Masarautar Burum

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Masarautar Burum


Gabatarwa

An kafa Masarautar Burum (Bogghom), a watan Maris na shekarar 2002, biyowa bayan fafutikar kafuwarta da Burumawa; ƙabilar Bogghom suka yi a tsawon shekaru 20 (1982 – 2002), a yunƙurinsu na ƙwatarwa kansu da zuriyarsu ‘yanci daga yunƙurin murƙushe ikonsu da kuma tarihinsu da sarkin Kanam, Alhaji Muhammadu Ibrahim ya yi, a lokacin bikin rantsar da shi, a cikin shekarar 1982.

Gwamnan jahar Plateau, Joshua Chibi Dariye, shi ne ya ƙirƙiri wannan masarauta tare da ƙarin wasu masarautu guda goma da aka sanar a gidan radiyon jahar Plateau, a ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2002, a ƙoƙarinsa na cika alƙawuran da ya ɗauka shi da jama’iyyarsa ta PDP a lokacin yaƙin neman zaɓe da aka gudanar a shekarar 1999.

Duk da wannan sabon cigaba da Burmawa suka samu wanda suka kalle shi kamar haƙarsu ta cimma ruwa, ashe tsugunne bata ƙare musu ba, saboda bita-da-ƙulli da kuma maƙarƙashiyar da suka biyo bayan wancan samun ‘yancin masarauta har sai da ta kai ga an dakatar da wannan masarauta, abinda ya zamar musu ta leƙo-ta-koma.

Daga ƙarshe, bayan kai-ruwa-rana da aka ɗauki ƙarin wasu shekaru goma sha biyar ana yi, wannan masarauta ta tabbata a shekarar 2017, inda gwamnan jahar ta Plateau, Solomon Baƙo Lalong, ya sake maido da wannan masarauta tare da naɗin Alhaji Shehu Suleiman a matsayin sarkinta mai daraja ta biyu, a ranar 9 ga watan Maris na 2017. Wannan jinkiri, shi ya ƙara tsawaita shekarun fafutikar neman kafuwar wannan masarauta daga shekaru 20 (1982 – 2002) lokacin da ka ƙirƙire ta, zuwa shekaru 35 (1982 – 2017), lokacin da ta zauna da gindinta.

Manazarta:


Shehu A.Y. (2018). Out of Mountain A Dynasty Is Born. Yaliam Press Limited (Babu adireshi).



Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub