Mukala kan Dankwairo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙasar Zamfara a Bakin Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun


Alhaji Ibrahim Muhammad
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Fadar Mai Martaba Sarkin Birnin-Magaji (Ɗan Alin Birnin-Magaji), Jihar Zamfara.
08149388452
birninbagaji4040@gmail.com


Tsakure

Wannan aiki a kan Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ne. Za a dubi fasihancinsa na adana tarihin ƙasar Zamfara a waƙe. Idan aka dubi ayyukan da suka gabaci wannan maƙala kan Alhaji Musa Ɗanƙwairo, za a daidaita sahun tunanin duk abinda aka ci karo da shi ta hanyar binciken Tarihinsa da tarihin waƙoƙinsa a bakin ‘ya’ya da jikoki da aminansa waɗanda ke raye. Wannan zai kai wannan bincike ga amfani da nau’in bincike na tattaunawa da kai ziyarar gani da ido a wurin mutane da wurare daban-daban. Wannan zai samu jagorancin ra’o’i guda biyu: Ra’in Tushe da Asali da Ra’in Fandarewa. Wadannan ra’o’i sun tsayu a cikin wannan aiki domin sanin asalin Musa Dankwairo, da kuma taskace tarihinsa da wakokinsa a cikin ayyukan da aka gabatar kansa. A fahimtar da na yi wa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun saboda sauraren waƙoƙinsa da nake yi tsawon lokaci, yana da matsayin da tarihin mawaƙan ƙasar Hausa da na Zamfara ba zai cika ba, ba tare da kawo sunansa da waƙoƙinsa ba. Fasihancinsa a waƙe, ya zama tamkar kotun yanke hukunci ga kowane al’amari na rayuwa.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub