Me ka ke nema?


Shafin Farko

Majalisar 'Yansandan Nijeriya


Gabatarwa

Majalisar ‘Yansandan Najeriya, wadda ake kira Nigerian Police Council a Turance, majalisa ce da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya kafa ta domin ta riƙa kula da wasu muhimman aikace-aikacen Rundunar ‘Yansandan Najeriya ciki kuma har da bai wa shugaban ƙasa shawara kan wanda ya dace a naɗa a muƙamin babban sufeton Rundunar ‘Yansandan Najeriya.

Kafa Majalisar ‘Yansandan Najeriya

Babi na VI, sashe na 153, ƙaramin sashe na (1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999, shi ya bayyana cewa a kafa wannan majalisa ta ‘yansanda.

Wakilan Majalisa

Ƙuduri na 27 na rataye na uku na sashe na ɗaya na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekarar 1999, ya zayyana cewa, masu riƙe da waɗannan muƙamai da za a zayyano a ƙasa su ne za su zama wakilan wannan majalisa ta ‘Yansanda Najeriya. Ga su kamar haka:

  1. Shugaban ƙasa, wanda shi ne zai zama shugaban majalisar.
  2. Dukkanin Gwamnonin jahahohin Tarayyar Najeriya.
  3. Shugaban Hukumar ‘Yansanda.
  4. Babban sufeton ‘yansanda.

Ayyukan Majalisar ‘Yansanda

Kudin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekarar 1999, ƙuduri na 28 na sashe na ɗaya rataye na uku ya bayyana ayyukan Majalisar ‘Yansanda da cewa:

  1. Fasalta Rundunar ‘Yansandan Najeriya; gudanar da ita; da dukkan wasu al’amuran da suka shafeta in banda al’amarin horo, naɗa muƙamai, ladabtarwa, da kuma korar ‘ya’yan rundunar, duk yana wuyan wannan majalisa ta ‘yansanda.
  2. Kula ko duba manyan aikace-aikacen rundunar.
  3. Shawartar shugaban ƙasa game da wanda za a naɗa a matsayin babban sufeton ‘Yansandan Najeriya.

Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Alamomi da Tambari

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub