Kemistiri - Chemistry

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kemistiri (Introduction to Chemistry)


Gabatarwa

Kemistry, fanni ne a ɓangaren kimiyya wanda ya himmatu wajen sanin abubuwa (matter), sauye-sauyen da ke tattare da su da kuma dalilan da ke haifar da sauye-sauyen. Fanni ne mai cin gashin kansa (field of study) a gidan kimiyya sannan kuma darasi (subject) duk dai a gidan kimiyya (science) da wasu masu son ƙwarewa a wasu rassan kimiyya da fasaha (science and technology) suke ɗauka.

Kalli Wannan Bidiyon Domin Ƙarin Haske

Ma’anar Kemistiri
Godwin O. Ojokuku, a cikin littafinsa mai suna Understanding Chemistry for Schools and Colleges ya bayar da ma’anar kemistiri da cewa:
Chemistry is the branch of science that deals with the study of matter: its structure, composition, properties, and the changes it undergoes. It involves the study of material substances that occur on earth and in the universe.

Farfesa H.A. Mohammed, Taibah University, Madina, Saudi Arabia.
Chemistry is the Study of Matter and its properties, the changes that matter undergoes, and the energy associated with those changes.

Daga ma’anonin da suka gabata, za mu fahimci cewa, kemistiri yana magana ne a kan matter; to mecece wannan matar? Matter is anything that has mass and occupies space; wato ita ce dukkan wani abu (anything) wanda ke da nauyi (mass) kuma zai iya mamaye wani muhalli (occupy a space). Nazartar dukkan abin da ke da wannan siffar ta fuskacin tsari (structure), ɓangarori (composition), siffofin baɗini (properties) da kuma sauye-sauyen da ke tattare da shi da kuma ƙarfin (energy) da ke da alaƙa da sauyin.

Alaƙoƙin Kemistiri da Wasu Fannonin Kimiyya
Akwai wasu fannonin ilimi da suke yi wa kemistiri kallon daddawa, mai ƙara miya zaƙi sannan kuma suke ƙulla alaƙar zara da wata a tsakaninsu. Irin waɗannan fannoni kemistiri yana zama musu fitila ne da take haskaka musu wasu fannonin bincike da ke da ruwa da tsaki a harkokin su. Daga cikin irin waɗannan fannoni akwai:

  1. Geology: Fannin kimiyyar sararin duniya da sauran duniyoyi. Fanni ne da ke nazarin duwatsu da dandagaryar ƙasa da kuma sinadaran da suke ɗauke da su da tarihinsu. Masana wannan fanni suna buƙatar ilimin kemistiri domin su gano bambance-bambance da ke tsakanin duwatsu da sinadaran da suke ɗauke da su da kuma irin amfanin da za a iya yi da su da dsauransu.
  2. Oceanography: Fannin kimiyyar tekuna, fanni ne da ke nazarin tekuna da abubuwan da suke da alaƙa da su. Masana wannan fanni suna da buƙatar ilimin kemistiri domin su nazarci yanayi da kuma lokutan da ruwa da sauran sinadarai ke gangarawa zuwa cikin tekuna, lokaci da kuma yanayin da tekuna ke ambaliya da dalilan yin haka, da sauransu.
  3. Engineering: Fannin fasaha, fanni ne da ke da ruwa-da-tsaki a fannin nazarin kayayyaki da kuma ƙera su kamar irin su jirgi, mota da sauran su. Masana wannan fani suna da buƙatar ilimin kemistriri domin su iya tantance kayan aikin da suka dace da kowane yanayi da kuma mataki da sauran abubuwa.
  4. Physics: Wannan fanni yana da buƙatar ilimin kemistiri domin ya nazarci sassan abubuwa na zahiri tare da yin kyakkyawan amfani da sakamakon domin samar da wasu sababbin abubuwa.
  5. Astronomy: Fannin nazarin sararin samaniya. Masana wannan fanni suna da buƙatar ilimin kemistiri domin su nazarci yanayin taurari da dangoginsu a sararin samaniya.

Sauran fannoni da suka haɗa da Environmental science, biochemistry, medicine, pharmacology, nutrition, toxicology, Archaeology, paleontology, forensic science da sauran fannoni masu yawa duk suna buƙatar ilimin kemistiri domin gudanar da nazari da bincike.

Manazarta:


ACS Chemistry for Life (2020). Chemistry Careers. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.acs.org/content/acs/en/careers/college-to-career/chemistry-careers.html

AGCAS (2020). Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.prospects.ac.uk/careers-advice/what-can-i-do-with-my-degree/chemistry

AGCAS (2020). Nuclear engineer. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.prospects.ac.uk/job-profiles/nuclear-engineer

Better Health (2017). Workplace safety - hazardous substances. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.betterhealth.vic.gov.au/health/healthyliving/workplace-safety-hazardous-substances

Cleveland Clinic (2018). Household Chemical Products and Their Health Risk An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://my.cleɓelandclinic.org/health/articles/11397-household-chemical-products-and-their-health-risk

Mendeley (2018). Top Ten Chemistry Jobs. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.mendeley.com/careers/article/top-10-chemistry-jobs/

Moore J.T (2020). Ten Great Careers in Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.dummies.com/education/science/chemistry/ten-great-careers-in-chemistry

Tucker L. (2019). What Can You Do With a Chemistry Degree? An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.topuniversities.com/student-info/careers-advice/what-can-you-do-chemistry-degree

United States Department of Labor (2020). Chemical Hazards and Toɗic Substances. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.osha.gov/SLTC/hazardoustoxicsubstances/


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub