Shafin Farko

Usman Ɗan Abdullahi 1919 – 1928 Miladiyya


Gabatarwa

Sarki Usman ɗan Abdullahi, wanda ake yiwa laƙabi da Usman II. Shi ne sarki na 52 a jerin sarakunan Kano, sannan kuma sarki na 9 a jerin sarakunan Fulani. Haka nan kuma shi ne sarki na biyu da Turawa suka naɗa.
An naɗa sarki Usman bayan ya riƙe Kano na tsawo kwana 40. A lokacin da ya samu sarautar ya tsufa ya zo masa. A wannan lokaci yana da shekaru 76 a duniya.

A zamanin sarki Usman II, an yi gagarumin taron sarakunan arewa sakamakon zuwan ɗan sarkin Ingila wanda ya zo a jirgi. Saboda haka a zamanin sarki Usman II ne jirgin sama ya fara zuwa Kano. An yi wannan taro a cikin shekarar 1925. A kuma zamanin sarki Usman II aka fara aikin ruwan famfo da na wutar lantarki, da kuma gina wasu asibitoci, da kuma babban ofishi a cikin birnin Kano. Amma ba a kai ga kammalawa ba rai ya yi halinsa.

Sarki Usman II, ya sarauci Kano ta tsawon shekara bakwai da wata biyu a cikin yanayin tsufa da rashin lafiya. Taci-bata-ci-ba, haka ya yi mulkin. Allah ya jiƙansa da Rahama. Amin.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Saɓannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Cop, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.