Sarkin Zazzau Muhammadu Sabo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Malam Muhammadu Sambo ɗan Abdulkarimu 1879 – 1888


Gabatarwa

Bayan tsige sarki Abdullahi ɗan Hammadan a karo na biyu, sai ‘yan takara suka fito masu neman wannan kujera ta sarkin Zazzau. Mutanen da suke kan gaba wajen wannan takara akwai Madaki Yero, wanda yake ɗa ne ga shi Malam Abdullahi ɗan Hammadan, sai kuma Wambai Sambo, shi ɗan Abdulkarimu ne, sai kuma Malam Zubairu ɗan Malam Musa wanda ya fito daga zuriyar Mallawa. Smith (1970), da Ɗalhatu (2002) duk sun faɗi hakan.

Galadiman Zazzau malam Adamu shi ya raka waɗannan ‘yan takara uku zuwa Sakkwato, wanda daga cikinsu Allah cikin ikonsa ya saka aka zaɓi shi Malam Muhammadu Sambo. Sarkin Musulmi Mu’azu ne ya naɗa shi kamar yadda Ɗalhatu (2002) ya bayyana.

Wannan naɗin nasa tare yake da umarnin naɗa abokin takararsa Zubairu daga ɓangaren Mallawa a matsayin Wamban Zazzau da kuma ci gaba da barin ofishin Ɗangaladima duk a ɓangaren Mallawa. Hakan kuma ya yi bai saɓa ba.

Waɗannan naɗe-naɗe da ya yi bisa umarni, sun ragewa sarautarsa ƙarfi, saboda haka dole ta sa ya ƙirƙiri wasu muƙaman da ya damƙa su a hannun magoyin bayansa kuma zuriyar haɓe, mai suna Salmanu. Sarki Sambo, bayan barin Salmanu da ya yi a matsayin Sarkin ruwa, ya kuma ƙara masa da sarautar Galadiman Zazzau. Wannan ta bashi wata ‘yar damar da ya samu natsuwar da zai iya fita wajen garin dan faɗaɗa masarauta da kuma ƙarfafa dangantaka da sauran maƙwabta.

Ɗalhatu (2002), ya kawo cewa, wancan ƙarfi da Salmanu ya samu ta bashi damar haɗa kai da sarkin Ningi Haruna, wanda shi ma haɓe ne cewa idan lokacin tafiya Sakkwato ya yi, shi sarkin Ningi Haruna ya haɗo tawaga ya zo garin Yakasai, wanda gari ne na Haɓawa da ke kusa da Zariya ya tare tawagar Sarki Sambo ya yaƙe su. Cikin rashin sa’a, amsar da sarki Haruna ya turowa Galadima sai ta faɗa hannun sarki Sambo lokacin yana daidai Tukur-Tukur bai yi nisa da gari ba.

Faruwar wannan lamari ta tursasawa sarki Sambo juyowa baya, amma kafin ya kai ƙofar Tukur-Tukur, rundunar sarkin Ningi suka far masa da yaƙi.

Haka nan kuma dai ya sake samun hari daga sarkin Damagaran ɗanbaskore, wanda shi ma haɓe ne. wannan runduna ta ɗanbaskore ta ratso Katsina ne ta zo ta cinye Kudan da yaƙi. Faruwar waɗannan yaƙe-yaƙe ta tabbatarwa da Sakkwato sarki Sambo ba zai iya riƙe Zazzau ba. A saboda haka sai sarkin Muslmi ya tsige shi.

Manazarta:


Ɗalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru ɗan Isiyaku, The Great Emir of Zazzau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press. Zaria – Nigeria

Northern Nigeria Ministry of Information (1965). The Fascinating Provinces of Northern Nigeria. Gaskiya Corporation, Zaria-Nigeria.

Smith M.G. (1970). Government in Zazzau 1800-1950. London: Oxford University Press for the International African Institute. 371p. (Amaury Talbot Book Prize). Reprinted in 1964 and 1970.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub