Me ka ke nema?


Shafin Farko

Masarautar Wukari


Gabatarwa

Wukari, kamar yadda aka fi kiranta, ita ce helikwatar masarautar Wukari. Asalin sunanta shi ne Ukari, wacce kuma kalma ce ta Jukunanci, wacce ke da ma’ana ta ka fifita (you have surpassed). Masarauta ce da aka kafa ta a shekarar 1596 bayan rushewar Daular Kwararrafa.

Tushe

Bayan rushewar Daular Kwararrafa wacce ke da helikwata a Api, sai Jukunawa waɗanda su ke tun asali su ne ke shugabanta waccar daula ta Kwararrafa suka matsa gaba zuwa wannan bigire, suka kafa garin da a yanzu ake kira Wukari. Ita kuwa wannan kalma ta Wukari, asalinta shi ne Ukari, wacce kuma kalma ce ta Jukunanci mai ma’ana ta ka fifita (you have surpassed). Sarkin Jukunawa na 40, Aku Uka Katakpa, shi ne ya jagoranci wannan ƙaura a cikin shekarar 1596 (Adamu, 2016; Oleyede, 1996). Dukkan wanda ke shugabantar wannan masarauta, shi ake kira Aku Uka, kalmomin da ke da ma’ana ta sarkin da ya fifici kowane sarki a duniya; wato sarkin da ya fi kowane sarki a duniya (Adamu, 2016).

Wannan gari shi ne ya zamo tubulin canjin tarihin Jukunawa, ya kuma zama sabuwar helikwatar daular Jukunawa zalla, a maimakon daular haɗaka ta Kwararrafa da Jukunawa suka shugabanta wacce ke ƙunshe da mabanbantan yarurruka.

Jama’a

Tun da fari, garin Wukari an kafa shi ne unguwa-unguwa, wanda kuma kowace unguwa mazauna cikinta kusan zuriya guda ce. daga cikin irin wannan unguwanni akwai Go-Ndoku, wacce ke nufin gidan sarki ko fadar sarki. Sai kuma wasu unguwannin da suka haɗa da Kinda Kuvyo, Adikyu-Gashi, Ndo Abonta, Kwanse, Ndo-Nwugye, Tsupando, da sauransu (Adamu, 2016).

Gari ne wanda ke kewaye da ganuwa da kuma ƙofofi guda bakwai duk da cewa a yanzu, ƙofar arewa ce kaɗai ta saura da jama’a ke amfani da ita; wacce kuma a zamanin baya, mafita ce ta gawarwakin jinin sarauta. Haka nan kuma a tsakiyar garin akwai tsohuwar kasuwar da tun da aka kafa garin take.

Sahun farko na sauran yarurruka mazauna wannan gari na Wukari akwai Gobirawa, waɗanda kasuwanci ya kai su garin kuma suke zaune kusa da fadar sarki, wanda har ta gai ga shugabansu mai suna Maiwuya ya auri ‘yar sarkin Wukari na wancan lokacin abin da ya bashi damar da aka yi masa sarkin kasuwar wukari, wanda ke da alhakin tattara haraji.

Haka nan kuma a shekarar 1932, a zamanin Aku Amadu Agbumanu, wasu jama’a daga Sakkwato sun ƙaura zuwa Wukari, biyowa bayan tuɓe sarkin Musulmi Muhammadu Tambari da aka yi, wanda kuma ya yi gudun hijira zuwa garin na Wukari, inda a can ya rasu kuma aka binne shi a can. A yanzu haka sauran zuriyarsa suna zaune a wannan gari na Wukari a wata unguwa da ake kira Unguwar Sakkwato wacce ke daura da Akata.

Bayan zamowar wannan gari na Wukari helikwatar masarautar Jukunawa, shi ne kuma helikwatar ƙaramar hukumar Wukari a ƙarƙashin jahar Taraba. Yanzu haka wannan gari yana da ci gaban da har ta kai ga yana da jam’o’i guda uku da kuma sauran manya da ƙananan makarantu.

Daga farkon kafa wannan gari zuwa yau, sarakuna ishirin da huɗu ne suka shugabance shi. na farkonsu shi ne Angyu Katakpa (1596 – 1615), sai kuma na ƙarshe wanda har yanzu yake kai (Dr.) Shekarau Angyu Masa-Ibi, Kuvyo II (1976 zuwa yau).

Manazarta:


Adamu  Ɗ. A. (2016). Shekarau Angyu Masa-Ibi, An Autobiography of the 24th Aku-Uka, as Told to Ɗanjuma A. Adamu. An buga a Able Productions tare da haxin Guiwar Animation Books.

Oluyede I.O. (1996). Shaped by Destiny, A Biography of (Dr.) Shekarau Angyu Masa-Ibi, Kuvyo II, The Aku Uka of Wukari. University of Ilorin.

Tattaunawa da (Dr.) Shekarau Angyu, Masa-Ibi, Kuvyo II, Aku Uka na Wukari, a ranar Asabar 19/08/2017, a fadarsa da ke Wukari

Masarautar Wukari

Sarakunan jukunawa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub