Sarki Musulmi Abdurrahman

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarki Musulmi Abdurrahman


Gabatarwa

Abdurrahman ɗa ne ga Sarkin Musulmi Abubakar Atiƙu, shi kuma ɗan Shehu Usmanu Mujaddadi. Shi ne Sarkin Musulmi na 11.

Ya zamo Sarkin Musulmi bayan an yi masa mubaya’a a gidan waziri Muhammadu Bukhari a garin Ƙauran Namoda ranar Laraba 17 ga watan Sha’aban. Sannan shi ne jikan Shehu na ƙarshe da ya yi sarauta daga ‘ya’yan Sarkin Musulmi Abubakar Atiƙu.

Bayan zamowarsa Sarkin Musulmi, ya yaƙi sarakunan Talatan Mafara da kuma Anka, wannan kuma ya biyo bayan ƙurar da ta taso ta rashin yin mubaya’a da sarkin na Mafara ya yi, maimakon zuwa da kai, sai sarkin na Mafara ya tura Galadimansa. Yayin da shi kuma sarkin Musulmi ya ƙi amsar wannan mubaya’a, ya buƙaci lallai sai shi sarkin ya je da kansa.

Taƙƙadamar ta ƙara tsamari tsakanin Sarkin Musulmi Abdurrahman da sarakunan Mafara da Anka, bayan shi sarkin Mafaran ya karɓe wa sarkin Burmi wani gari mai suna Birnin Tudu. Sai sarkin Burmi ya kai ƙorafi ga Sarkin Musulmi dan a samu sasanto, da Sarkin Musulmi ya tura ɗan saƙon sa zuwa ga sarkin Mafara, ya neme shi da ya miƙa wannan gari ga sarkin Burmi matuƙar dai ya san cewa ba nasa ba ne, in kuma ba haka ba, to ya tura da bayani. Sai sarkin Mafara ya amsa da cewa wannan gari ba mallakin Burmi ba ne.

Da ɗan saƙo ya dawo ga Sarkin Musulmi ya sanar da shi amsar sarkin Mafara, sai Sarkin Musulmi ya sake tura shi da saƙon cewa su sulhunta tsakani, idan kuma sarkin na Mafara bai yarda da wannan hukunci na Sarkin Musulmi ba, to fa ba komai a tsakanin su sai yaƙi.

Da jama’ar Mafara suka samu labarin aiken Sarkin Musulmi zuwa gare su, sai suka tare wannan ɗan saƙo na Sarkin Musulmi a kusa da wani gari da ake kira Rani, suka kashe shi, suna masu ikirarin cewa su, sun zaɓi yaƙi tsakanin su da Sarkin Musulmi.

Da haka ta faru, sai Sarkin Musulmi ya yi umarni da a buga gangar yaƙi, a sanar da jama’a cewa sarakunan Mafara da Anka sun zama abokan yaƙi. Sannan kuma ya aike wa sarkin Zamfara Umaru ɗan Muhammadu yana mai umartar sa da ya tsare sashen gabas, sannan kuma ya tura wata ƙaramar runduna tana yaƙi safiya da maraice.

Sannan kuma ya umarci sarkin Rafi Alhaji da cewa ya tafi zuwa wani gari da ake kira Magami ya datse Muradun. Sannan ya tura barade zuwa ga sarkin Burmi dan su zauna tare da shi a wani gari da ake kira Maɗushi, dan su tsare wannan yankin. Sannan ya umarci sarkin Salsalbi wanda ya ke a Shauni, da ya yaƙe su safiya da maraice. Haka nan ma Magajin Gari an tura shi zuwa Maru, dan ya tara barade su tafi zuwa Mafara. Sannan kuma ya umarci sarkin Mafaran Gumi, ya tsare ƙasar Zoma. Ya kuma umarci sarkin Danku Ali, shi kuma ya tafi zuwa Laji, duk su haɗu su yaƙi mutanen Mafara. Sannan ya umarci mutanen Gabas da su datse hanyar da mutanen Mafara suke bi suna zuwa kasuwa. Kada wani ya yi hulɗa da wanin su, har sai sun koma zuwa garinsu.

Da sarkin Mafara ya ga haka nan, sai ya nemi taimakon mayaƙa daga sarkin Gobir. Shi kuma sarkin Gobir ya haɗa runduna mai ƙarfi ya tafi zuwa gare shi. Sai sarkin Burmi ya aike wa sarkin Musulmi cewa, idan Ibo (sarkin Gobir) ya zo Damri, to fa basu da natsuwa. Saboda haka sai Sarkin Musulmi ya umarci mutanen Muradun da cewa su kai ɗauki Damri. Sannan sai Sarkin Musulmi ya kira Abo, suka je suka same shi a Wurno.

Shi kuwa sarkin Gobir sai ya tashi runduna mai ƙarfi zuwa Tureta, suka tafi suka yaƙe ta, suka rushe garin. Suka koma gida. Shi sarkin Gobir ya zauna a Mafara, shi kuma sarkin Mafara ya tafi Ɗankade tare da rundunarsa, suka fafata yaƙi da shi da mutanen Burmi. Aka kashe Bawa ɗan sarkin Mafara. Sannan sai Sarkin Musulmi ya tura barade suka tare Wababi. Shi kuma ya yi shiri da kansa ya tafi ya yaƙi garuruwan Mafara da suka haɗa da Ruwan Bure. Da ya dawo, sai mutanen Zamfara suka tafi zuwa Gamji, ya umarci Marafa Muhammadu Maiturare Laji da su tafi zuwa Damru da Sabon Gari, su yaƙe ta. Da suka dawo gida, jama’ar Mafara suka ƙuntata, sai suka nemi sulhu, Sarkin Musulmi ya ƙi yarda.

Daga nan sai Hajj ya sake rushe garin Muradun, abubuwa suka sake rincaɓewa, mutanen Mafara, suka sake neman sulhu, Sarkin Musulmi ya ƙi yarda. Sai a karo na uku suka taru suka tafi gurin sarkin Burmi, suka roƙe shi cewa ya nema musu sulhu a wajen Sarkin Musulmi.

Da abin ya isa ga Sarkin Musulmi, sai ya ce da su idan har da gaske suke yi, to su turo masa sabon sarkin da suka zaɓa bayan sun cire tsohon. Gabanin tafiyar su sai Alhaji da Ali Danka, suka ruguje garuruwan Zoma. Haka nan ma kuma sarkin Zamfaran Anka Hassan, shima ya nemi sulhu, Sarkin Musulmi ya ce ba zai yi sulhu da shi da sarkin Mafara ba har sai sun je gare shi. Daga nan sai sarkin Mafara ya tafi zuwa ga sarkin Burmi suka haɗu suka tafi zuwa ga Sarkin Musulmi, suka taras da shi a Gwandu.

Sai Sarkin Musulmi ya umarce su da sakin duk wani fursunan yaƙi da suka kama, nan take suka aikata. Sannan ya nemi su bashi bayi dubu, suka aikata. Sannan ya ce dukkan garin da ya ci da yaƙi nasa ne, suka amince. Sannan ya ce a mayar wa da sarkin Burmi Birnin Tudu, suka aikata. Sannan aka baiwa sarkin Muradun Sabon Garin Ranbori da kuma Damri. Garuruwan Zoma kuma aka rarraba su ga sarkin Mafara Alhaji da kuma sarkin Danka Ali. Aka baiwa Alhaji garuruwa biyar, haka nan shi ma Ali aka bashi garuruwa biyar. Sannan aka umarce su da dawo da dukkan wanda ya gudu zuwa gare su na daga bayi, suka amince da haka. Sannan aka umarci sarkin Mafara da jama’arsa da su daina aiwatar da al’adar su ta zuba ƙasa a jikinsu kamar yadda aka sani.

Daga ƙarshe dai aka sanar da dukkan sarakunan da ke sashen gabas cewa an yi sulhu da sarakunan Mafara, cewa daga wannan lokaci ba za a yaƙe su ba. Haka kuwa suka zauna cikin aminci har ƙarshen rayuwar Sarkin Musulmi Abdurrahaman.

Bayan ƙare wannan yaƙi kuma, Sarkin Musulmi Abdurrahman ya yi yaƙuƙuwa tsakaninsa da sarakunan Argungun da kuma na Ranbori har sau uku-uku.

Bayan ƙare waɗannan yaƙuƙuwa kuma, sai wani yaron Auzinawa (Azbin) mai suna Adau, ya kawo masa hadaya tare da rakiyar ɗan sarkin Zazzau kamar yadda aka saba suna yi duk shekara a zamanin Sarkin Musulmi na goma Umaru ɗan Ali.

Haka nan a zamanin Sarkin Musulmi Abdurrahman aka samu matsala a Masarautar Kano. Wannan rikici da ya gudana tsakanin Sarkin Kano Muhammadu Tukur da Yusufa, ya wakana a gaban Wazirin Sakkwato Muhammadu Buhari ɗan Ahmadu lokacin da ya yada zango a Kano, a kan hanyarsa ta zuwa Barno, a zamanin Sarkin Kano Muahammadu Ballo. Bayan Waziri ya kwana guda, sai ya yi nufin yin bankwana da sarki, sai ya samu sarki a cikin halin jinyar da abu ne mawuyaci ya warke. Saboda haka sai ya zauna tare da aike wa Sarkin Musulmi saƙo.

Da sarkin Kano ya rasu, sai Waziri ya aika labari zuwa ga Sarkin Musulmi. Da saƙo ya je ga Sarkin Musulmi, sai ya turo 'yan aike da saƙon ta'aziyya ga jama'ar Kano sannan kuma da umarnin naɗin Muhammadu Tukur a matsayin sabon sarkin Kano.

Abin da ya biyo bayan wannan naɗi daga ɓangaren 'ya'yan sarki da Yusufu ya jagoranta, suka fice daga gari, zuwa Takai. Da Waziri ya samu labari, ya yi iya iyawar sa ya kwantar da rigimar amma su 'yan tawaye suka ce bal! Basu yarda ba. Haka suka haɗa ƙarfi ta hanyar raba goron gayyata ga wasu garuruwan da suka haɗa da Dutse, Haɗejia, da Ningi. Suka zo suka yaƙi Kano, ba tare da nasara ba. Daga ƙarshe har sai da ta kai Sarkin Musulmi ya bayar da umarni ga sarakunan Katsina da Zazzau kan su samar da mafita kan wannan rigima, abu ya gagara. Kwanci-tashi har shi Yusufu ya rasu sannan kuma Aliyu Babba ya ɗora daga gun da ya tsaya bisa wasicinsa.

Daga ƙarshe dai bayan dukkan yunƙure-yunƙure, wannan runduna ta 'yan tawaye da Babba ke jagoranta suka hilaci Sarki Tukur suka kashe shi a garin Tafashiya cikin ƙasar Katsina. Bayan wannan kisa sai shi Aliyu Babba da aka fi sani da Alu Mai Sango ya zama sarkin Kano.

Bayan faruwar wannan, sai babba ya tura ɗan saƙon sa zuwa Sakkwato. Da wannan ɗan saƙo ya isa Sakkwato, sai ya isa ga Waziri, Waziri kuma ya yi masa iso zuwa ga Sarkim Musulmi. Shi kuma ya karɓe shi hannu biyu-biyu. Sannan Sarkin Musulmi ya aike shi da saƙon afuwa da kuma tabbatar da Babba a matsayin sabon sarkin Kano.

Bayan haka, sai Sarkin Musulmi ya umarci Waziri da zuwa Kano dan tabbatar da sarautar Alu tare kuma da yi musu afuwa. Bayan isar Waziri Kano, ya labarta wa Babba abin da ke tafe da shi. Jin wannan labari ya yi matuƙar farantawa Babba rai. Bayan tabbatar da shi sai Waziri ya rubuta wa dukkan sarakunan gabas yana mai sanar da su tabbatar da Babba a matsayin sabon Sarkin Kano tare kuma da yi masa afuwa kan dukkan abubuwan da suka faru.

Su kuwa Auzinawa ta nasu ɓangaren, an samu daidaito tsakanin su da Sarkin Musulmi, inda ya ci gaba da karɓar kyaututtukan su har zuwa lokacin da Waziri ya je Zazzau ya samu labarin cewa sun ƙwace Nupe. Da labari ya je kunne Sarkin Musulmi sai ya daina karɓar kyautar su. Su kuma suka ci gaba da cin garuruwa ɗaya-bayan-ɗaya har sai da suka kai Bauchi, sarkin ya gudu zuwa Kano.

Da suka samu labarin zuwan Waziri ƙasar Zazzau, sai suka tafo gare ta. Haka aka zuba rundunoni biyu-biyu a kowace ƙofa, sai ƙofa ɗaya rak da Waziri ya fice ta cikin ta zuwa Kano. Wannan kuma shi ne abin da ya kawo ƙarshen zaman Zazzau a ƙarƙashin Sarkin Musulmi.

Sarkin Musulmi Abdurrahman ya rasu ranar Juma'a 23 ga Rajab. Ya yi sarauta ta tsawon shekaru goma sha biyu. Ya rayu a duniya tsawon shekaru saba'in da biyar. An yi jana'izar sa bisa sunna aka binne shi a Wurno.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub