Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare,   ɗa ne ga  Sarkin Musulmi Abubakar Atiƙu, shi kuma ɗan Shehu Usmanu Mujaddadi. Shi ne Sarkin Musulmi na goma sha huɗu.  An yi masa mubaya’a a Ƙofar Fadar Sakkwato a ranar Juma’a 11 ga watan Sha’aban.


Fadar Sakkwato

Ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen raya masallatai. Shi ya sake sabunta masallatan Juma’a na Shehu Usmanu da kuma na Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo. Sannan shi ya sabunta Ƙubba; ɗakin da ƙabarin Shehu Usmanu Mujaddadi ya ke a ciki, da kuma dukkan Hubbaren na Shehu.


Ƙubbar Hubbaren Shehu

Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare ya kuma gina wasu masallatan masu yawa a faɗin ƙasar Sakkwato; wasu na salloli biyar wasu kuma na sallar Juma’a. A zamanin Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare Turawa suka ci sassan Sakkwato; suka rushe gidaje.

Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare shi ne sarki na farko da ya fara hawa keken dawaki a Sakkwato. Daga baya kuma ya sayi mota tare da saya wa babban ɗansa da ke sarautar Gobir wani keken dawakin.

Sannan a zamaninsa aka fara busa algaita da daddare a cikin garin Sakkwato, dan sanar da mutane lokacin hana fita daga gida, sakamakon sace-sace da suka yawaita a garin na Sakkwato.

A lokacin Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare yaƙi ya ɓarke tsakanin Turawan Ingilishi da na Jamus kan mallakar yankin Kamaru, inda Turawan Ingilishi suka yi galaba a kan na Jamus bisa gudunmawar yankunan da Birtaniya ke yi wa mulkin mallaka wanda Daular Sakkwato tana daga ciki.

A zamaninsa aka fara zaman majalisa na mako-mako tasakinsa da Turawa. Wannan kuma ya biyo bayan wata maƙarƙashiya da wasu ashararai a garin na Sakkwato suka ƙulla masa da nufin kawo ƙarshen mulkin nasa, kuma Allah bai yardar musu ba. Su waɗannan ashararai sun haɗa baki ne da dukkan sarakunan da ke yankin Sakkwato suka riƙa rubuta munanan bayanai, suna yaɗa su game da sarki, har sai da bin ya kai kunnuwan Turawa, inda su kuma Turawa suka tayar da ɗaya daga cikin su ya kewaya yankin na Sakkwato dan tantancen gaskiyar lamarin. Da waɗannan asharari suka samu labarin wannan rangadi na wannan Bature, sai suka tafi cikin sirri suka ce da dukkan sarakunan duk abubuwan da Turawa suka tuhumi Sarkin Musulmi da su, su amsa da cewa haka ne.  Daga ƙarshe dai wannan farfaganda ta kusa yin nasara dan sai da ta kai ga gwamnan Najeriya na wannan lokacin ya ziyarci Sakkwato daga Ikko da nufin cire Sarkin Musulmi. Amma Allah cikin ikonsa daga irin tarbar da aka shirya masa da kuma halartar sarakunan yankunan, gwamna ya tabbatar da cewa duk abubuwan da aka tura masa maƙarƙashiya ce. Saboda haka ya mutunta sarki bai tuɓe shi ba.

Bayan shekara guda da afkuwar wannan lamari, Sarkin Musulmi ya nemi zuwa Ikko dan yin godiya ga gwamna, sai shi gwamna ya sauƙaƙa masa tafiyar, ya ce su haɗu a Zazzau, wanda kuma hakan aka yi Sarkin Musulmi ya je can suka haɗu.

Bayan dawowar Sarkin Musulmi daga Zazzau, sai rashin lafiya ta kama shi, wacce ta yi ta ƙaruwa sannu a hankali har ta zama ajalin sa. Ya rasu a ranar Laraba 14 ga watan Zulhijja bayan ya yi sarauta ta tsawon shekaru tara da watanni biyar. Ya rasu yana da shekaru 70  duniya.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub