Takalmin Kaza...

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Takalmin Kaza...

Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji
Inkiya: Fadar Mai Martaba Ɗan’alin Birnin Magaji, Birnin Magaji Jihar Zamfara,
Jihar Zamfara Nijeriya
+2348149388452 birninbagaji4040@gmail.com


Tsakure

Maƙala kan Marigayi Makaɗa Sa’idu Faru ta ginu domin shiga sahun marubuta maƙalu a samar da kundin karrama Sa’idu Farun. Sa’idu Faru Mawaƙi ne na baka cikin Hausa. Sa’idu Faru mawaƙin rukunin manyan mutane ne, da Sarakai na ƙasar Hausa. Sauraren waƙoƙinsa na manyan mutane musamman na sarakuna, da nazarin ƙumshiyarsu, da neman tarihin abinda ya samar da waƙoƙin nasa ya yunƙurar da azamar wannan maƙala. Bayan na saurari tattaunawar da aka yi da shi lokacin da yake raye, da kuma wasu bayanai da masu gidansa Sarakai suka gabatar game da shi, sai na fahimci matsayin da ya bai wa kansa da kuma lura da matsayin da yake da shi a wajen Sarakai. In dai sarauta da waƙoƙin sarauta a ƙasar Hausa za a yi nazari to ba za a tsallake na Sa’idu Faru ba. In ko shahararren mai zalaƙar baka ake neme, to Sa’idu shi ne kullume. Takalmin kaza mutu ka raba na nuna irin zamantakewa mai nuna ƙauna tsakanin basarake da baransa kamar yadda ya kasance tsakanin Sa’idu Faru da Muhammadu Macciɗo.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub