Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji Kabi Ɗan Kumbari 1743 – 1752 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Alhaji Kabi shi ne sarki na talatin da tara a jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Zainabu. Sarki Alhaji Kabi sarki ne mai Kwarjini da kuma son yaƙi. Tun yah au gadon sarauta bai taɓa zama gida na tsawon wata biyar ba, kullum yana fagen fama.

A zamanin sarki Kabi ne Gobir ta sake cin Kano da yaƙi. Saboda tsanin son yaƙinsa an yi ittifaƙi cewa ba wanda ya san adadin yaƙuƙuwan da ya yi. An ce shi ne sarkin da ya fi kowa yawan yaƙe-yaƙe a sarakunan Kano. Sarki Kabi ya mulki Kano tsawon shekara tara da wata bakwai kafin Gobirawa su kashe shi a wa fagen yaƙi.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub