Kofar Bulbula

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar Gadon Ƙaya 1619M


Gabatarwa


Tsohuwar Ƙofar Gadon Ƙaya


Sabuwar Ƙofa Gadon Ƙaya

Ita ma wanna ƙofa Sarki Muhammadu Nazaki ne ya gina ta. Sunanta ya samo asali ne daga sunan wanda aka gina ƙofar a gonarsa. Akwai wani mutum manomi mai suna malam Isma’il, shi ne ya ke da gona a daidai gurin da aka gina wannan ƙofa ta Gadon Ƙaya. To mutane suna yi masa kirari da “Arziƙi gadon ƙaya” shi kuma yana amsawa da “Idan ka haushi sai ya soke ka”.  Saboda haka aka saka wa wannan ƙofa wannan suna dan a riƙa tunawa da shi (Gwangwazo, 2003). Sannan kuma, Ƙwalli (1997), ya ce ta wannan ƙofa Turawa suka shigo Kano.

Manazarta:


Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub