Tatsuniya: Gizo Ɓarawon Gyaɗa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Gizo Ɓarawon Gyaɗa


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

A wani gari akwai wani sarki, yana da babbar gona. Sai ya shuka gyaɗa a wannan gona tasa. Ana nan, a nan, sai gyaɗar nan ta yi yabanya mai kyau, aka nome ta tsaf, ta rankatsa ‘ya’ya.

Da Gizo ya ga gyaɗar nan ta nuna, sai ya riƙa ɗaukar matarsa Ƙoƙi suna zuwa gonar nan, suna satar gyaɗa. Sannu a hankali har sarki ya gane ana yi masa satar gyaɗa. Shi ke nan, sai wata rana sarki ya ce, ya kamata mu ɗana wa mai satar gyaɗar nan tarko mu kama shi. Sai ya saka fadawa suka je gonar suka yi mutum-mutumin budurwar danƙo, sannan aka ajiye abinci shi ma na danƙo a gabanta.

Da Gizo ya je gona satar gyaɗa sai ya ga budurwar nan, sai ya ce, ‘yar budurwa-budurwa, na ɗan ci abincin naki ne? Sai ta yi shiru ba ta ce komai ba, sai Gizo ya saka hannu zai ci abinci, sai hannun ya manne a cikin abincin. Sai Gizo ya ce, to ba ga ɗaya hannun ba. ‘Yar budurwa-budurwa, in ɗan taɓa nonon naki ne? Sai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Sai Gizo ya taɓa da ɗaya hannun. Sai shi ma ɗaya hannu ya manne. Sai Gizo ya ce, to ai ga ƙafafu nan. Sai ya dunguri jikin budurwar nan da ƙafafuwansa, sai duk suka manne a jikin budurwar nan.

Can sai sarki ya tafo da shi da fadawansa. Sai suka ga Gizo manne a jikin budurwa. Sai suka ce, ashe dama kai ne ɓarawon gyaɗar. Sai suka kama shi suka ɗaure a jikin bishiya, suka tafi su nemo bulalu.

Bayan sun tafi neman bulalu, sai ga kura ta zo wucewa. Da kura ta ga Gizo ɗaure a jikin bishiya, sai ta ce da shi, Gizo ya na ganka a ɗaure? Sai ya ce, wasu ne suka ɗaure ni suka tafi su samo min nama. Da kura ta ji haka sai ta ce da Gizo, in kwance ka, ka ɗaure ni? Sai Gizo ya ce, yaya kura ai duk abin da ki ka ce shi za a yi. Sai kura ta kwance Gizo shi kuma ya ɗaure ta. Bayan ya ɗaure ta sai ta ce da shi, nan bai ɗauru ba. Shi kuwa Gizo ya ɗaure ta tamau. Sai ya gudu ya hau kan bishiyar kanya.

Bayan wani lokaci kaɗan, sai kura ta hango mutane sun nufo ta da bulalu a hannayensu. Sai hankalinta ya tashi ta fara kururuwa tana zawo, can da suka fara zumbuɗa mata bulalu, ta ji ba daɗi, sai ta samu ta fincike igiyar nan da ƙarfi, ta ruga da gudu. Bayan ta gudu sai ta je gindin bishiyar kanyar nan da Gizo ya ke kai tana hutawa. Can sai Gizo ya jefo mata guburin kanya a kanta ral! Sai kura ta sosa kan. Zuwa can an jima sai ya sake zubo mata da kanya nunanniya mai kyau, sai ta kama sha ta ce kai, amma fa ɗan tsuntsun nan yana sona. Bayan ta gama shanye nunanniyar kanyar, sai ya sake zubo mata da guburi a kanta. Da ta ji zafi, sai ta ɗaga kai ta ce, kai bari dai na leƙa ɗan tsuntsun nan. Tana cira kanta sama kawai sai ta hango Gizo. Sai ta ce da shi, da ma kai ne? To, sauko na cinye ka. Sai Gizo ya ce da ita, to kin ga idan kina so ki kama ni, to, ki je gindin kargon can, a can zan dirgo. Sai kura ta tafi Gindin kargo ta tsugunna. Can sai Gizo ya faki idon kura ya sauko ya fita da gudu, ya tsere.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub