Umar Faruk Umar
Shafin Farko

Mai Martaba Umar Faruk Umar


Gabatarwa

“Sarki Umar Faruƙ Umar shi ne sarkin Daura na sittin. Ya gaji yayansa sarkin Daura Muhammad Bashar a shekarar 2007. An haife shi a garin Daura a ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 1936. Ya yi karatu a makarantar Elimatare ta Zango amma ya ida a Ɓaure saboda komawar mahaifinsa Alhaji Umaru Abdurrahman a matsayin Hakimin Ɓaure.


Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruq Umar

Bayan kammala karatunsa na Elimatare sai ya ci gaba da zama tare da mahaifinsa Bunturawan Daura, Hakimi Ɓaure. Amma a 1952 aka canza wa Bunturawa Alhaji Umaru masarauta, inda ya dawo Daura a matsayin Magajin garin Daura (Hakimin Birni da Kewaye). Wannan sarauta ta Magajin Gari ita ce ya riƙe har zuwa rasuwarsa a 1977.

Alhaji Faruƙ Umar, ƙane ne ga marigayi mai martaba Sarkin Daura Dr. Muhammadu Bashar. Alhaji Umar an saka shi cikin harkar mulki tun gama Elimantare amma bayan dawowar su Daura ya kama aiki tare da ‘NA’ a matsayinsa na mai duba koyar da karatun manya a Ɓaure, daga bisani aka maido shi ƙasar Zango.

Zamanin Alhaji Umar Faruƙ a Zango ya ƙara masa kwarjini da soyayya daga matasa, ganin mutunci da girmamawa daga dattawan garin saboda iya tafiyarsa da jama’a. Ba a kai ko’ina ba sai ya sami ɗaukaka da amsuwa a ko-ina a cikin ƙasar Daura saboda ganin gashi ɗan sarauta amma a ko-yaushe yana tare da jama’a iri daban-daban.

Ya sami zama wakili na majalisar jihar Kaduna 1979-1983. Ya zama shugaban majalisar Katsina 1988-1990, an naɗa shi Hakimi na farko a ƙasar Babban Mutum ranar 5 ga watan Mayu na 1992 da sarautar Buram. A ranar 9 ga Junairun 2006 ya samu sauyi zuwa Hakimin Ɓaure da wannan sarauta ta Ɗan Buran.

Allah cikin ikonsa bayan Alhaji Umar Faruƙ Umar ya zauna a Ɓaure shekara ɗaya da wata biyu sai wansa wanda yake matuƙar biyayya a gare shi sarkin Daura Muhammadu Bashar ya rasu.

Alhaji Umar Faruƙ Umar shi Allah ya baiwa gadon kujerar yayansa a ranar Alhamis 1 ga watan Maris na 2007. Ya zama sarkin Daura na sittin (60) daga Bayajida”. Abubakar (2007).

Manazarta:


Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Masarautar Daura. Wallafar Masarautar Daura. An buga a Ammani Prints, Kano-Nigeria.
Babban Shafin Tarihi
Masarautr Daura

Sarakunan Daura


Ƙofofin Daura


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub