Zinder

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zinder


Gabatarwa

Kalmar Zindar wadda ake rubuta ta da Zinder, suna ne na wani gari mai daɗaɗɗen tarihi. Garin ya soma ne daga matsugunnin Hausawa daga baya kuma wasu maharba Barebari suka jirkita shi ya koma koma cibiyar Daular Musulunci ta Damagaran, sannan ya zama helikwatar sojojin mulkin mallaka na Faransa, daga ƙarshe kuma ya zama babbar alƙaryar da ke a matsayin helikwatar jahar Damagaran a jamhuriyyar Nijar.

Sunan garin ya samo asali ne daga kalmar nan ta Hausa wato zindir, wadda ke da ma’ana ta tsirara, saboda irin shigar da maharban gurin ke yi idan za su shiga daji farauta.

Asali
Asalin Garin Zinder wani ɗan ƙaramin garin Hausawa ne (Wikipedia, 2017) daga baya kuma ya koma matsugunnin Barebari mafarauta (In ji Wakilin Tarihi, 2017), waɗanda suka zauna a kan dutse, sannan ya sake koma babban garin Hausawa tare da zamowar masu sarautar garin Barebari, kuma cibiyar mulkin daular Musulunci ta Damagaran.

Wannan gari mahaɗa ce da ke kan tsohuwar hanyar Kasuwancin Sahara ko Kasuwancin Hamada wadda ke sada tsakanin manyan garuruwan Ƙasar Hausa, Daular Barno da kuma wasu sassan duniya da suka haɗa da Agadas, Alje, Turai da kuma yankunan Larabawa.

Ana Kiran wannan gari da suna Zindar ne bayan da sarki Sulaimanu ya taso da fadar daular Musulunci ta Damagaran daga garin Gafati, a cikin shekarar 1822 AD. Sai dai, shafin Wikipedia (2017), ya ruwaito cewa, a shekarar 1736 aka yi wannan ƙaura zuwa Zinder.

A yunƙurin mutane na furta sunan sabon gurin da cibiyar daular ta koma, sai suka riƙa ambaton gurin da suna zindir, wadda kalma ce da ke da ma’ana ta tsirara. Wannan kuma saboda kasancewar waɗannan maharba da ke zaune a wannan waje basu da wata suturar da ta wuce warkin da suke yafawa idan za su fita farauta. Saboda haka sai mutane suka riƙa kwatanta gurin da garin Zindir; wato garin mutanen da suke yawo zindir ba tare da suturar da ta rufe dukkan jikinsu ba kamar yadda wakilin tarihin Masarautar Damagaran ya shaida mana a cikin tattaunawar mu da shi.
Sannu a hankali mutane suna kwatanta wannan waje da wannan suna garin Zindir, har sunan ya bishi ya zama cikakken sunan gurin. Da zarar mutum ya ambaci kalmar zindir, to an san yana nufin wannan gari kenan.

A lokacin da Turawa suka shigo wannan gari, sai suka jirkita wannan kalma ta zindir ta koma zinder kamar yadda ake rubutawa a yau ɗin nan.

Girma
Garin Zindar shi ne gari na biyu a yawan jama’a a duk faɗin ƙasar Nijar ta yau. Yawan jama’arsa za ta iya kai wa kimanin mutanen 200,000 a shekarar 2005 (Wikipedia, 2017).

Yana da nisan kilomita 861 daga Yamai (Niamey) babban birnin Nijar. Sannan kuma ta kudu yana da nisan kilomita 240 zuwa birnin Kano da ke tarayyar Najeriya.

Zuwan Turawa
Baturen Faransa mai suna Cazemajou, shi ne ya je garin Zindar a shekarar 1897 (Wikipedia, 2017). Wannan Bature ya je fadar sarkin Damagaran Ahmadu Kuren Daga, ya shiga har farfajiyar farko ta gidan wadda ke kewaye da dogwayen katangu da kuma zauruka da ake ratsawa kafin a kai gare shi. Sakamakon haka, Kuren daga ya sa aka aika da wannan Bature lahira da tawagarsa. Turawa sun ci wannan gari da yaƙi a cikin shekarar 1899 bayan shigar su garin da rundunar sojoji masu yawa da Lt. Pallier ya jagoranta.

Helikwatar Turawa
Garin Zindar ya taɓa zama helikwatar rundunar mayaƙan Turawa a cikin shekarar 1911. Gudun abin da ka iya faruwa na turjiya daga sauran garuruwan Hausawa saboda kusancin su da rundunar, da kuma ƙaruwar danƙon zumuncin da ke gudana a tsakanin garin na Zindar da kuma jarma (Djerma), ta saka Turawan ɗauke wannan runduna daga garin na Zindar ta mayar da shi Yamai (Niamey), babban birnin ƙasar.

Yanayi
Garin Zinder, shi ne gari mafi samun ruwan sama a duk faɗin Nijar kasancewarsa mai yanayi irin na Najeriya. Bincike ya tabbatar da cewa, kashi arba’in cikin ɗari na geron da ake nomawa a duk faɗin ƙasar Nijar daga Zinder ake samunsa (Hoddinott, Sandström da Upton, 2013).

Wannan dalili na kasancewar garin Zinder mai ni’imar ruwa, ya bai wa jama’ar yankin damar zama manoma sannan kuma makiyaya a lokaci guda; wato suna sana’ar noma da kuma kiwon dabbobi.

Manazarta


Hoddinott J., Sandström S. da Upton J. (2013). Impact Evaluation of Cash and Food Transfers in Zinder, Niger: Analytical Report. An ciro a shekarar 2017 daga shafin, http://documents.wfp.org/stellent/groups/public/documents/ resources/wfp257676.pdf

Wikipedia (2017). Zinder. An ciro a shekarar 2017 daga shafin, https://en.wikipedia.org/wiki/Zinder

Wikipedia (2017). Sultanate of Damagaram. An ciro a shekarar 2017 daga shafin, https://en.wikipedia.org/wiki/Sultanate_of_Damagaram

Tattaunawa da Alhaji Laminu, Magajin Gari (Kwatankwacin shugaban ƙaramar hukuma a Najeriya) Shiyyar Birnin Zinder a ranar 24/07/2017 a ofishinsa da ke garin Zinder a Nijar.

Tattaunaw da Wakilin Tarihi na fadar masarautar Damagaran a ranakun 24-30/07/2017 a fadar Masarautar Damagaran da ke birnin Zinder a Nijar.



Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub