Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo (1996 - 2006)



Hoto, Newsimg.bbc.co.uk
Sarki Musulmi Muhammadu Macciɗo


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, basarake ne shi kuma ɗan siyasa. Mutun ne mai adalci, tausayi, haƙuri, juriya, sadaukarwa da kuma son zaman lafiya. Ya bayar da gagarumar gudunmawa tun daga rayuwarsa ta aikin gwamnati kamawa har zuwa harkokin sarauta; mutum ne da ya fara aiki da hukumar gargajiya (NA) a matsayin mai bayar da taimako a ofishin kansila (office assistance) Sir Ahmadu Bello Sardauna, ya kuma kai har zuwa matsayin kansila (councilor).

Ciroman Sakkwato, hakimin Talatan Mafara, a ƙarshe kuma Sarkin Musulmi. Shekara goma ya yi a kan kujerar Sarautar Daular Musulunci mai cibiya a Sakkwato kafin rasuwarsa a cikin Shekarar 2006 sakamakon hatsarin jirigin sama a garin Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya.

Haihuwa

An haifi Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo a shekarar 1926 a cikin garin Dange. Sunansa na asali shi ne Muhammadu Bello. Kalmar Maciɗɗo kuma, kalma ce ta Fullanci wacce ke da ma’ana ta Allabura; kamar a ce Allah ya raya, kasantuwar, dukkan ‘ya’yan da shi sarkin Musulmi Abubakar III ya haifa kafin Maciɗɗo duk sun mutu. Wannan kuma yana daga cikin al’adun Hausawa, idan aka samu ɗan da aka haifa bayan rasuwar ‘ya’ya guda biyu kafin sa, to akan yi masa laƙabi da Allabura, ma’ana, Allah ya bar wannan ɗa, da ma’ana ta Allah ya raya.

Shi ɗa ne ga Sarkin Musulmi Abubakar III (1938 – 1988), shi kuma ɗan Shehu, shi kuma ɗan Sarkin Musulmi Mu’azu ɗan Bello (1877 – 1881), shi kuma ɗan sarkin Musulmi Muhammadu Bello (1817 – 1837), shi kuma ɗan Shehu Usman Ɗanfodiyo (1744 – 1817).

Karatu

Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo ya fara da koyar karatun addinin Musulunci a gidansu tun yana ɗan ƙarami. Daga baya kuma ya fara karatun zamani kamar yadda za a zayyana a ƙasa:

  1. Makarantar Elimatare ta Dange 1933. Sai kuma aka kai shi makarantar Elimantare ta Sakkwato da ke unguwar Hakki dan yin karatu na tsawon shekara ɗaya. Daga baya kuma aka sake mayar da shi Makarantar Elimantare ta Dange, inda ya ƙarasa karantunsa na Elimantare a can.
  2.  Makarantar Midil da ke Sakkwato, wacce yanzu ta zama Makarantar Sikandire ta Nagarta (Nagarta Secondary School).
  3. ‘Clerical Training School, da ke Zariya 1947 – 1949. Wannan makaranta ita ce ta rikiɗe ta koma Tsangayar Jami’ar Ahmadu ta Zariya da ke unguwar Kwango.
  4. 1952, ya samu zuwa ƙasar Ingila inda ya samu difiloma a fannin gudanar da mulki (Diploma in Public Administration).

Abokan karatunsa lokacin da ya ke makarantar Midil akwai Malam Aminu Kano, Alhaji Bello Sakkwato, Abdullahi Tsoho Dogondaji, da sauransu.

Haka nan lokacin da ya ke karatu a Ingila, ya yi karatu tare da mutanen da suka haɗa da, Muhammadu Bashar wanda ya zama sarkin Daura daga baya, Muhammadu Bahago, wanda ya zama sarkin Minna, Bello, wanda ya zama sarkin Paiko ta jahar Neja, Magajin garin Musawa, Alhaji Sule Minjibir wanda ya zama Marafan Kano, da sauran su.

Gogayyar Aiki

  1. Ya yi aiki da hukumar gargajiya (NA), a matsayin mai bayar da taimako a ofis (office assistance), a ofishin kansilan ayyuka (councilor for works), wanda a wancan lokacin Sir Ahmadu Bello Sardauna ke riƙe da wannan muƙami. Ayyukansa a wannan ofishi sun haɗa da rubuta takardu, tsattsara takardu, da kuma shisshirya su, da kuma dai dukkan wani aiki da ya shafi takardu wanda shugabansa zai iya saka  shi.
  2. Sakataren Ofishin Kansilan Ayyuka, daga baya an ɗaukaka darajarsa zuwa muƙamin sakatare.
  3. 1952 – 1966, wakili a Majalisar Wakilai ta Gwamnatin Yankin Arewa (member of the Northern Regional Legislative Assembly) da aka yi a Kaduna.
  4. 1956, an yi masa muƙamin kansila mai kula da gidan yari, ‘yansanda, da kuma ayyuka (Councilor in charge of Prison Services, Police and Works). Matakin da shugabansa na farko wato Ahmadu Bello Sardauna ya bari shi kuma ya maye gurbinsa.
  5. 1960, ya zama kansilan ma’aikatar raya karkara (Councilor for Rural Development) wacce daga baya aka mayar da ita  ma’aikatar gona.

Zuwansa wannan ama’aikata ya bashi damar kai ziyarar aiki zuwa ƙasar Amurka da wata cibiya mai suna Rockefeller Foundation ta ɗauki nauyinsa. Bayan dawowarsa daga wannan ziyara ya yi amfani da ilimin da ya samo wajen haɓɓaka harkar noma a iya faɗin Lardin Sakkwato.

  1. Ya riƙe muƙamin kwamishina a ma’aikatar lafiya ta sabuwar Jahar Arewan-Yamma (Northwest State), jahar da ke da helikwata a Sakkwato, wacce kuma ta haɗiye jahohin Sokoto, Kebbi, Zamfara da kuma Neja.
  2. Ya zama Kwamishinan Ayyukan Gona na Jahar Arewan-Yamma (Commissioner for Agriculture in the Northern-Western State). Daga cikin irin gudunmawar da ya bayar akwai gina dama-damai, da kuma samar da hanyoyin noman rani a duk faɗin wannnan jaha.
  3. 1976, ya zama shugaban hukumar ma’aikatan ƙananan Hukumomi ta Jahar Sakkwato (Chairman Sokoto State Local Government Civil Service Board).
  4. Ya riƙe muƙamin shugaban jama’iyyar NPN na jahar Sakkwato (NPN Sokoto State Chairman).
  5.  Ya riƙe muƙamin jami’in tuntuɓa tsakanin Jahar Sokoto da Gwamnatin Tarayya (Liaison Officer in the Office of the President of the Federal Republic of Nigeria Attached to Sokoto State) a zamanin Shugaba Shehu Usman Aliyu Shagari.
  6.  1985 – 1988, ya riƙe muƙamin Shugaban Majalisar Cikin Gida ta Daular Musulunci (Inner Council), ita kuwa wannan majalisa, majalisa ce ta musamman da aka kafa ta, da nufin taimakawa Sarkin Musulmi Abubakar III gudanar da ayyukan sa saboda tsananta da yanayin rashin lafiyarsa ta yi. Saboda wannan dalili ne ya saka gwamnatin Sakkwato ta wancan lokacin ta kafa wannan majalisa, wacce kuma aikinta ya ƙare nan take bayan rasuwar Sarkin Musulmi Abubakar III.

Sarauta

  1. 1952, Chiroman Sakkwato.
  2. 1953, Sarkin Kudun Sakkwato, hakimin Talatan Mafara.

Malam Muhammadu Maciɗɗo, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen haɓɓaka wannan guduma tasa ta Talatan Mafara, farkon abin da ya fara yi shi ne zaburantar da jama’a wajen ƙara ƙaimi kan harkar noma. Shi da kansa ya shaci wata gona da ya ke ɗaukar ma’aikata suna zuwa su yi masa noma sannan kuma ya biya su. saɓanin yadda aka saba a al’adar sarakuna a wancan lokacin, sai dai kawai a kai mutane gonar sarki su yi noma ba kwabo. Sannan kuma yakan ma je gona, masu aiki suna yi shi kuma yana saka ido ta hanyar kewaya gona da sauran ‘yan abubuwan da ba za a rasa ban a saka hannu a cikin aikin. Wannan adalci nasa wajen biyan ma’aikata haƙƙinsu yadda ya dace, ya saka jama’a daga sauran sassa su ke tururuwa zuwa Talatan Mafara dan samun shiga wannan aiki.

Wani abun sha’awa da wannan aiki nasa shi ne cewa, a duk ƙarshen damina, bayan ya fitar da zakka, yakan ɗauki wannan kayan amfani ya rarraba wa jama’a da suka haɗa da mahaifinsa sarkin Musulmi Abubakar III, bayinsa, da kuma sauran talakawa mabuƙata kafin ya ɗauki ragowar zuwa gidansa dan amfanin iyalansa.

Daga cikin abubuwan ambato da ya bari a lokacin zamansa na hakimi, ya riƙa cire kuɗin aljihunsa yana biya wa talakawansa haraji, abin da ya haifar da zage dantse wajen talakawan su ga cewar sun biya.

Siyasa

  1. A jamhuriya ta farko, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Macciɗo, ya zama mamba na Jama’iyyar Mutanen Arewa (Northern Peoples Congress (NPC)), bayan dogon lokaci da jama’iyyar ta ɗauka tana yaɗa manufofinta ta hanyar rubuta wa sarakunan Arewa wasiƙar da ke wayar da kan su game da wannan jama’iyya.
  2. Jamhuriyya ta biyu, da farko ya fara shiga jama’iyyar GNPP wacce ya tsaya wa takarar neman kujerar gwamna, daga baya kuma ya koma NPN. Tun da farko, bayan dawowar dimokuraɗiyya karo na biyu, a cikin shekarar 1978, Alhaji Ibrahim Waziri ya roƙi alfarma a wajen mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III, mahaifin Sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo da ya ba shi shi, ya yi masa takarar gwamnan jahar Sakkwato a jama’iyyarsa ta GNPP, wanda shi kuma Mai Alfarma Abubakar III ya ce matuƙar dai shi Alhaji Muhammadu Maciɗɗo ya amince, to shi fa ba shi da ja. Wanda kuma hakan aka yi, Alhaji Waziri Ibrahim ya kirayi Alhaji Muhammadu Maciɗɗo da wannan buƙata kuma ya amince.

Daga baya, sai Malam Shehu Shagari da wasu jama’a suka sake roƙar Alhaji Muhammadu Maciɗɗo da ya bar waccar jama’iyya ta GNPP, ya dawo NPN ya yi musu wannan takara. Haka Alhaji Muhammadu Maciɗɗo ya sake amince wa da wannan buƙata bisa tasirin abokai da aka kama ƙafa da su, ya mayar wa da jama’iyyar GNPP kayan takarar su ya kuma karɓi na NPN.

Zamowarsa Sarki

Bayan rasuwar sarkin Musulmi Abubakar III. Gadon wannan kujera ya zo da tangarɗa, inda da farko gidan radiyon Rima ya bayar da sanarwar naɗin Alhaji Muhammadu Maciɗɗo a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa. Sanarwar da ta haifar da murna daga cincirindon mutanen Sakkwato, wanda ya saka ‘yankasuwa rufe rumfunan su, da sauran jama’a, amma wannan murna ta su daga baya ta koma ciki, inda aka sanar da naɗin Alhaji Ibrahim Dasuƙi a matsayin sabon Sarkin Musulmi. Abin da ya haifar da tarzoma mai muni wacce ta sabauta rasa rayukan jama’a da dama.

A cikin shekarar 1996, gwamnan Sakkwato na wannan lokacin ya bayar da sanarwar tsige Alhaji Ibrahim Dasuƙi daga wannan kujera da kuma naɗa Alhaji Muhammadu Macciɗo a madadinsa. Wannan shi ne abin da ya kawo zamowar Alhaji Muhammadu Macciɗo sarkin Musulmi na 19 a wannan Daula ta Usmaniyya mai daɗaɗɗen tarihi.

Gudunmawarsa

Sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo Abubakar III, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ɗaukaka wannan daula ta Musulunci. Kamawa tun daga gina masallatan da suka haɗa  da na salloli biyar da kuma na juma’a, zuwa makarantu, taimakon ɗaiɗaikun jama’a, kyautata danganta tsakanin musulunci da sauran addinnai, da kuma samar da tsaro da zaman lafiya da sauran abubuwa masu tarin yawa.

Ayyukan Yau-da-Kullum

A cikin rayuwarsa ta yau da kullum, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, yakan tashi da safe kullum a tsakankanin 4:30 zuwa 5:00 na asubahin kowace rana dan shirya zuwa masallaci sallar Asuba wacce ya ke yi a masallacin da ke cikin gidan sarki. Bayan ƙare sallar Asuba, yakan zauna yana addu’o’i har zuwa fitowar rana kimanin 7:30 na safe.

Daga nan kuma sai ya shiga wajensa na musamman ya yi karin kumallo, sannan kuma ya samu ganin duk wanda ke da buƙatar ganinsa daga ɓangaren ‘yan’uwansa mata har zuwa 10:00 na safe.

Da misalin 10:00 na kowace safiya kuma, matuƙar da yana gari, akan ɗauki mai Alfarma Sarkin Musulmi zuwa masallacin Juma’a, inda ake gudanar da karatun Al-Ƙur’ani, bayan an ƙare kuma a yi addu’ar zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa da kuma neman rahama ga magabantasa, shi kansa, iyalansa, daular Musulunci, jahar Sakkwato, ƙasa baki ɗaya, da sauransu.

Daga 10:30 kuma, yakan koma fada dan sauraren jama’a. A wannan lokaci ne talakawa ke zuwa suna gaishe shi, da kuma hakimansa ko wakilan su. Haka nan ma Gwaggon Kano, matar marigayi Ahmadu Bello Sardauna, kan tura wakilanta su gaishe da sarki.

Bayan dukkan sauran jama’a da kuma wakilan masu riƙe da muƙaman sarauta na wannan masarauta sun gama gaisuwa, sai kuma mashawartan (Councilors) wannan fada su shigo wanda Waziri Alhaji Usman Junaidu ke wucewa gaba saura kuma na biye da shi. Bayan duk sun shiga sun zauna, sai kuma zaman majalisa na safe ya fara. Kaɗan daga cikin abubuwan da suka fiye faruwa a wannan majalisa akwai Musuluntar da waɗanda ba Musulmi ba, bayar da takardar shedar canjin suna, tallafawa waɗanda suka Musulunta da kuɗaɗe dan gudanar da kasuwanci, da sauran su.

Da misalin 1:00 na rana kuma, sai majalisa ta tashi. Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi shirin sallar Azahar har zuwa sallar La’asar. A wannan tsakanin ne sarki ke cin abinci, sannan kuma ya samu ya huta.

4:00 na yamma, bayan sallar La’asar, shi kuma wannan lokaci ne na sauraron karatuttuka da malamai ke gudanarwa wanda ake kama-kama daga wannan malami zuwa wannan a fannoni ilimin addini daban-daban, kamawa daga fassarar Al-Ƙur’ani, Hadisai, da sauransu. Wannan kuma ana yi ne a ranakun Asabar zuwa Laraba.

Daga 4:30 zuwa 6:00 na yamma kuma, lokaci ne da Sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo ya ke sake sauraron koken jama’a da sauran bayanai daga gare su.

Daga 6:30 kuma har zuwa 8:00 na dare, Sarkin Musulmi yakan zauna a cikin masallacin fada dan yin sallar Magariba, sannan ya jirayi sallar Isha. Daga 8:00 kuma zuwa 9:00, sai ya sake sauraron jama’arsa. Da zarar ƙarfe 9:00 ta yi, sai kuma ya koma wajen iyalansa.

A ranakun Talata kuma, sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo yakan je fadar gwamnatin jahar Sokoto dan halartar zaman tattaunawa kan harkar tsaro (security meeting).

Larabar ƙarshen kowane wata, ita kuma rana ce ta zaman majalisar sarki, inda ya ke zama da dukkan hakimansa da kuma masu naɗin sarki. A ƙarshen wannan zama ne ake sanar da faruwar abubuwan da suka haɗa da rasuwar wani mai sarauta, sabon naɗin sarauta, umarnin da ya fito daga gidan gwamnati, sanar da aukuwar wata annoba da kuma matakin da za a ɗauka game da ita, da sauran abubuwa da suka shafi wannan.


Hoto, shafin onlinenigeria
Jirgin da ya yi hatsari da Marigayi Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo

Rasuwarsa

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo Abubakar III, ya rasu shi da ɗansa Badamasi Maciɗɗo a ranar 29 ga watan Oktoba na shekarar 2006 a wani hatsarin jirgin sama ƙirar boing 737 na wani kamfanin sufurin jirage mai suna ADC, jim kaɗan bayan tashin jirgin daga filin jirgin sama na Abuja, da tazarar da bata wuce kilomita biyu ba a wata unguwa da ke kusa da filin jirgin mai suna Tunga Madaki.

Sarkin Musulmi Muhammadu Maciɗɗo ya rasu yana da shekaru 80 a duniya, bayan ya riƙe wannan kujera mai daraja na tsawon shekaru 10.

An yi jana'izar sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, aka kuma binne shi bisa sunna a Hubbaren Shehu da ke cikin garin Sakkwato.


Hubbaren Shehu

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ayobolu J. (2006). The Death Sultan Muhammadu Maciɗɗo. An ciro a shekarar 2017, daga shafin: http://www.gamji.com/article6000/NEWS6478.htm

Britannica (2006). Muhammadu Maciɗɗo Sultan of Sokoto Nigeria. An ciro a shekarar 2017, daga shafin: https://www.britannica.com/biography/Muhammadu-Maccido


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub