Ike Nwachukwu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Janaral Ike Nwachukwu, CFR



Janaral (ritaya) Ike Nwachukwu

Gabatarwa

Nwachukwu, tsohon sojan Najeriya mai muƙamin janaral (ritaya), sannan kuma daga baya ɗan siyasa mai muƙamin tsohon sanata. Shu Inyamuru (Igbo) ne kuma Bahause. Ya baiwa Najeriya gudunmawa iya bakin gwargwadonsa. A yanzu haka yana ɗaya daga cikin dattawan ƙabilar Igbo.

Haihuwarsa

An haife shi a rana 9 ga watan Satumba na shekarar 1940, a garin Fatakwal (Port Harcourt) na jahar Rivers, ta Najeriya. Mahaifinsa marigayi Chief Moses Maduka Nwachukwu, mutumin jahar Abia ne mahafiyarsa kuma Hajiya Binta Mohammed Dikko, ‘yar asalin jahar Katsina ce. Saboda haka ake kiransa da Ike Omar Sanda Nwachukwu. Maganar Igbo sannan kuma Bahaushe ta tabbata kenan.

Karatunsa

Janaral (ritaya) Ike Omar Sanda Nwachukwu ya yi karatunsa na firamare da sikandire a makarantun ‘Ladi-Lak Institute’, da kuma ‘Lagos City College’, duk a garin Yaba, ta jahar Legas.

Daga nan kuma sai  makarantar horas da sojojin Najeriya (Nigerian Military Training College) ta Kaduna, sai kuma ‘Royal Canadian School of Infantry’ da kuma ‘School of Infantry’, ta garin Warminster, a ƙasar Ingila. Sai kuma ‘Institute of Humanitarian Law’, da ke garin San Remo, a ƙasar Italiya, sai kuma Makarantar koyar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (United Nations Peace Academy), sai kuma ‘National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPPS)’, ta garin Kuru, jahar Filato (Plateau State) a Najeria.

Gogayyar Aiki

Janaral (ritaya) Ike Omar Sanda Nwachukwu, ya riƙe muƙamai da daman gaske tun bayan fitowarsa daga makarantar horon soja. Daga cikin irin waɗannan muƙamai, ya riƙe muƙamin ‘General Officer Commanding’, wanda ya kula da runduna ta 1 ta sojojin Najeriya sashen tankoki da sauransu (1st Mechanised Division, Nigerian Army), sannan ya zama ‘Provost Marshal’, na rundunar sojan Najeriya, sannan ya zama kwamanda a makarantar koyar da dabarun yaƙi (Commandant, Nigerian Army School of Infantry) mai kula da makarantar ja ji (Directing Staff, Command and Staff College, Jaji). Ya zama gwamnan soja na Jahar Imo, sannan ya riƙe muƙamin ‘Minister for Employment, Labour and Productivity’ daga shekarar 1986 zuwa 1987, ya riƙe muƙamin ministan harkokin ƙasashen waje (Minister of Foreign Affairs) daga shekarar 1987 zuwa 1989, inda aka canja shi da wani sannan kuma aka sake dawo da shi kan wannan muƙmi na ministan harkokin ƙasashen waje a shekarar 1990 har zuwa 1993.

Barinsa Aikin Soja

Janaral Ike Nwachukwu ya bar aikin soja a shekarar 1990. Ya bar gidan soja yana da muƙamin Janaral.

Shigarsa Siyasa

Janaral (ritaya), kuma sanata Ike Omar Sanda Nwachukwu, ya shiga siyasa a shekarar 1999, inda ya tsaya takarar sanata mai wakiltar Mazaɓar Abiya ta Arewa (Abia North Constituency), takarar da ya samu hayewa a ƙarƙashin tutar jama’iyyar PDP daga 1999 zuwa 2003.

Ya riƙe muƙamai da dama a wannan majalisa ta dattawan Najeriya (Senate), daga ciki akwai: ‘Chairman of the Senate Committee on Power and Steel’, sai kuma ‘member of the Senate Committee on Water Resources’.

A siyasance kuma ya riƙe ‘Chairman National Peace and Reconciliation Committee’ na jama’iyyarsa ta PDP.


Ike Nwachukwu tare da shugaba Buhari

Gudunmawar da ya Bayar

Janaral (ritaya) Ike Omar Sanda Nwachukwu mutum ne mai son ganin ƙasarsa da jama’arta sun ci gaba, saboda haka duk muƙamin da ya riƙe yana bada gudunmawa mai gwaɓi, daga cikin gaggan gudunmawowi da ya bayar waɗanda suke wanzuwa har yanzu su ne: Shi ya gina matsugunnin din-din-din na jami’ar jahar Imo (Imo State University) wacce yanzu ta koma jami’ar jahar Abiya (Abia State University) a lokacin da yake riƙe da muƙamin gwamnan soja na jahar ta Imo. Sannan kuma shi ne ya ƙirƙiri hukumar nan mai samar da ayyukan yi ga matasa (National Directorate of Employment (NDE)) a lokacin da yake riƙe da muƙami ‘Minister for Employment, Labour and Productivity’, da nufin kawar da matsalolin rashin ayyukan yi musamman ga matasa waɗanda ke da karatu a matakin digiri ko kuma daidai da shi.

Lambobin Yabo da Girmamawa

Mutum mai son bada gudunmawa kamar wannan ya samu lambobin yabo da girmamawa a ciki da wajen Najeriya da suka haɗa da: A nan gida Najeriya an bashi: ‘Nigerian Independence Medal’, ‘Forces Serɓice Star’, ‘Defence Serɓice Star’ ‘Nigeria Republic Medal’ ‘National Serɓice Medal’, da kuma ‘Order of Commander Federal Republic of Nigeria (CFR)’. Sai kuma ‘Special Certificate of Merit of the African Youth Congress’, ‘Award of Recognition of the Iron and Steel Senior Staff Association of Nigeria (ISSSAN)’, da kuma ‘Merit Award by Hon. Achike Udenwa, former Goɓernor of Imo State, on the occasion of the state’s Silɓer Jubilee’.

A ƙasashen waje kuma ya samu: ‘Grand Commander of Eƙuatorial Guinea’, ‘Federal Republic of Germany’s Grand Cross of Merit (GMCS)’ da kuma ‘Grand Master of the National Order of the Southern Cross (GMSC), Brazil’. ‘Diplomatic Medal (DMM) South Korea’, ‘Grand Cruz de la Order dei Merito Ciɓil de Espana (GCMC), Spain’,  ‘Knight Grand Cross of the Order of St Michael and St George (GCMG), United Kingdom’, da kuma ‘Commander of the Order of Mono (COM), Togo’.

Manazarta:


Abia State Government (2015). Rtd Major Gen. Ike Nwachukwu. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.abiastate.gov.ng

Anugwara B (2013). Ike Nwachukwu  Gentleman soldier. Newswatch Times. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.mynewswatchtimesng.com/ike-nwachukwu-gentleman-soldier/

Nigeria National Conference (2014). PROFILE  Ike Nwachukwu . An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.premiumtimesng.com/national-conference/profile-ike-nwachukwu/

Ohaneze Ndibe (2016). Ohaneze Ndigbo Elders Meet With Buhari In Abuja. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.ndibe.org/2015/04/ohaneze-ndigbo-elders-meet-with-buhari.html

Wikipedia (2016). Ike Nwachukwu. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Ike_Nwachukwu


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub