Sarki Musulmi Abubakar Atiƙu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarki Musulmi Abubakar Atiƙu


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Abubakar Atiƙu ɗa ne ga Shehu Usmanu Ɗanfodiye. Shi ne ma’abocin sirririkan Shehu. Ya zauna tare da Shehu a garuruwan Gwandu, Sifawa, da kuma Sakkwato.

An yi masa muba’aya a masallacin Juma’a na garin Wurno, cikin watan Sha’aban, kwanaki bakwai bayan rasuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo.

Bayan zamowarsa Sarkin Musulmi, sai wasu daga cikin kafiran Zamfara da Gobir suka warware amanar su, abin da ya saka Sarkin Musulmi Abubakar Atiƙu ya yi shirin yaƙi, ya je ya yaƙe su yaƙi mai tsanani. Daga nan kuma ya sake tura wata runduna zuwa wasu garuruwan Katsina da Shinkafi aka yaƙe su. Sannan kuma dai ya yaƙi ƙasar Zoma, sai kuma yaƙi da ya gwabza da rundunar haɗin guiwar mayaƙan Gobirawa, Katsinawa, Auzinawa (Azbin) da kuma mutanen Barno. Haka ya yi ta fita yaƙuƙuwa yana kuma samun nasara da taimakon Allah.

Ya rasu a garin Katuru ranar Alhamis a kan hanyar sa ta dawo wa gida daga yaƙin Tsibiri. Yaƙin da ya samu raunin da ya zamar masa ajali. Ya rasu a cikin watan Shawwal.

Ya yi sarauta ta tsawon shekaru biyar da watanni uku. Ya bar duniya yana da shekaru sittin.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub