Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu'azu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu'azu


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Hassan, shi ne sarki na goma sha shida a cikin jerin sarakunan Musuluni na Daular Sakkwato.  Shi ɗa ne ga Sarkin Musulmi Mu’azu, shi kuma ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo, shi kuma ɗan Shehu Usmanu Mujaddadi. Mutum ne shi mai sauƙin kai, karimci; mai farin jini a wajen jama’a; mai tausayin naƙasssu, yara da kuma tsofaffi. An yi masa mubaya’a a ranar Alhamis da subahin ranar idin ƙaramar sallah.

Abubuwa da dama na ci gaba sun faru a zamanin sa. A lokacinsa aka kammala gina sakatariyar Hukumar Gargajiya (NA), wanda wannan ta bashi damar zamowa sarki na farko da ya fara gudanar da harkokin mulki a wannan sakatariya. Haka nan ma shi ya mayar da baitil mali zuwa wannn sakatariya. Kuma dai a lokacinsa aka buɗe babban asibitin Sakkwato, makarantar midil; da kuma sabunta ginin ƙofar fada, aka mayar da shi na zamani; a zamanisa ne aka fara ɗaukar matasa aikin ɗansanda a Sakkwato.

A zamanin Sarkin Musulmi Hassan aka fara busa begila bayan sallar Isha da kuma Sallar Asuba a garin Sakkwato, saboda dalilan tsaro. Shi ne sarkin da ya gina a ɓangren Gabas na garin Sakkwato; wanda ake kira Nassarawa. Shi ne ya gina babbar majalisar da ke cikin gidan sarki.

A zamanin Sarkin Musulmi Hassan aka fara zaman majalisar sarakuna a garin Kaduna, da kuma taron shekara-shekara na sarakunan yankunan Sakkwato dan yin shawara a tsakanin su game da abubuwan da ke gudana a faɗin yanki, sannan kuma daga ƙarshe a tura sakamakon zuwa Sakkwato. Sannan a zamanin sa aka fara tura ɗalibai zuwa makarantar koyon shari’a da ke Kano dan ci gaba da karatu. Haka nan kuma a lokacin sarautar sa mata ‘yan duba-gari suka fara shiga gidaje dan duba tsabtar muhalli da tabbatar da lafiyar jama’a.

A irin adalcin Sarkin Musulmi Hassan, ya mayar da sarautar Rimi ga jikokin Sarkin Musulmi Aliyu Babb, bayan ta kuɓuce daga hannunsu na sama da shekaru arba’in. Kuma dai shi ya shigo da jikokin Shehu Mujaddadi; ‘ya’yan Sarkin Musulmi Ahmadu Rufa’i cikin harkokin sarauta.

Sarkin Musulmi Hassan, ya rasu ranar Talata, 1 ga watan Rabbi’ul Akhir, bayan magariba. Ya rayu tsawon shekaru sittin da uku a duniya. An binne shi a Hubbaren Shehu da ke Sakkwato.


Hubbaren Shehu

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub