Professor Abdallah Uba Adamu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Farfesa Abdalla Uba Adamu



Farfesa Abdallah Uba Adamu
Hoto: An ciro daga shafin Jami'ar Noun mai adireshi https://noun.edu.ng



Gabatarwa

Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019).

Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nuif, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.

Allah ya yi masa baiwa da fasahar magana, gogewa, jajircewa da kuma himma a fannonin da ya yi fice a kai, wato karantarwa, rubuce-rubuce da kuma gabatar da jawabai. Mutum ne shi mai son bai wa jama’a gudunmawa a fannin ilimi tare kuma da ƙarfafar guiwar na ƙasa da shi domin su taso. Gudunmawar da ya bayar wajen kawo sauyi a fagen yadda ake rubuta littattafan Hausa, abu ne mai wahalar taskacewa.

Abdallah Uba Adamu, cikakken Bahaushen Kano ne da ke Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.

Haihuwa

An hafi Farfesa Abdallah Uba Adamu a ranar 25 ga watan Afirilun shekarar 1956, a Unguwar Daneji da ke cikin ƙwaryar birnin Kano. Ɗa ne shi ga fitaccen marubucin tarihin Kano, wato Dakta Uba Adamu; marubucin littafin tarihin Kano mai suna Kano Ƙwaryar Ƙirar Matattarar Alherai, mujalladi na ɗaya zuwa na huɗu.

Karatu

  1. 1979: Digirin Farko a Fannin Ilimi, Kimiyyar Halittu da kuma Fishiyoloji (Education/Biology/Physiology), daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
  2. 1982: Difilomar Mai Zurfi (Postgraduate Diploma) a Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education), daga Kwalejin Chelsea ta Jami’ar London.
  3. 1983: Digiri na biyu a fannin Ilimin Kimiyya (Science Education), daga Kwalejin Chelsea ta Jami’ar London.
  4. 1988: Digirin Digirgir daga Jami’ar Sussex da ke Falmer, Brighton, England.
  5. 1997: Farfesa a Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education), Jami’ar Bayero, Kano.
  6. 2004: Farfesa a Fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Culture Communication), Jami’ar Bayero ta Kano.

Gogayyar Aiki

Fitaccen masani ne shi a harkar ilimi, rubuce-rubuce da kuma karantarwa; ayyukan da ya ɗauki shekaru arba’in cif (1979 – 2019) yana yi.

Tun fitarsa daga jami’a a shekarar 1979 ya fara karantarwa a matakin bautar ƙasa a Makarantar ‘Yanmata ta Ekwerazu (Ekwerazu Girls Secondary School, Umoarkrika, Imo) a Jahar Imo a Najeriya, inda ya karantar har zuwa 1980.

Ya shiga karantarwa a Jami’ar Bayero a shekarar 1981, aikin da yake ciki har zuwa yau ɗin nan a matsayinsa na Mataimakin Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami’ar Najeriya (NOUN).

Maluntar Ƙasa-da-Ƙasa

Bayan zamowar Farfesa Abdallah Uba Adamu malami a Jami’ar Bayero ta Kano, to kuma ya zama Maziyarcin Malami (Visiting Lecturer) a wasu jami’o’in ciki da wajen Najeriya. Kaɗan daga cikin su sun haɗa da:

  1. 1992: Jami’ar California da ke Berkely ta ƙasar Amurka.
  2. 2004: Jami’ar Köln da ke ƙasar Germany.
  3. 2006: Jami’ar London, da ke London.
  4. 2007: Kwalejin Barnard ta Jami’ar Columbia da ke New York, a ƙasar Amurka.
  5. 2009: Jami’ar Basel da ke ƙasar Switzerland.
  6. 2010: Jami’ar Florida da ke ƙasar Amurka.
  7. 2012: Jami’ar Warsaw da ke ƙasa Poland.
  8. 2015: Jami’ar Jahar Rutgers (Rutgers State University) da ke New Jersey ta ƙasar Amurka.

Mataimakin Shugaban Jami’a

Farfesa Abdallah Uba Adamu ya zama mataimakin Buɗaɗɗiyar Jami’ar Ƙasa ta Najeriya wato Vice Chancellor a Turance, a shekarar 2016. Muƙamin da yake kai har lokacin yin wannan rubutun (2019).

Shafukan Sadarwa

Ga wasu shafu da za ka ziyarta domin cin karo da ɗimbin ayyukan alheri a fannin rubutu da Farfesa ya rubuta kuma yake yaɗa su a duniya domin amfanin mabuƙata:

Manazarta:


National Open University (2019). Professor Abdalla Uba Adamu. An ciro daga shafin: http://nou.edu.ng/officers/professor-abdalla-uba-adamu-0 a shekarar 2019

Wikipedia (2019). Abdalla Uba Adamu. An ciro daga shafin: https://en. wikipedia.org/wiki/Abdalla_Uba_Adamu a shekarar 2019

Adamu A. U (Babu shekarar wallafa). Abdalla Uba Adamu Full CV. An ciro daga shafin: https://auadamu.com/index.php/biography/6-au-adamu-ngr-full-cv-nov-2015-3 a shekarar 2019

Bayero University Kano (2019). Abdalla U Adamu _ Bayero University, Kano- Academia.edu. An ciro daga shafin: https://buk.academia.edu/AbdallaAdamu a shekarar 2019.

Shafin Tarihi


Mashahuran Mutane



Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub