Sarkin Zazzau Abdussalami

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Malam Abdussalami Basulluɓe 1853 – 1857 A.D.


Gabatarwa

A ƙoƙarin sa na toshe ɓarakar da ke akwai ta gadon sarautar Zazzau daga gidajen sarauta guda uku; Mallawa, Barebari da Katsinawa, Sarkin Musulmi ya yi umarni da naɗin Malam Abdussalami Basulluɓe a matsayin sabon sarkin Zazzau.

Faruwar wannan lamari ta saka shi Malam Abdussalami zamowa sarkin Zazzau na sittin da bakwai sannan kuma sarki na bakwai a jerin sarakunan Fulani, sannan kuma sarki na farko daga gidan Sulluɓawa.

Shi yake riƙe da muƙamin Makama tun zamani sarki Musa Bamalli, sannan kuma shi ne ya saura daga cikin mutanen da suka yi zamani da Shehu Ɗanfodiyo, saboda waɗannan dalilai da kuma tsoron afkuwar rarrabuwar kai tsakanin waɗancan gidajen sarauta, suma suna daga cikin dalilan naɗa shi a matsayin sabon sarkin Zazzau.

Duk da haka, Sarki Abdussalami bai samu sukunin aiwatar da wani abu da ya hafi ci gaban masarautar ta Zazzau ba, saboda rigingimun cikin gida da suka yiwa wannan masarauta tasa katantanwa. Bayan waɗancan gidaje guda uku, suma kansu sulluɓawan sun kasu kashi biyu, akwai Sulluɓawan Ibada, wanda shi Malam Abdussalami ya fito daga cikinsu, sannan kuma akwai Sulluɓawan gidan Ja’e waɗanda suke a Ricifa.

Malam Abdussalami Basulluɓe ya riƙe kujerar Sarautar Zazzau tsawon shekara huɗu, sannan ya rasu a fagen yaƙi a shekarar 1857. Sannan kuma shi ne na farko kuma na ƙarshen Basulluɓen da ya riƙe sarautar Zazzau.

Manazarta:


Ɗalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru ɗan Isiyaku, The Great Emir of Zazzau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press. Zaria – Nigeria

Northern Nigeria Ministry of Information (1965). The Fascinating Provinces of Northern Nigeria. Gaskiya Corporation, Zaria-Nigeria. Smith M.G. (1970). Government in Zazzau 1800-1950. London:

Oxford University Press for the International African Institute. 371p. (Amaury Talbot Book Prize). Reprinted in 1964 and 1970.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub