Shafin Farko

Muhammadu Rumfa 1463 – 1499 Miladiyya


Gabatarwa

Muhammadu Rumfa shi ne sarki na ishirin a jerin sarakunan Kano. Shi ne wanda aka yiwa sarautar Makaman Kano lokacin yana ɗan shekaru shida a duniya. Wannan kuwa ta faru ne bayan wani abin mamaki da ya faru da shi. Shi Muhammadu Rumfa asalin sunansa shi ne Muhammadu Mansur, kuma shi jika ne a gun sarkin Kano Abdullahi Barja. Abdullahi Barja shi ne mahaifin babar Muhammadu Rumfa (wato kenan shi Muhammadu Rumfa ya gaji sarautar Kano ne ta ɓangaren mahaifiyarsa).

A lokacin Sarki Abdullahi Barja, karnuka sun riƙa zuwa suna cinyewa talakawan Kano guntun tuwon da suka ci suka rage da daddare. Da al’amari ya yi ƙamari, sai talakawa suka haɗa kansu suka ɗunguma zuwa fada, da isar su fada sai Shamakin Sarki na wancan lokacin ya tunkare su ya tambayesu cewa me ke tafe da su. Sai suka amsa masa da cewa sun kawo ƙarar dukkan karnukan Kano ne. Daga nan sai Shamaki ya yi musu jagaba ya kai su gaban Sarki. Da isarsu gaban Sarki suka faɗi, suka yi gaisuwa sannan suka faɗi kokensu cewa karnuka ke zuwa da daddare suna cinye musu guntun tuwon da suka ci suka rage da daddare, wanda hakan ke jawo musu rashin na kummalo. Saboda haka suna ƙarar dukkan karnukan Kano. Da Sarki ya ji haka, sai ya ɗan yi shiru na jim kaɗan, sai ya juya ya tambayi fadawa ko da shawara. To a daida wannan lokaci wannan jika nasa mai suna Muhammadu Mansur yana gefen karagarsa yana wasa. Sai caraf! Ya ce da Sarki, su koma kawai su je su yi rumfuna a ƙofar ɗakunansu sai su riƙa ɗora gutun tuwon har da miyar a kan rufunan.

Talakawa suna ji, sai sarki ya ce kai ku rabu da shirme na yara. Fada mecece shawara? Sai Galadiman Kano Daudu, ya kada baki ya ce da sarki ai wannan magana ya yi ta hankali. Saboda haka sai su tafi su gwada. Sarki ya basu umarni cewa su je su gwada duk abun da ya faru sai su dawo gobe. Talakawa suka koma suka kakkafa rumfuna a ƙofar ɗakunansu.


Rumfa a gaban ɗaki

Sannan da dare ya yi aka ci tuwo aka rage sai suka ɗoɗɗora tuwo da miya a kan rumfuna. Da gari ya waye suka tarasa da tuwonsu ba abinda ya same shi. sai suka ɗauko suka ɗumama tuwon suka ci suka yi hani’an. Sannan sai suka sake ɗunguma zuwa fada a karo na biyu. Da suka isa sai Shamaki ya yi musu iso, suka je gaban sarki, suka sanar da sarki abinda ya gudana cewa wannan shawara ta yaro ta yi aiki. Sannan suka yiwa yaro addu’ar zamowa sarkin Kano a loto na gaba.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.