Sarautar Fulani a Zazzau
Sarakunan Fulani su ne waɗanda suka sarauci wannan masarauta ta Zazzau tun daga lokacin nasarar Jahadin Shehu Ɗanfodiye har zuwa ya ɗin nan. A Zazzau sun fara mulki daga shekarar 1804 har zuwa yau ɗin nan (2016) su suke yi. Kenan yanzu sun kai tsawon shekaru Ɗari byu da goma sha biyu suna mulkin Zazzau.
Sarkin su na farko shi ne Malam Musa Bammali. Wanda kuma ya ke kai yanzu shi ne Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Shehu Idris.
Wannan gida na sarautar Fulani a Masarautar Zazzau ya sake kasuwa zuwa gidajen sarautar guda huɗu kamar haka:
- Mallawa: Asalinsu shi ne Malam Musa Bamalli, wanda ya karɓo tuta a hannun Shehu Ɗanfodiye.
- Barebari: Su ne gda na biyu a sarautar Zazzau, su kuma asalinsu shi ne Malam Yamusa Babarbare, tare suka karɓo tuta a hannun Shehu Ɗanfodiye, wanda shi ya zama sarkin yaƙin masarautar Zazzau a zamanin Malam Musa Bamalli.
- Katsinawa: Su kuma tushensu shi ne Malam Abdulkarimu Bakatsine, shima da shi aka karɓo tuta daga hannun Shehu Ɗanfodiye aka je Zariya da ita.
- Sulluɓawa: Su ne jikokin Malam Abdussalami Basulluɓe. Shima da shi aka karɓo tuta a hannun Shehu Ɗanfodiye.
Tun daga tushen wannan sarauta ta Fulani a Masarautar Zazzau zuwa lokacin da muke sabunta wannan rubutun (2018), an samu sarakuna kamar haka:
- Malam Musa Bamalli 1804 - 1821
- Malam Abdulkarim Bakatsine 1834 - 1846
- Malam Sidi Abubakar 1853 - 1853
- Malam Abdussalami Basulluɓe 1853 - 1857
- Malam Abubakar Ɗan Malam Musa 1871 - 1874
- Malam Muhammadu Sambo Ɗan Abdulkarimu 1879 - 1888
- Malam Aliyu Ɗan Sidi 1903 - 1920
- Malam Muhammadu Aminu 1959 - 1975
- Alhaji Shehu Idris 1975 zuwa yau (2016)
Manazarta:
Ɗalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru ɗan Isiyaku, The Great Emir of Zazzau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press. Zaria – Nigeria
Northern Nigeria Ministry of Information (1965). The Fascinating Provinces of Northern Nigeria. Gaskiya Corporation, Zaria-Nigeria.
Smith M.G. (1970). Government in Zazzau 1800-1950. London: Oxford University Press for the International African Institute. 371p. (Amaury Talbot Book Prize). Reprinted in 1964 and 1970.
Sarakunan Zazzau
- Musa Bamalli
- Yamusa Babarbare
- Abdulkarim
- Hammada
- Muhammadu Sani
- Sidi Abubakar
- Abdussalami
- Abdullahi
- Abubakar
- Abdullahi
- Muhammadu
- Usman Yero
- Shehu Idris
Ƙofofin Zazzau
- Ƙofar Kona
- Ƙofar Gayan
- Ƙofar Kuyambana
- Ƙofar Doka
- Ƙofar Bai
- Ƙofar Galadima
- Ƙofar Matarkwasa
- Ƙofar Jatau
- Ƙofar Tukur-Tukur
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin