Burumawa
Burumawa, ƙabila ce wacce ta fi yawa a ƙaramar hukumar Kanam, yawanta ya kai kashi tamanin (80%) cikin ɗari na yawan jama’ar ƙaramar hukumar ta Kanam, a cikin Jahar Plateau ta Tarayyar Najeriya. Haka nan ma kuma ana samun su a ƙaramar hukumar Wase, wanda a can kuma yawansu ya kai kashi arba’in (40%) cikin ɗari na yawan jama’ar ƙaramar hukumar ta Wase.
Sannan kuma ana samun su a cikin yankin tsakiyar Najeria (Middle Belt). Har-wa-yau dai ana samun cu a jahar Taraba, a garin Wukari da kuma wasu garuruwan. Hakanan kuma, akan same su a garuruwan Lantang, Shendem, Ƙua’an-Pan, da sauransu a cikin jahar ta Plateau.
Asalin sunan wannan ƙabila shi ne Bogghom, ana ambatonta da furuci mabambanta bisa bambancin ƙabilu. Furucin Hausawa; Burum, shi ne wanda ya fi karɓuwa, ya danne saura. Saboda haka sai ƙabilar ta fi shahara da suna Burumawa.