Oduduwa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Oduduwa



Gidan Oduduwa a Ile-Ife

Gabatarwa

Kalmar Oduduwa, wacce a ƙa’idar yare ake rubuta ta da Odùduwà, kalma ce da ake kiran wani mutum da ita. Shi wannan mutum da shi ake danganta duk wani Bayarabe. Ya rayu a garin Ile-Ife ko kuma Ife wacce take cikin jahar Osun ɗin Najeriya.

Akwai maganganu da dama dangane da wannan mutum. Wasu sun ce ya zo ne daga ƙasar Egypt, wasu kuma sun ce a’a, daga Makka ya zo, wasu kuma sun ce ai ɗan sarkin Edo ne ma da aka nunawa Bambanci, wasu kuwa cewa suka yi aikakke ne daga sama, an turo shi ya halicci ƙasa da sauran mutane.

Zuwan Oduduwa

Adijola (2006), ya ruwaito cewa, Yarabawa (Yoruba) sun yi imani cewa, Allah ne ya aiko Ododuwa dan ya halicci ƙasa da kuma jinsin mutane, a saboda haka shi da jama’arsa sun sauka ne a garin Ile-Ife a cikin sarƙa. Eke (1992), shi ma ya yarda da wannan ra’ayin amma ya ƙara da cewa, "Oduduwa ya sauka a wannan yanki na Ile-Ife da tantabara, da ɗantsako, da kuma ƙasa a cikin mazubi inda ya zuba wannan ƙasa a ciki ko gefen ruwa, su kuma tantabarar da ɗantsako suka riƙa tona su suna barbazawa har suka samar da wannan ƙasar da muke raye a kanta". Gurstelle (2015), shi ma ya ruwaito wannan tare da ƙarin cewa da Oduduwa ya samu nasarar aiwatar da wannan aiki sai aka bashi mulki.

A labarin kunne ya girmi kaka kuwa, da muke zantawa da wasu dogarawan sarkin Ife, cewa suka yi tabbas Ubangiji mai suna Oludumare shi ya aiko shi duniya dan ya halicci ƙasa da sauran mutane. Sun kuma yarda cewa shi Oduduwa shi ne kakan dukkan wani Bayarbe da ke raye a wannan duniyar. Kuma su kansu Yarabawan sun yarda da wannan.

Haka nan Aderibigbe (2014), ya kawo cewa shi Ododuwa Allah (Oladumare) ne ya aiko shi daga sama kuma ya sauka a garin na Ile-Ife, garin da a zamanin baya, ruwa ne shi ya mai she shi ƙasa.

Wannan mutum mai suna Oduduwa ya kafa fadar mulkinsa da shi da sauran jama’arsa a garin na Ile-Ife wanda daga baya ya bunƙasa ya haifar da wasu masarautun Yarabawa guda goma sha shida ciki kuma har da daɗaɗɗiyar daular Yarabawa ta Oyo.

Oduduwa ya hafi ɗa guda ɗaya tilo mai suna ‘Okanbi’ wanda shi kuma ya haifi wasu ‘ya’yan guda goma sha shida. Su waɗannan ‘ya’ya na Okanbi su ne jikokin Ododuwa na farko waɗanda kuma ta hanyarsu ne dukkan wani jinsi na Bayarabe ya samu.

Oduduwa ya rasu a garin Ile-Ife, wanda gidansa na farko shi ya zama kushewarsa. Har yau ɗin nan wannan gida yana nan a kewaye da katangar jan bulo a garin na Ile-Ife wanda ba shi da nisa daga gidan sarkin Ile-Ife.

Manazarta:


Adijoja T.M. (2006). Historical Notes on Yoruba-Speaking of South Western Nigeria. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: www.macosconsultancy.com/

Aderibigbe A. (2014). The State of Osun. The Cradle of Yoruba Civilization and Cultural Tourism.

Eke C. (1992). Oduduwa, the Ancestor of the Crowned Yoruba Kings. An ciro a shekarar 2006, daga shafin: https://yorubafactfinder.files.wordpress.com

Gurstelle A. W. (2015). The House of Oduduwa: An Archaeological Study of Economy and Kingship in the Savè Hills of West Africa, A dissertation submitted in partial fulfillment of the requirements for the degree of Doctor of Philosophy (Anthropology) in the University of Michigan, 2015.

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub