Barka da Zuwa Cibiyar Bayar da Magunguna ta Pharm Sadi M. Haruna SITM    ...Dukkan Cuta Tana da Magani...


Pharm Sadi M. Haruna, SITM, ƙwararren masani ne a fannin harhaɗa magunguna da kuma bayar da su a kimiyyance. Ya ɗauki shekaru yana aiki tare da 'Yan China domin samun ƙwarewa tare kuma da karantar wannan fanni na bayar da maganin asali kuma a kimiyyance

Wannan cibiya ta Pharm Sadi M. Haruna, SITM, reshe ce ta fitaccen kamafanin harhaɗa magunguna ta hanyar tsirrai na duniya, wato TASLY. Sunan wannan kamfani kuma ba ɓoyayye ba ne a harkar lafiya a duniya.

A wannan cibiya tamu muna bayar da magungunan da ke zuwa daga manya-manyan ƙasashen waje da suka haɗa da China, India, Malasia, Amurka, Canada da sauransu, domin bayar da kariya da kuma samar da waraka daga manya-manyan cututtuka a zamanance ta hanyar ƙwarewa tare da gwaje-gwaje ta hanyar amfani da na'urorin zamani.

Ƙari a kan haka kuma, muna gyaran jiki ko kula da jiki ta hanyar magunguna. Kenan, jiki zai zauna sumul kuma cikin ƙoshin lafiya ta hanyar shan maganin da aka samar daga ciyayi da sauran cimaka.

A tuntuɓe mu ta: 0808 829 0265 (+234808 829 0265) ko 0708 411 5553 (+234708 411 5553)

Muna Aiki a Ƙungiyance Kuma a Zamanance


Tawagar Wasu daga cikin ma'aikatanmu

Muna iya zuwa har gida domin kula da ku


Na'urar Gwaje-Gwaje da aune-aunen domin gano larura

Wasu daga cikin Magungunanmu


                                                                       

Muna da Kayayyakin Tausa na Zamani


                                       

Tuntuɓa:Tasly Health Care Centre
#178 / 492 BUK Road by Qofar Famfo, Kano


+234806 907 7102