Sarkin Musulmi Muhammadu Tambari

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Musulmi Muhammadu Tambari


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Muhammadu Tambari, shi ne Sarkin Musulmi na goma sha biyar a jerin sarakunan Musulunci. Shi ɗa ne ga Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare, shi kuma ɗan Sarkin Musulmi Ahmadu, shi kuma ɗan Sarkin Musulmi Abubakar Atiƙu, shi kuma ɗan Shehu Usmanu Mujaddadi. An yi masa mubaya’a ranar Litinin a ƙarshen watan Muharram bayan kwanaki arba’in da rasuwar mahaifinsa sakamakon rigingimu da suka biyo bayan mutuwar mahaifin nasa dangane da gadon wannan kujera ta wannan sarauta ta Musulunci.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub