Me ka ke nema?


Shafin Farko

Abdullahi Barja ɗan Kanajeji 1438 – 1452 Miladiyya


Gabatarwa

Abdullahi Barja shi ma ƙani ne ga Sarki Dawuda, shi kuma Ƙani ga Sarki Umaru dukkansu ‘ya’yan Sarki Ibrahim Kanajeji.  Sunan mahaifiyarsa Takiɗa. Sarkin Kano Abdullahi Barja ya zauna  a unguwar Garke.  Sarkin Kano Abdullahi Barja shi ne Sarkin da ya naɗa jikansa ɗan shekara shida a matsayin Makaman Kano. Wannan kuwa ta faru ne saboda abubuwan al’ajabi da wannan yaro ya riƙa yi.

Sarki Abdullahi Barja ya rasu yana da shekaru sittin da bakwai a duniya. Ya mulki Kano tsawon shekaru goma sha biyar. Ya rasu bayan wata gajeruwar rashin lafiya da ya yi ta tsawon kwanaki ishirin.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub