Bola Ahmed Tinibu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Bola Ahmed Tinibu



(Dr.) Bola Ahmed Tinibu

Gabatarwa

Bola Ahmad Tinibu ɗansiyaya ne, tsohon sanata, sannan kuma tsohon gwamnan Lagas wanda ya yi wa’adin mulki biyu a jere, sannan kuma ɗaya daga cikin iyaye a sabuwar jama’iyyar haɗaka ta APC wacce ta ɗora shugaba Buhari a kan kujerar shugabancin Najeriya.

Shi ne Jagaban, sarautar da tsohuwar daular Borgu wacce ke arewacin jahar Neja ta yi masa. Haka nan kuma shi ne Asiwajun Legas, wanda shi ma muƙami ne na sarauta.

Bola Ahmed Tinibu hamshaƙin mai kuɗi ne kuma ɗan fafutikar rajin kare haƙƙin bil’adama, fafutikar da ta zamar masa gado daga mahaifiyarsa “Ita ta nuna min hanya, a duk lokacin da yanayi ya rincaɓe, takan haskaka min fitilar da ke taimako na na gane hanya, kuma tana ƙarfafa min guiwa, wanda in banda uwa mai son ‘ya’yanta ba me yin wannan” In ji Bola Ahmed Tinibu (2013).

Haihuwarsa

An haifi Bola Ahmad Tinibu a garin Legas a ranar 29 ga watan Maris na shekara 1952. Ana kiransa da Asiwajun Adekunle Ahmed Bola Tinibu Jakadan (Omeh, 2015). Sunan mahaifiyarsa Hajia Abibatu Mogaji.


Bola Ahmed Tinibu da Mahaifiyarsa

Karatunsa

Bola Ahmed Tinibu ya yi karatunsa na firmare da sikandire a makarantar ‘St. John's Primary School’, da ke Aroloya, ta jahar Legas da kuma makarantar sikandire ta ‘Children's Home School’ ta garin Ibadan ɗin jahar Oyo.

A shekarar 1975 ya samu tafiya ƙasar Amurka dan yin karatunsa na gaba da sikandire. Ya fara yin karatunsa a makarantar ‘Richard J. Daley College’ da ke garin Chicago, na jahar Illinois, kafin daga baya ya koma ‘Chicago State University’. Ya kammala wannan karatu nasa a shekarar 1979 inda ya fita da digirinsa na farko a fannin tsimi (Bachelor of Science degree in Accounting).

Gogayyar Aiki

Bola Ahmed Tinubu ya yi aiki da wasu kamfanoni a ƙasar Amurka da suka haɗa da: Arthur Andersen, Deloitte, Haskins, & Sells, sannan sai kuma kamfanin GTE Services Corporation. A shekarar 1983 ya dawo gida Najeriya. Bayan dawowarsa gida najeriya ya yi aiki da kamfanin manfetur na Mobil Oil Nigeria.

Shigarasa Siyasa

Bola Ahmed Tinibu ya tsunduma harkokin siyasa a shekarar 1992 inda ya tsaya takarar sanatan Legas ta yamma kuma aka zaɓe shi a shekarar 1993. Bayan rushe zaɓensu da aka yi, Bola Ahmed Tinibu yana daga cikin mutanen da suke kan gaba wajen kafa ƙungiyar nan mai rajin ganin an gudanar da mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya (National Democratic Coalition (NADECO)), tare da ganin cewa an mutunta zaɓen da aka gudanar na ranar 12 ga watan Yuni (June, 12).

Wannan fafutika tasa, ta saka shi gudun hijira ya bar gida Najeriya tun daga shekarar 1994 har zuwa 1998, inda ya dawo gida bayan rasuwar marigayi shugaba Muhammadu Abacha.

Zamowarsa Gwamna

Bola Ahmed Tinibu ya sake tsayawa zaɓe a shekarar 1999 inda aka zaɓe shi a matsayin gwamnan Legas a ƙarƙashin tutar jamai’iyyar AD (Alliance for Democracy), kujerar da tun da ya ɗare ta a shekarar 1999 bai sauka ba sai a shekarar 2007 bayan cikar wa’adin mulkinsa na biyu inda ya damƙa kujerar a hannun magajinsa.  

Lambobin Yabo da Girmamawa

Bola Ahmed Tinibu ya karɓi lambobin yabo da girmamawa da dama daga ciki da wajen Najriya. Akwai A shekarar 2000, ya karɓi kyauta ‘Best Governor in Nigeria for Y2000’ kyautar da Nigerian-Belgian Chamber of Commerce ta bashi, haka nan ya karɓi kyautar ‘Y2002 Best Practices Prize in improving the living environment’, kyautar da Federal Ministry of Works tare da haɗin guiwar UN Habitat Group suka bashi, sannan ya karɓi kyautar ‘Y2000 Best Computerized Government in Nigeria Award’, kayutar da ƙungiyar masu kwamfuta ta Najeriya (Computer Association of Nigeria) ta bashi.

Haka nan kuma ya karɓi kyautar digirin digirgir na girmamawa (digiri na uku) a fannin doka (Doctor of Civil Laws, (DCL)) wanda jami’ar Njala University da ke ƙasar Sierra Leone ta bashi a ranar 15 ga watan Faburairun shekarar 2014.

Sannan a shekarar 2015 ya karɓi ‘Silverbird Extraordinary Man Of The Year Award’, a ɗakin taro na ‘Eko Hotel convention hall’, da ke Legas  a daren Lahdi 24 ga watan Afirilu na shekarar 2015.

Manazarta:


Naija.com (2015). Tinubu bags Silverbird Eɗtraordinary Man Of The Year Award. An ciro a shekarar 2016 daga shafin: https://www.naij.com/809587-tinubu-wins-silverbird-extraordinary-man-year-award-2015-photos.html

Premium Times (2013). My Mother, Her Life, Her Legacy, By Bola Ahmed Tinubu. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: file:///D:/Rumbu%20All/Biography/Tinubu/My%20Mother,%20

Pmnews (2014). Sierra Leone university to honour Tinubu. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.pmnewsnigeria.com/2014/02/13/sierra-leone-university-to-honour-tinubu/

T.I.N Magazine (2015). Asiwaju Bola Tinubu Full Biography, Life, And Career. An ciro  shekarar 2016, daga shafin: http://www.takemetonaija.com/2015/11/asiwaju-bola tinubu-f -life.html#sthash.sd1ɗohAɗ.dpuf.

Wikipedia (2016). Bola Ahmad Tinibu. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Bola_Tinubu


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub