Masarautar Pindiga

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Masarautar Pindiga


Gabatarwa

Pindiga, ita ce helikwatar mulkin masarautar Pindiga, wacce kuma ɗaya ce daga cikin masarautun Jahar Gombe. Wannan gari mai daɗaɗɗen tarihi, Jukunawa suka kafa shi a tsakankanin ƙarni na goma sha shida zuwa ƙarni na goma sha bakwai. Garin ya fara daga ɗanƙaramin matsugunni na wasu jama’a a kan dutse har zuwa bunƙasarsa kamar yadda yake a yau a matsayin masarautar sarkin yanka mai daraja ta biyu a cikin jahar Gombe.

Asali

Pindiga, gari ne mai tsohon tarihi, asalin kafuwar wannan gari yana farawa daga lokacin da Jukunawa suka shigo yankunan baƙaƙe daga ƙasar Yamen, a cikin ƙarni na goma sha shida zuwa ƙarni na goma sha bakwai.

Fitowar wannan jama daga Yamen, sun shigo ta ƙasar Sudan ta yau, inda suka yada zango a garin Kartum. Daga nan suka rankayo ta gefen kogin Cadi, kama-kama har suka zo Dutsin Bima. Daga wannan Dutsi na Bima ne suka rabu gida biyu; kashi ɗaya daga ciki suka kama hanyarsu tiryan-tiryan har zuwa Dutsen Binga, inda suka kafa wani gari wanda a yau ake kiransa da sunan Yalwa.

A cikin shekarar 1815 A.D., sarkin Gombe Buba Yero, ya fara kai harin yaƙi a wannan gari na Binga. Dukkan yaƙuƙuwan da wannan sarki ya yi da Jukunawan Binga, bai samu nasarar murƙushe su ba har ya bar duniya. Haka nan aka ci gaba da wannan yaƙi kama-kama har zuwa zamanin sarkin Gombe Umarun Kwairanga, wanda ya haɗa rudunar haɗaka da ta tattara mayaƙa daga ƙasashen Bauchi, Misau, Jama’are da kuma wasu garuruwan. Wannan runduna su suka yaƙi Jukunawan da ke wannan gari mai suna Binga; yaƙi irin na ƙare-dangi. Ba su bar kowa ba sai waɗanda suka gudu suka sha da ƙyar.

Ragowar waɗannan mutane da suka famtsama uwa-duniya, su ne suka sake dawowa daga baya suka sake kafa wani garin a kan wani dutse wanda shi kuma suka kira shi da suna ‘Kartum’. Sun zaɓi su kira shi da wannan suna dan ya riƙa tuna musu da zaman da suka taɓa yi a garin ‘Khartoum’ wanda ke cikin ƙasar Sudan ta yau.


Dutsen Kartum

Bayan wani lokaci suna zaune a kan wannan dutse mai suna Kartum, sai suka ga cewa ya kamata su ƙara gaba, saboda haka sai suka gusa gaba kaɗan, tazarar da bata haura kilomita ɗaya da rabi ba, suka sake kafa wani sabon garin a kan Dutsen Puli, wanda yanzu ake kiransa da suna Dutsen Jukun. Shi wannan dutse yana nan a bayan garin Pindiga.


Dutsen Jukun

Bayan Turawa sun ci Gombe da yaƙi, a shekarar 1903, sai suka sauko da waɗannan mutane daga kan wannan dutse zuwa matsugunnin da a yanzu suke zaune a ciki; wato garin Pindiga kenan.


Wani Sashen Garin Pindiga daga kan Dutsen Jukun

Masarautar Pindiga

Tun daga farko, a lokacin da helikwatar mulkin wannan yanki na Pindiga ke zaune matsugunninta na farko; garin Binga, ikonta ya malala har zuwa garin Gwana daga kudu, ta arewa kuma har zuwa garuruwan Kwami da Gadam. Sai kuma ta ɓangaren yamma inda ta dangana da garuruwan Fali da Kirfi. Da ta miƙe gabas kuma ɗoɗar, sai da ta kai garin Gwani, sannan ta karkata zuwa gabas-maso-yamma inda ta kai har zuwa garuruwan Tangale da Wurkum. Alaƙar da ke tsakanin Jukunawan Binga da waɗannan garuruwa da aka lissafa, alaƙa ce ta addini. Ana kuma iya tantance haka daga ɗan sauran tasirin abin da ya rage na al’adu da addini daga Bolewa, Terawa, Waja, Wurkum da kuma Tangalu.

Wannan tasiri na wannan gari na Jukunawa wato Binga, ya fara disashewa a cikin shekarar 1830 zuwa 1840 inda ta koma ƙarƙashin mulkin masarautar Gombe ƙarƙashin tutar Musulunci. An ce, wannan ta faru ne sakamakon karɓo tuta da ɗaya daga cikin ‘ya’yan sarautar gidan ya yi mai suna Hassan daga Gombe. Bayan ya karɓi tutar, sai ya koma gida da nufin yaƙar ɗan’uwansa mai suna Giwa wanda a lokacin shi ke sarautar ƙasar, sai shi Giwa ya ce ba zai yi yaƙi da ɗan’uwansa ba. Saboda haka sai ya ƙara gaba ya kafa garin Tudun Ƙwaya wacce a yanzu ta ke cikin ƙaramar hukumar Ɓilliri-Kaltungo ta Jahar Gombe. Wannan kuma ya biyo bayan karɓar Musulunci da shi Hassan ya yi, shi kuma sarki Giwa a ta nasa ɓangaren ya ƙi karɓar addinin na Musulunci.

A farkon ƙarni na ashirin kuma; wato a shekarar 1903, lokacin da Turawa suka ci ƙasar Gombe da yaƙi, wannan ƙasa ta Pindiga ta koma ƙarƙashin mulkin hakimin Akko a matsayin garin Digaci. Tun daga wannan lokaci, Pindiga ta ke zama a matsayin garin digaci har zuwa shekarar 1978, inda ta samu ci gaban da ya kai ta kujerar hakimi a zamanin sarki Alhaji Ahmadu Shu’aibu.

A cikin shekarar 2000, zamanin Alhaji Abubakar Habu Hashidu, wanda shi ne gwamnan farar hula na farko a jahar Gombe, Allah ya albarkaci wannan gari na Pindiga da komawa masarauta ƙarƙashin sarkin yanka mai daraja ta biyu, wanda Alhaji Mohammad Seyoji Ahmad ya zamar mata sarkin farko.

Kenan a taƙaice, garin Pindiga, gari ne da Jukunawa suka kafa shi a ƙarni na goma sha shida zuwa ƙarni na goma sha bakwai. Wannan gari ya fara ne daga matsugunninsa na farko mai suna Binga wanda yanzu ake kiransa da Yelwa, sannan bayan yaƙi ya fatattaka garin aka sake kafa wani a kan Dutsen Kartum, sai kuma aka sake matsawa gaba aka sake kafa wani da aka kira shi da Puli, wanda yanzu kuma ake kiransa da Dutsen Jukunawa, sannan aka gangaro ƙasa aka kafa wannan gari na Pindiga wanda ya zama helikwatar mulkin masarautar Pindiga, wacce aka samar da ita a zamanin mulkin gwamnan farar hula na farko Alhaji Abubakar Habu Hashidu a shekarar 2000, wacce kuma sarkin yanka mai daraja ta biyu, Alhaji Muhammad Sayoji Ahmad ya zamar mata sarkin yanka na farko kuma har yanzu yake a kan kujerar sarauta.

Manazarta:


Northen Nigerian Publishing Company. (1970). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company, Zariya – Najeriya.

Okunna, E da Gausa, S. (2014). Adapting the Jukun Traditional Symbols for Textile Design and Production. Mgbakoigba: Journal of African Studies. Vol. 3. July, 2014

Tattaunawa da Mai Martaba Sarkin Pindiga, Alhaji Muhammad Sayoji Ahmad a ranar 13/02/2017 a Pindiga, Fadar Masarautar Pindiga.

Tattaunawa da Galadiman Pindiga, Alhaji Gambo Garba, a Gidansa da ke Gombe, a ranar 13/02/2017.



Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub