Ƙofar Gabas
Babu wata takamaimiyar magana dangane da wane lokaci aka gina wannan ƙofa ta Daura. Amma ofisihin waikilin tarihi na Masarautar Daura ya tabbatar da cewa ta wannan Ƙofa Bayajidda ya shiga garin na Daura. Saboda haka suna kyautata zaton tun zamanin sarauniya Daurama aka gina wannan ƙofa.
Manazarta:
Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Daura. Majalisar Sarkin Daura. An buga a: Ammani Printing Press.
Tattaunawa da Wakilin Tarihin na Daura da kuma Dogarin Sarkin Daura mai suna Ɗandaushe, a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2016.