Me ka ke nema?


Shafin Farko

Janaral Muhammadu Buhari, GCFR



Alhaji Muhammadu Buhari

Gabatarwa

Manjo Janar Muhammadu Buhari, sojan Najeriya mai ritaya, sannan kuma ɗan siyasa. Jajirtaccen mutum wanda ‘yan Najeriya suke yiwa laƙabi da “Mai Gaskiya”. Wannan kalma ta ‘yan Najeriya ta tabbata a kansa saboda kasantuwarsa maras hannu a cikin badaƙalolin maƙudan kuɗaɗen da mafiya yawa daga tsoffi da sabbin shugabannin Najeriya suka tsunduma kawukansu a ciki.

Janaral Muhammadu Buhari mutum ne da ke da gogayya a fannin mulki saboda aikin da ya yi a gidan soja, wanda ya fara tun daga sakan laftanar har sai da ya zamo shugaban ƙasa bayan tarin muƙaman da ya riƙe kafin hakan, sannan kuma bayan ritayar sa ya shiga siyasa wacce ta sake bashi damar sake ɗarewa kujerar shugabancin Najeriya a karo na biyu kuma a matsayin farar hula.

Ya samu kafa tarihin cewa shi ne farkon Ɗan’najeriya da ya taɓa tsayawa takarar zaɓe a jama’iyyar hamayya sannan kuma ya kayar da shugaban da ke kan karagar mulki.

Haihuwarsa

Janaral Muhammadu Buhari, haifaffen garin Daura ne ta cikin Jahar Katsina. An haife shi a ranar 17 ga watan Disamba na shekarar 1942. Sunan mahaifinsa Adamu, mahaifiyarsa kuma Zulaihatu. Mahaifinsa ya rasu a lokacin da Janar Muhammadu Buhari ya ke da shekara huɗu kacal a duniya.

Karatunsa

Manjo Janaral Muhammadu Buhari ya yi karatunsa na firamare a garin Daura da kuma Mai’adua daga shekarar 1948 zuwa 1952. Daga nan sai ya shige makarantar Middle ta Katsina a shekarar 1953. Sannan kuma sai ‘Katsina Provincial School’ wacce daga baya ta koma Kwalejin Gwamnati ta Katsina, daga shekarar 1956 har zuwa 1961.

A shekarar 1961, Manjo Janaral Muhammadu Buhari ya samu shiga makarantar sojojin Najeriya da ke Kaduna (Nigerian Military Training School, Kaduna), inda ya gama a shekarar 1963.

Bayan kammala wancan horo da ya samu na soja a Kaduna, a cikin wannan shekara ta 1963 aka tura shi ƙaro karatu a ƙasar Ingila inda ya samu horo a makarantar ‘Cadet School’ da ke garin Aldershot ta ƙasar Ingila. Da Kammalawarsa kuma nan take aka ƙaddamar da shi a matsayin sakan laftanar (second lieutenant) na soja. Aka kuma tura shi zuwa Abekuta.

A dai wannan shekarar ta 1963 aka sake tura shi samun ƙarin horo a fanni ‘Platoon Commanders Course’ wanda ya halarta a  makarantar sojojin Najeriya ta Kaduna (Nigerian Military College, Kaduna), makarantar da ya fara da ita. Ya samu wannan horo har zuwa 1964.

A shekarar 1965, Manjo Janaral Muhammadu Buhari ya sake tafiya samun horo a fannin ‘Mechanical Transport Officers Course’, wanda ya yi a makarantar ‘Army Mechanical Transport School’ da ke garin Borden, na ƙasar Ingila.

Sannan kuma  a shekarar 1973 ya sake samun horo makarantar ‘Defence Services’ Staff College’, da ke garin Wellington na ƙasar Indiya. A shekarar 1979 zuwa 1980 kuma ya je kwalejin yaƙi ta sojoji (United States Army War College) da ke ƙasar Amurka.

Muƙaman da ya Riƙe


Janar Muhammadu Buhari

Manjo Janaral Muhammadu Buhari, ya riƙe muƙamai da dama tun fitowarsa ta farko daga makarantar soja da aka fara ƙaddamar da shi a matsayin sakan laftanar (second lieutenant). Manya daga cikin muƙaman da ya riƙe sun haɗa da:

  1. Gwamnan Jahar Arewa-maso-Yamman Najeriya (Governor North-Eastern Nigeria), a shekarar 1975, a zamanin mulkin shugaban Najeriya Janaral Murtala.
  2. Kwamishinan man fetur na tarayyar Najeriya (Federal Commissioner for Petroleum Resources) muƙamin da ya ke daidai da na minister a yanzu, daga shekarar 1976 zuwa 1978. Ya riƙe wannan muƙami a zamanin mulkin soja na shugaba Janaral Olushegun Obasanjo.
  3. Ciyaman na Kamfanin Manfetur na Najeriya (Chairman, NNPC) a shekarar 1978.
  4. Shugaban rundunar sojojin Najeriya ta uku da ke Jos (General Officer Commanding (GOC), Third Armored Division of Jos) a shekarar 1983.
  5. Shugaban ƙasa. Manjo Janara Muhammadu Buhari ya zama shugaban mulkin soja na tarayyar Najeriya a shekarar 1984 har zuwa 1985 bayan an hamɓarar da gwamnatin farar hula ta shugaba Shehu Usman Shagari.
  6. Shugaban hukumar tara rarar manfetur (Chairman of Petroleum Trust Fund (PTF), daga 1995 zuwa 99 muƙamin da ya riƙe lokacin yana farar hula a zamanin mulkin shugaban soja na Najeriya marigayi Janaral Muhammadu sani Abacha.

Shigarsa Siyasa

A shekarar 2003, Janaral Muhammadu Buhari ya shiga siyasa ƙarƙashin tutar jama’iyyar ANPP, jama'iyyar da ta bashi takarar shugaban ƙasa wanda ya shiga zaɓe tare da shugaba Janaral Olushegun Obasanjo mai ritaya.

Takarkarun da ya yi

Janaral Muhammadu Buhari ya tsaya takarar neman ɗarewa kujerar shugabancin Najeriya a karo na biyu a matsayin farar hula har sau huɗu, sai a karo na huɗu ne aka dace. Ga yadda lissafin ya ke:

  1. A shekarar 2003, shugaba Muhammadu Buhari ya yi takara a ƙarƙashin tutar ANPP.
  2. Shekarar 2007, ya sake wata takarar a dai jama’iyyar ANPP.
  3. Shekarar 2011, ya sake yin takara wannan karon kuma a sabuwar jamaiyyarsa ta CPC mai alamar alƙami.
  4. Sai kuma 2015, ya sake yin wata takarar wacce ita ta kai shi ga ɗarewa kujerar shugabancin Najeriya a karo na biyu a ƙarƙashin tutar jama’iyyar gamayya ko haɗaka ta APC.

Shugaban Farar Hula


Alhaji Muhammadu Buhari Karɓar Mulki, 2015

An sake rantsar da Janaral Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Najeriya karo na biyu, a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015, muƙamin da yake kansa har zuwa yau ɗin nan.

Manazarta:


Naija.com (2016). President Muhammadu Buhari. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://www.naij.com/tag/muhammadu_buhari.html

Nigerian Biography (2016). Biography Of Muhammadu Buhari: President Of The Federal Republic Of Nigeria. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.nigerianbiography.com/2015/05/ muhammadu-buhari-president-politician.html

Oladeinde O. (2015). Muhammadu Buhari: A profile.An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.news24.com.ng/Elections/Voting101 /Muhammadu-Buhari-A-profile-20150126

Sean (2015). Who Is General Muhammadu Buhari ? Biography/Profile/Curriculum Vitae Unɓeiled. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://dailymail.com.ng/who-is-general-muhammadu-buhari/

T.I.N. Magazine (2015). President Muhammadu Buhari Full Biography,Life And News. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.takemetonaija.com/2015/02/general-muhammadu-buhari-full.html

Wikipedia (2016). Muhammadu Buhari. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Muhammadu_Buhari


Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Alamomi da Tambari

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub