da sauran dangoginsu su kuma daga jikin zangarniyarsu ake cire su.

Akan ware wani fili na musamman domin yin wannan aiki na sussuka mafiya yawancin lokuta filin kan kasance a bayan gari ko kuma a can gefen gida a irin gidaje na zamanin da can. Wannan fili shi ake kira masussuka. Ƙaiƙayin da aka fitar daga jikin dangogin hatsi, da kuma kowar wake, sukan zama na ita mai sussukar. Ita kuma bayan ta ƙare sai ta ɗure a buhu ta sayar da shi ga masu sana'ar kiwo.

Bayan kuma wancan ƙaiƙayi ko kowar wake (kwanson wake) da ake bar musu, ana kuma biyan su ladan aikinsu. Mata zalla suke gudanar da wannan sana’a ta sussuka.

Sussukar Turmi

Kayan Aiki

  1. Turmi da Taɓarya: Su ne muhimman kayan aikin sussuka, ana zuba dukkan abin da ake son casawa a cikin turmi sai kuma a riƙa bugunsa da taɓarya har sai an cire asalin ƙwayar daga jikin abin da ba a so.
  2. Babbar tabarma: Akan zuba abin da ake casawa a kai. Sannan kuma wasu lokutan akan yi sussukar a kan tabarmar ta hanyar bugu.
  3. Masaki: Ana zuba sussukakken abu a ciki.
  4. Ƙwarya: Kamar masaki take, sai dai girmanta bai kai na masaki ba. Da ita ake yin shiƙa (shiƙa ita ce cire ƙaiƙayi ko kwanso daga cikin asalin ƙwayar abin da aka sussuka ta hanyar ɗaga abin sama ana juyewa a cikin ƙwaryar da ke ƙasa, idan iska ta ratsa tsakani sai ta kore ƙaiƙayin ya fice daga cikin ƙwayar).
  5. Faifai: Ana tankaɗe sauran abin da bai sheƙu ba domin a cire abubuwan da ba a so kamar tsakuwa wacce ita bata sheƙuwa.
  6. Sanda: Dogon ita ce ne mai kauri da kuma ƙarfi. Da shi ake bugu idan ba a turmi za a yi casar ba.

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub