Sheikh Nasir Muhammad Kabara

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sheikh Nasir Muhammad Kabara



Sheikh Nasir Muhammad Kabara

Gabatarwa

A dukkan zamani akan samu wasu mutane waɗanda Allah Maɗaukakin Sarki ke yiwa baiwa da abin da ya so. Wasu ya basu kuɗi, wasu sarauta wasu ilimi, wasu kuma wata fasahar daban, wasu kuma ya yi musu tagomashi da abubuwa da dama. Shehin Malami Nasir Muhammad Al-Mukhtar Kabara, Mashahurin malami ne wanda Allah ya yi wa baiwa da tarin ilimin da duniya ta san da shi. Haƙiƙa sunansa ya kewaya duniya a fagen ilimi.

Haihuwarsa

An haifi Shehin Malami Nasir Muhammad Al-Mukhtar Kabara a shekarar  1912, a garin Guringawa da ke Kano, a Najeriya.

Salsalarsa

Zuriyar Shehin Malami Nasir Muhammad Al-Mukhtar Kabara ta fito ne daga garin Kabara na Timbuktu wanda ke a Ƙasar Mali ta yau. Kakansa na uku Mallam Umar (Omar) shi ne ya taso daga garin Kabara ta Timbuktun Ƙasar Mali. Malam Umar ya fara zama a Unguwar Adakawa da ke Ƙaramar Hukumar Dala ta Jahar Kano kafin ya ƙaura zuwa Unguwar Kabara da ke cikin birnin Kano a yau; unguwar da sunanta ya samo asali daga inkiyar malamin.

A cikin shekarar 1787 da Mallam Umar ya shiga unguwar Kabara ta Kano, ya mayar da zauren gidansa makaranta wacce a yau ɗin nan ta zama katafariyar cibiyar Ɗariƙar Ƙadiriyya ta Afirka baki ɗaya; gidan da a yau aka fi saninsa da Darul-Ƙadiriyyah. Wannan cibiya tana daga cikin daɗaɗɗun makarantun soro na Kano.

Karatunsa

Haƙiƙa, Sheikh, Nasir Muhammad ya kasance mutum mai matuƙar son karatu wanda haka ta saka ya zamo ɗalibi mai ƙwazo. Ya fara karatunsa tun yana ɗanƙarami da karatun Alƙur’ani mai girma kamar yadda aka saba. Bayan kammala karatunsa na Allo sai kuma ya shiga fagen karatun littattafai a fannonin addini da dama inda ya fara da karanta littafin Bad’ul Amli da Murshid; waɗanda sanannun littattafai ne wajen karantar da Tauhidi.

Bayan kammala waɗannan littattafai sai kuma ya ɗora da na fiƙihu inda ya fara da littafin Ahlari, Iziyya da kuma Risala kamar yadda aka saba a Mazahabin Malikiyya.

Karsashinsa, ƙwazo da hazaƙa suka sa ya samu karɓuwa a wajen babban malaminsa wato Mallam Natsugunne, inda ya bashi dukkan tallafin da ya dace. Wannan kuma ita ta saka ya yi wa sa’anunsa rata nesa ba kusa ba, wanda hakan har ta sanya ya ke yi musu ƙarin bayani kan fassarar Alƙur’ani.

Matashi Nasir Muhammad Kabara ya kasance mai ƙishirwar ilimi wanda hakan ta saka shi jonewa da manya-manyan makarantun birnin Kano dan kamfato ɗimbin ilimin da Allah ya jibge a waɗannan makarantu da suke ja-gaba a cikin shekarun 1920. A wannan lokaci akwai manyan makarantu guda biyar da suke kamar makarantun share fagen shiga jami’a na yanzu a fannin ilimi. Waɗannan makarantu sun zamo suna da ƙosassun ɗakunan karatu da Matashi Nasir Muhammadu Kabara ke zuwa yana nazari a cikinsu. Waɗannan makarantu su ne:

  1. Gidan mataimakin limamin masallacin birni wanda ya ke da zama a unguwar Daneji.
  2. Gidan Mallam Ibrahim babban Alƙalin Kano wanda ke unguwar Yakasai.
  3. Gidan Alhaji Musɗafa Kurawa Alƙalin Kotun Bichi wanda ya ke a unguwar Kurawa.
  4. Gidan Mallam Abdulkarim wanda aka fi sani da Mallam Sambo da ke unguwar Ciromawa.
  5. Gidan Mallam Inuwa babban limamin zawiyya da ke unguwar Mayanka.

Salon karatunsa ya bambanta da na sauran abokan karatunsa inda ya kasance mai neman ƙarin bayani a duk wani abunda bai gane ba. Yakan yi amfani da siga ta girmamawa da kwantar da kai gaba ga malamansa a yayin karatu da kuma neman ƙarin haske wanda hakan ta sa, a nasu ɓangaren su malaman suka zamo suna maraba da shi a duk lokacin da yake da buƙata.  

Shigarsa Ɗariƙar Ƙadiriyya

Allah mai kowa mai komai, kuma Mai yadda Ya so a kuma lokacin da Ya so, kuma ta yadda Ya so. Cikin nufinSa da yardarSa Ya so Sheikh Nasir Muhammad Kabara ya zamo sanadin yaɗuwa da ɗaukakar Ɗarikar Ƙadiriyya a Afirka.

A shekarar 1937, an yi tururuwar shiga ɗariƙar Ƙadiriyya a cikin birnin Kano. Daga cikin dubunnan mutanen da suka samu karɓar Ɗarikar Ƙadiriyya a wannan shekara akwai Sheikh Nasir Muhammad Kabara. Duk da cewa kakansa Mallam Natsugunne ya so a ce jikansa Nasir Muhammad ya samu zamowa mamba na Ɗariƙar Ƙadiriyya a wannan shekarar amma saboda ƙarancin shekarunsa; wanda a wannan lokaci yana da shekaru 17 a duniya, sai Shehin Malami Mallam Sa’ad ya damƙa masa wazifa, duk kuwa da zuzzurfan ilimi da shi Nasir Muhammad yake da shi a fannin sufanci.

A cikin wata shekara da Mai Martaba Sarkin Kano Abdullahi Bayero zai tafi aikin Hajji, sai Sheik Muhammadu Nasiru ya rubuta wasiƙa ta hannun Wali Sulaiman zuwa ga Halifan Ƙadiriyya na wancan lokacin Shehi Abu al-Hassan as-Samman wanda yake jika ne ga wanda ya kafa Ɗariƙar Ƙadiriyya Sammaniyya, yana mai roƙon sa da ya yi masa izinin zamowa muƙaddamin zawiyarsa.

Mamaki ya yi matuƙar kama Shehi Abu al-Hassan da ganin irin wannan baƙon abu daga wannan Sheikh. Saboda haka nan-take ya aiko masa da kyautar riga jubba da hula da kuma rubutacciyar takardar naɗa shi muƙamin muƙaddamin na Ɗariƙar Ƙadiriyya Sammaniyya.

A shekarar 1949 Shehi Muhammad Nasir Kabara ya samu zuwa aikin hajji da kansa inda ya samu ganawa da Halifa Shehi Hashim da Shehi Muhammad duk daga Murtaniya.

A kan hanyarsa ta dawowa gida, ya biya ta ƙasar Sudan inda ya samu ganawa da Sayyady Shehi Muhammad al-Fatih ɗan Shehi Ƙaribullah, babban Shehin Sammaniyya ta Sudan inda a nan ma ya sake karɓar izinin zama Muaƙaddimin Sammaniyya-Ƙaribiyya a karo na biyu.

Tun kafin sannan, Shehi Muhammadu Nasir Kabara ya karɓi ijazar sa ta asali a Ɗariƙar Ƙadiriyya Kuntiyya da kuma Ahl al-Dar daga hannun babban malami Mallam Ibrahim Natsugunne, wanda ya yi zamaninsa daga 1867 zuwa 1941.

Shehi Muhammad Nasir Kabara ya samu ganawa da tushen gidajen Ƙadiriyya da ke a garuruwan Khartoum ta ƙasar Sudan, Timbuktu ta ƙasar Mali, da kuma asalin tushen Ƙadiriyya da ke a Bagadada ta ƙasar Iraƙi tsakankanin shekarar 1935 zuwa 1955.  Ziyararsa zuwa Bagadada a shekarar 1953 ita ce tubalin zamowarsa kankat a harkar ɗariƙar Ƙadiriyya wanda wannan ce ta bashi dama ta kafa masallacinsa na Ƙadiriyya.

Dukkan gidajen Ƙadiriyya na ciki da wajen Kano da ma faɗin Najeriya sun zama a ƙarƙashinsa tun daga shekarar 1958 har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

Gudunmawarsa

Shehi Muhammadu Nasiru Kabara ya bada gagarumar gudunmawa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci da Ɗariƙar Ƙadiriyya. Kasancewarsa mutum mai ƙwazo wajen neman ilimi haka kuma ya zamo wajen yaɗa shi. Shehi Muhammadu Nasir Kabara ya bada gagarumar gudunmawar da baki ba zai iya faɗa ba, haka kuma alƙalamin marubuci ba zai iya taskace ta ba. Shi ne mutumin da ya fara gabatar da mauludin wanda ya kafa Ƙadiriyya (Maulana Sheikh Abdulƙadir Jilani) a Kano a shekarar 1959. Shi ne mutumin da ya yaɗa zikirin bandiri a saƙo-saƙo da lardunan Najeriya.

Shehi Muhammad Nasir Kabara ya kasance ya zagaya dukkan yankunan Najeriya yana mai buɗe masallatan Ƙadiriyya da kuma naɗa muƙaddiman Ɗariƙar Ƙadiriyya waɗanda Allah shi kaɗai ya san adadinsu.

Muƙaman da ya Taka

  1. Ya zamo muƙaddamin Ɗariƙar Ƙadiriyya al-Sammaniyya a tsakankanin shekarar 1937 zuwa sama da ita.
  2. Ya sake zama Muƙaddamin Ɗariƙar Ƙadiriyya al-Sammaniyyal-Ƙaribiyya a shekarar 1949.
  3. Ya zamo mamba na majalisar mashawartan Mai Martaba Sakin Kano Abdullahi Bayero a shekarar 1949.
  4. Ya zamo ƙwararren mai bada shawara a harkar shari'a ga kotun Musulunci ta Arewacin Najeriya a shekarar 1954.
  5. Ya zamo ɗaya daga cikin mutane biyu da suke gabatar da tafsiri a fadar masarautar Kano tun daga 1954 har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
  6. Ya zamo shugaban makarantar shari'a da labirare ta Shahuci a shekarar 1958.
  7. Ya kafa babbar makarntar firamare ta Islamiyya a shekarar 1961 a Gwale.
  8. Ya sake zamowa Mashawarcin Mai Martaba Sakin Kano Alhaji (Dr) Ado Bayero a shekarar 1963.
  9. Ya zamo mamba na Majalisar Malamai ta Kaduna a shekarar 1963.

Rubuce-Rubucensa

Shehi Muhammad Nasir Kabara ya bada gagarumar gudunmawa a fagen rubutu. Bincike ya tabbatar da cewa ya rubuta littattafan da adadinsu yah aura ɗari uku (300). Daga cikin mashahuran rubuce-rubucensa akwai: Tafsirin Ƙur’ani mai girma.

Rasuwarsa

Wannan rayuwa mai tarin albarka bata ƙare ba saboda shukokin da ya dasa, amma dai ruhinsa mai daraja ya koma ga Allah a ranar 21 ga watan Jumada Auwal na shekarar 1417 wanda ya yi daidai da 4 ga watan Oktoba na shekarar 1996. Allah ya jiƙansa da rahama amin.

Manazarta:


www.darulƙadiriyya.org


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub