Shafin Farko

Muhammadu Shashiri ɗan Yakufu 1573 – 1582 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Muhammadu shi ne sarki na ishirin da shida a jerin sarakunan Kano. Sunan mahafiyarsa Fatsumatu. Sarkin ne mai yawan alheri, an ce iya tsawon dukkan sarakunan da suka gabace shi ba wanda ya kais hi alheri.

A zamaninsa ya yaƙi ƙasar Katsina. Ya fita da nufin ko ya yi nasara ko a kashe shi kamar yadda y ace, “Idan na fita b azan dawo ba sai na rinjaye su, ko kuwa in mutu”. Da ya fita Katsinawa sun tare shi a Kankiya. A nan aka gwabza yaƙi, Katsinawa suka fatattaki Kanawa saboda sun fi su yawa. Amma shi da Santurakin Manya Narai, da Santuraki Kuka-zuga, da Ɗandunki basu gudu ba. Sarki ya yi matuƙar baƙincinki da aukawar wannan lamari, amma su Santuraki suka lallashe suka ce “ Kada ka yi fushi, ma rinjaye su shekara mai zuwa idan Allah ya yarda”.

Bayan dawowarsa daga yaƙin Katsina, sai ‘yan uwansa suka shirya za su kashe shi. Da Santurakin Manyan Narai ya samu labari sai ya ce sarki, “Kada ka fita da kai da limaminka yau, in ka fita za a kashe ka”. Sarki ya zauna a gida. Santurakin Manya Narai ya je ya zauna a gurin da saki ke zama, masu kisa suka zaci sarki ne, suka kashi da shi da ‘ya’yan sarki goma sha biyu. Sauran shida kuma daga cikin ‘ya’yan sarki goma sha takwas a kama su. Muhammadu Zaki ya yi nufin kashe su suka ce das hi, “Kada ka kashe mu jikokinka ne, ka maishe mu bayinka”. Sarki Muhammadu ya yi sarautar Kano ta tsawon shekaru bakwai da watanni huɗu da kwanaki ishirin da huɗu.  

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.