Zariya Kofar Kuyambana

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zariya Ƙofar Kuyambana


Wannan ƙofa ta samo asalin sunanta ne daga garin Kuyambana wanda ke da nisan tazarar mil 80 (80 miles) daga birnin Zariya. Wannan kuma ta faru ne saboda zamowar ƙofar kafar shigi da fici tsakanin Zariya da wannan gari na Kuyambana, bayan da sarauniya Amina ta ci Kuyambana da yaƙi sannan kuma ta naɗa digacin da zai riƙa kula da garin a madadinta. Wannan ƙofa ta taka muhimmiyar rawa wajen kai-komo tsakanin Zariya da garin na Kuyambana.

Manazarta:


Arnette E.J. (1920). Gazetteer of Northern Provinces of Nigeria. Gazetteer of Zaria Province. Waterlow & Sons Limited. London, Dunstable & Waterford.

Dalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru Dan Isyaku, The Great Emir of Zazzau. Woodpecker Communication Limited. Zaria-Nigeria.

Suleman U. (2007). A History of Birnin ZAria from 1350 – 1902. M.A. History, Ahmadu Bello University, Zaria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub