Me ka ke nema?


Shafin Farko

Lambobin Yabo da Girmamawa


Gabatarwa

Kowace ƙasa, tana da tsari, salo da kuma hanyoyin da take bi wajen bayar da lambobin yabo da kyaututtukan girmamawa ga ‘yan ƙasarta domin ƙara musu ƙaimi da ƙwarin guiwar tare kuma da zaburantar da ‘yan baya domin kowa ya ƙara ƙwazo wajen gudanar da ayyukansa da nufin kai ƙasar tudun mun tsira.

Nijeriya tana da lambobin yabo da kyaututtukan girmamawa da ta tanada domin bai wa ‘yan ƙasa daga mabambantan fagagen ƙwarewa na rayuwa, waɗanda aka kasa su zuwa rukunai huɗu kamar haka:

  1. Lambobin Girmamawa Na Ƙasa (National Hounours);
  2. Lambobin Yabo na Ƙasa (Nigerian National Merit Award);
  3. Lambobin Girmamawa na Ƙasa ga Masu Ƙwazo (National Productiɓity Merit Award); da kuma
  4. Kyautar Yabo ga Masu Ƙirƙira ta Ƙasa (National Creativity Award).

Lambobin Girmamawa

Dokar Majalisar Tarayya mai Lamba 5 ta shekarar 1964, (National Honour Act No. 5 of 1964) a zamanin Jamhuriyar Siyasar Tarayyar Najeriya ta farko ƙarƙashin shugaba Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa, KBE, ita ta samar da wannan doka domin girmama ‘yan Nijeriya da suka hidimtawa ƙasa da nufin hakan ya zama abin koyi ga ‘yan baya.

Dokar ta halastawa shugaban gwamnati (A lokacin) daga baya kuma shugaban ƙasa damar samar da guraben bayar da lambobi , ƙayatarwa tare kuma da girmama zaƙuƙuran mutane.

Ana bayar da wannan lamba bisa tantancewar gwamnatocin jahohi da mutanen da su karɓi dokar suka fito. Dokar ta tanadi rukunai biyu na lambobin yabo; Order of the Federal Republic da kuma Order of the Niger duka a darajoji huɗu kowace.  Ga su za a jero su daga daraja ta farko zuwa ta ƙarshe:

  1. Grand Commander of the Order of the Federal Republic (GCFR). Ita ce lamba mafi girma a Najeriya, ana bai wa shugabanin ƙasa ita.
  2. Grand Commander of the Order of the Niger (GCON). Ita ce ta biyu a daraja, ana bai wa mataimakan shugaban ƙasa.
  3. Commander of the Order of the Federal Republic (CFR).
  4. Commander of the Order of the Niger (CON).
  5. Officer of the Order of the Federal Republic (OFR).
  6. Officer of the Order of the Niger (OON).
  7. Member of the Order of the Federal Republic (MFR).
  8. Member of the Order of the Niger (MON). Ita ce mafi ƙarancin daraja a cikin wannan jerin.

Sai kuma wasu lambobin tagulla guda biyu da aka ƙara daga baya:

  1. Federal Republic Medal.
  2. Order of the Niger Medal.

Duk da cewa, Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa ne ya samar da wannan tsari na bayar da lambobin yabo da girmamawa, Allah cikin ikonsa bai nufe shi da bai wa kowa ba aka hamɓarar da gwamnatin tasa. Saboda haka sai da shugaban ƙasa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari (GFCR) ya zo sannan ya fara bayarwa a ranar 23 ga watan Satumba na shekarar 1981 ya bai wa Dakta Nmadi Azikwe da kuma shugaban ƙasa Obasanjo saboda a lokacin su ne kaɗai shugabannin ƙasa rayayyu wanda suke zaune a Nijeriya kasantuwar shi kuma har ya zuwa wannan lokacin shugaban ƙasa Janar Gowon yana gudun hijira a Ingila.

Waɗannan lambobi da aka zayyana a sama guda takwas, yan ƙasa kawai ake bai wasu.

Lambobin Yabo na Ƙasa (Nigerian National Merit Award)

Lamar yabo ce ta ƙasa da shugana ƙasa Janar Obasanjo ya samar domin bai wa ‘yan ƙasa da suka yi fice a fannin ayyukan tunani da suka shafi fagage kamar rubuce-rubuce da sauransu. Dokar Soja mai lamba 53 ta shekarar 1979 ita ta samar da wannan damar (Act no 53 of 1979).

Ana bai wa mutanen da suka yi fice a fannonin da suka shafi zurfafa tunanin, ƙwazo a fannin ilimi, bayar da gudunmawa a fannin ci gaban ƙasa a fannin fasaha, kimiyya, kiwon lafiya, taimakon jama’a, al’adu da ma kowane fanni ne Kwamatin Amintattu Na Bayar da Kyautar suka sahale wa.

Manufar bayar da wannan lamabar yabo it ace ƙarfafar guiwar manazarta wajen ƙara himmar zaƙulo mafita ga matsalolin da suke addabar ‘yan ƙasa.

Kwamatin Amintattu (Board of Trustees) da shuagabn ƙasa ya naɗa su suke kula da bayar da wannan kyauta. Ana bayar da wannan kyauta ga waɗanda suke bayar da gudunmawa a fannin zurfafa tunani da kuma ilimi.

Sharruɗan Bayar da Kyauta

Akwai wasu sharruɗa da aka gidanya waɗanda sai mutum ya cika su kafin ya samu karɓar wannan kyauta ta hanyar tantancewa. Abubuwan da za a lura da su su ne:

  1. Kyautar buɗaɗɗiya ce ga duk wani ɗan Najeriya. Wato kenan kowane ɗan Najeriya da yake jin cewa ya kamata ya karɓi wannan lamba zai iya nema.
  2. Ana zaɓar waɗanda za a bai wa kyautar ta hanyar la’akari da abin da zamani yake tafiya da shi.
  3. Ana lura da samar da ƙirƙire-ƙirƙiren fasaha da za su zama masu amfani ga ‘yan Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.
  4. Aikin da aka yi ya zama ya ɗaukaka darajar Nijeriya a idon duniya ta fuskacin al’adu da kuma tattala kyakkyawan sunan Najeriya.
  5. Nasarar da aka samu ta zama ta kere sa’a a fannin da aka samar da ita ko kuma ta zama ta keɓanta da wasu siffofi da sa’aninta basu da su.

Matakan Zaɓi

Bayan cika sharruɗan da aka zayyana a sama, akwai kuma matakai da kwamatin zai bi wajen zaɓar waɗanda za su ci gajiyar wannan kyauta:

  1. Ita dai kyautar ana iya bayar da ita ga ɗaiɗaikun mutane ko kuma masu ɗaukar nauyin su kamar a ce kamfanoni.
  2. Dole a maƙala takardar bayanin aiki (CV) na duk wanda aka ya ci gajiyar wannan kyauta tare da kiyaye cewa an fito da sashen da mai karɓar kyautar ya yi fice a fili da kuma cikakken bayanin dalilin zaɓar tasa.
  3. Duk wanda za a zaɓa, to a maƙala dukkan wasu takardu da suke da alaƙa da samun nasarar zaɓar tasa domin su taimaka wajen tantancewa.
  4. Ana ayyana ranar rufe karɓar takardun neman shiga wannan tsarin tantancewa.
  5. Kwamatin tantancewa bas a shiga kowace irin inkiya ga wanda za a tantance.

Mutunen farko da suka fara karɓar wannan kyauta shi ne Farfesa Chinuwa Achebe, wanda yake bajimin marubuci ne; Farfesa Taslim Olawale Elias, Babban Ministan Shari’a kuma Babban Alƙalin Alƙalan Tarayya na farko; Farfesa Thomas Adeoye Lambo, Ɗan Nijeriya na farko da ya fara riƙe muƙamin mataimakin Darakta Janar na Ƙungiyar Lafiya ta Duniya (WHO); da kuma Dakta Abubakar Imam, fitaccen masanin larurorin mata (Gynecologist) sannan kuma tsohon jami’in kula da lafiya na Kano.

Lambobin Girmamawa na Ƙasa ga Masu Ƙwazo (National Productivity Merit Award)

Yunƙurin samar da hanyar haɓɓaka ƙirƙira a fannin tattalin arziƙin ƙasa shi ya saka aka samar da wanan kyauta. Babbar manufarta ita ce ƙarfafar ɗabi’ar ƙirƙira a harkar aiki.

A ɗaiɗaikun mutane ana so kyautar ta ƙarfafi ƙwarewa a wajen aiwatar da ayyuka, sadaukarwa, jajircewa, ƙirƙira, gaskiya, tabbaci, kamun-kai, kyakkyawan jagoranci, mayar da kai, kula da lokaci, aiki tare da juna, bayar da gudunmawa wajen gina al’umma da ƙungiyoyi da kuma kyakkyawar cuɗanya da jama’a.

A matakin ƙungiyoyi kuma da kamfanoni, ta ƙuduri aniyar karrama kamfanoni masu dogaro da kansu wajen aiki da fasaha domin su tabbatarwa da kansu rage kashe kuɗaɗen gudanar da ayyuka.

An ƙirƙiri wannan kyauta a shekarar 1991. An sahalewa ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyin da suka cancanta wajen saka lambar NPMA a gaban sunaye.

Kyautar Yabo ga Masu Ƙirƙira ta Ƙasa (National Creativity Award).

A ranar 23 ga watan Janairun 1995, Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Janar Sani Abacha ta ayyana ranr 14 ga watan Satumba a matsayin ranar Ƙirƙira ta Ƙasa (National Day of Creatiɓity).

Manufar ayyana wannan rana ita ce ankarar da jama’a tare kuma da zaburantar da su game da gudunmawar da ƙirƙire-ƙirƙire ke bayarwa a fannin ciyar da ƙasa gaba. Ƙari a kan haka kuma an nufi ranar ta zama ranar baje kolin hazaƙa da basirar ‘yan ƙasa a fannin kimiyya, Fasaha da kuma Al’adu.

Daga baya, a cikin shekarar 1999, shugaban ƙasar farar hula a Jamhuriyar Siyasar Nijeriya ta huɗu, Janar (Murabus) Obasanjo ya yi dokar bayar da kyautar girmamawa ga masu hazaƙa a fannin al’adu kodai ta fuskacin rubutu ko kuma wasan kwaikwaya domin a zaburantar da masu tasowa su ƙara zage damtse a wannan fage domin ganin sun kai ga wani matsayi a fannin.

Bayan kafa Kwamtin da zai kula da wannan bayar da kyauta da shugaba Obasanjo ya yi, daga ƙarshe suka fitar da suna Farfesa Chinuwa Achebe a matsayin zakaran gwajin dafin karɓar wannan kyauta saboda littafinsa mai suna Things Fall Apart.

An bashi wannan kyauta a ranar 14 ga watan Satumba na shekarar 1999 wadda kuma ƙumshi ce ta Naira Miliyan Ɗaya (1,000,000). Gwamnati tana nufin cusa al’adar ɗaukar nauyi a zukatan kamfanoni da wannan kyauta da ta bayar wadda aka kallafa wa kwamatin amintattun nauyin gudanar da ita.

Mazarta:


Ajaegbu H.I., ST. Matthew-Daniel B.J., and Uya O.E. (2000). Nigeria A people United, A Feature Assured Volume 1, A Compendium, Millenium Edition. Gabumo Publishing Company Limited, Nigeria.


Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Alamomi da Tambari

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub